Connect with us

Labarai

Ziyarar Sallah; JAGORA YA GANA DA WAKILAN ‘YAN UWA

Published

on

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin ranar Asabar 9 ga watan Shawwal 1444H (29/4/2023) ne Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da wasu daga wakilan ‘yan uwa da na bangarorin Harka a gidansa da ke Abuja.

A yayin ziyarar ta barka da Idil Fidr, baya ga taya murna, har wa yau, Jagora ya gabatar da nasihohi ga maziyartan. “Zan fara da taya mu murnar kammala azumin watan Ramadan din wannan shekara, da kuma (murnan) ganin wannan Idi na karamar Sallah.” Inji shi.

Shaikh Zakzaky (H) fara jawabinsa ne da bayani a kan halin da aka jefa kasar nan a ciki, inda ya bayyana mamakinsa kan yadda wannan al’ummar take cikin baganniyar rashin gane mene ne ya jefa ta cikin wannan halin, ballantana ta yi tunanin mene ne mafita? Yace: “Tun shekarun baya mun sha maganar cewa idan kana batun matsala, kowa ya san matsala, amma meye musabbabin matsala, mene ne kuma magani? Nan ne za ka ji maganganu mabambanta, wannan ya ce kaza, wancan ya ce kaza.”

Yace: “Bara ina cewa kullum ka tambayi mutane meye mafita? Sai su ce maka to a jira sai an yi zabe. Sai an zabi shugaba mai adalci, sai ya gyara, sai a huta. Har nace to ba irin wannan ne kuka yi ba shekarun baya? Sai da kuka darje waliyi zanqalele, kuma yanzu ya kwashe shekara takwas yana ta muku gyara, sannan kuma sai kuna wayyo-wayyo?” Ya kara da cewa: “har a bara nake cewa to wa ya sani, idan aka sake irin wannan? Suna cewa sai a jira 2023. Yanzu gashi 2023 din ta yi, har ma an yi zaben ko? Nake cewa to yanzu wa ya sanar da ku ko ma sai kun sake cewa wayyo? Wa ya sanar da ku ko ma sai kun ce ina ma tsohon waliyin nan ya dawo?”

Shaikh Zakzaky yace: “Ba haka nake fata ba, amma tana iya yiyiwu ya zama hakan ai. Wa ya tsammaci abin da ya faru yanzu zai faru? Ai da mutane sun dauka mafita suka samu ko? To sai suka ga abin da suka samu. To wa ya sanar da su ko nan gaba abin da za su gani sai sun sake cewa wayyo? To, wayyo kam gaskiyar magana, yana da wahalar gaske a bar wayyo din nan, har sai ranar da aka gane cewa wai mene ne asalin lalacewar nan, kuma mene ne mafita?”

Jagora yace: “wadanda su basu san addinin Musulunci ba, ba su wa Allah karya ba, su gara su. Su iyakan rayuwar duniyar nan suka sani, basu san ma akwai lahira ba. Iyakanta kenan a wajensu. Su gara ma su, kila ma duniyar tasu ta musu kyau. Amma mu mun san cewa ita rayuwar nan gidan gwaji ce, an dora mu ne a doron kasa don a gwada mu na gajeren lokaci. Abin da muka aikata a wannan rayuwa shi za a dauka a duba a rubuta, shi ne za a bamu sakamakonsa a rayuwa mai zuwa –rayuwa ta dindindin.

A nan ne ya shiga bayani a kan yadda aka mai da hankali ga duniya maimakon lahira, inda ya kawo kawo wani hadisin Manzon Rahma (S) da yake cewa, “Da duniyar nan ta kai darajar fiffiken sauro da kafiri bai sha ruwa ba.”

Yace: “Duniya tana da hadari. Ina iya cewa ma ta fi Lahira, domin a nan ake samun lahirar. Idan mutum ya bar duniyar bai sami lahirar a nan (cikinta) ba, to ba zai je can (lahirar) ya samu ba, saboda a can ba zai yi Istigfari a amsa masa ba, ba zai yi sallah ko addu’a a amsa masa ba, an gama. Sakamako ne kawai (ake riska a lahira). Ka ga ashe ta fi hatsari kenan, saboda duk muhimmancin lahirar nan a nan (duniya) ake nemanta.”

Ya yi bitan yadda babanmu Annabi Adamu (AS) ya rika koyar da mu kan yadda ya kamata mu koma inda muka fito. Yace, “aka ce yayin da Mala’ikan mutuwa ya zo daukar ran Annabi Adamu (AS), sai ya same shi a rana. Sai yace masa ya zo daukar ransa ne. Sai Adam yace masa, to ka bari na koma inuwa. Sai yace to. Sai ya koma inuwa. Sai Mala’ikan mutuwa yace masa, mene ne bambanci tsakanin a dauki ranka a rana da kuma a nan inuwa? Sai yace, ina son na koyawa ‘ya’yana ne cewa rayuwar duniyar nan gaba daya kamar ka tashi daga rana ne ka koma inuwa.”

Jagora yace, ina ma mun koyi darasi daga babanmu? Mun dauki nan (duniya a matsayin) wajen bidan can (lahira) don rayuwar dindindin? Amma sai wasu suka shantake. Wasu iyakan abin da suka sani kenan, kuma nan ne hankoronsu.

Ya cigaba da cewa: “Idan mutum bai san addini ba, ya zama abin da ya sani kenan (duniya), to kila ma ace shi gara shi. Amma mu Allah Ta’ala ya yi mana tagomashi, mun san cewa, an zo da mu nan ne domin a gwada mu, kuma aka aiko mana da fiyayyen halitta, fiyayyen Manzonni, ya zama mu ‘yan al’ummarsa ne.

“Daraja bayan daraja. Bayan an samar da mu daga rashi, aka yi mu mutane, aka yi mu Musulmi, aka yi mu ‘yan al’ummar Manzon Rahma (S), ni’ima bayan ni’ima. To, sai kuma muka zo muka shantake muka ce da mu da wanda bai san wannan ba, wai duk mu daya ne, wai muna neman mafita. Wai rayuwa bata da dadi, (ta ya za) a gyara. To, idan shi bai san mafita ba ai yana da dalili ko? To mu me za mu ce?

“Mu aka zo aka same mu a nizamin da yake bisa addini aka ce mana ga wannan ku koma kai. Sai muka koma a kansa muka zauna, kuma muka shantake muka ce ai komawa ga abin da muke a kai tun farko na (Musulunci) ma ba ma zai yiwu ba. Wai ba zai yiwu ba sam-sam. Haka za mu cigaba da rayuwa a yadda muka ga kanmu, illa iyaka kawai. Wai ba fata. To lallai akwai fata, mu mun san cewa ba muna zaune ne a lokacin da ba fata ba sam-sam. Mun san cewa akwai alkawarin Allah Ta’ala wanda baya saba alkawari.”

Jagora ya bayyana yadda Allah Ta’ala ke cika alkawarinsa, inda ya bayyana bayyanar Imam Mahdi (AS) a matsayin mai ceton al’umma a matsayin wani abu da ba makawa sai ya auku. Yace: “Mu muna da kyakkyawan fata (kan bayyanar Imam Mahdi (AJ). Abin da ake nufi da ‘Intizar’ kenan, wato ana dakon zuwansa ne. Dakon zuwan nan nasa aiki ne, ba kuna zaune ne ku shantake ku rike hannu kuce kuna jiran ya bayyana ba. A’a, za ku yi aiki ne don bayyanarsa har ya zo, kuna nan da rai ko baku nan. Ballantana kuma idan baku nan alkawari ne cewa wadansunku za a dawo da su da rai su rayu su taimaka masa a wannan zamanin. Ka ga Alhamdulillahi muna da dalilin da za mu tsaya kyam a tafarki.”

Har wa yau, a bangaren jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya nuna takaicinsa a kan yadda aka shagaltar da al’ummar Musulmi da junansu. Yace: “Ana nan an ba mu (al’ummar Musulmi) aiki, wanda ya kamata ace mu ne muka zama mafitan al’ummar nan gaba dayanta, amma sai aka ba mu aiki na fada da junanmu.”

Yace tun ba ma a wannan lokacin da ake da ‘social media’ ba. “Wannan hanyar sadarwa din, ya ba da damar kowa ya zama rediyo da talabijin din kansa kai tsaye, saboda haka yanzun nan za ka ji maganganu, ka ji kowa yana fadin abin da ransu ya ga dama, kuma za ka ga duk hankoron Musulmi shine su yi fada da junansu, su rarraba kawukansu su yi fada da junansu. Ita gaskiya a wajensu ita ce wacce ta zo ta inda suke bukatarta.

“Ba ma gaskiya ba, mutum dai yana da kungiyarsu da malamin kungiyar, to duk abin da malamin kungiyar ya fada daidai ne, ko karya ya yi ya yi daidai, kuma ko ya yi ba daidai ba sai sun kare shi. Kuma duk abin da wani ya fada idan ba dan kungiyarsu bane to ba daidai bane.”

Yace: “To haka ake yi? Haka gaskiya take? Ita gaskiya ba kana saninta bane sannan ka ce ita ce wannan? Ko ma waye ya fade ta sai kace haka nan ne. Ko da mutum ba gaskiya yake fada ba a mafi yawan bayanansa, sai ya fadi gaskiya (a wani lokaci) me za ka ce? Wannan abin da ya fada gaskiya ne. Amma yanzu ba haka bane, su gaskiya za ta zo musu ne ta inda suke so, ala dole sai a kungiyarsu, kuma duk abin da wasu suke fada kawai basu da wani aiki sai jafa’i. Wani ma yana jira ne kawai yana ganin ko hoto ya gani ko wani abu, yanzun nan a irin ‘comment’ din nan sai ya yi ashar. Shi ba sauraro yake ba, tunda ba na kungiyarsu bane, ashar kawai zai yi, zagi ne kawai na cin mutunci.

“To kuma sai ya zama yanzu shaidan ya samu hanyar ba Musulmi aiki. Sai wani can ya bullo da wata magana, sai yace shi bai yarda da kaza ba. Sai cacacaca, ya zaka ce baka yarda da kaza ba, kai dan kaza. Da mai yi da sassauci da mai kunduma ashar da mai jafa’i, caicaicai. Can kuma sai shaidanin yan sake kunno wata kuma, sai a sake. A yi raddi a yi raddin raddi, a yi raddin raddin raddi, aikin kenan. Haba don Allah. Yanzu shaidan ya same ku haka ai shikenan ya kare, yanzu ya baku aiki, baku da wani aiki sai jifa’i. ga abin da ya kamata ya zama shi ya dame mu, amma ba shi ya dame mu ba.”

Ya jaddada cewa: “Wannan abu da ban-takaici, ka ga ga abin da ya kamata ya zama shi ya dami al’umma, amma sam ba shi ya dame su ba, su ba su damu ba. Makiya sun riga sun gano mu ta nan.”

A bangarorin jawabinsa, ya yi bayani a kan yadda aka yi kokarin haddasa fada tsakanin al’ummu da musamman tsakanin Hausawa da Fulani a kasar nan, da kuma yadda aka mai da kashe-kashe ya zama ruwan dare. Har ya zama yanzu jami’an tsaron kasar ma da aka basu bindiga domin su kare rayukan mutane sun mayar da rayukan mutanen abin kashewa.

A nan ne ya yi bitan yadda jami’an tsaro suka budewa ‘yan uwa Musulmi wuta a Kaduna gab da Ramadan, inda bisa umurnin gwamnan Kaduna aka kashe mutane shida. Da kuma yadda jami’an tsaro suka kashe wani dan uwa mai suna Musa Yakubu a ranar da kotu ta kori karar shari’ar Fasfo a Abuja. Ya kuma yi bayani a kan irin shirin da jami’an tsaro suka yi da yadda suka budewa ‘yan uwa wuta a Muzaharar Quds din bana a Kaduna da Abuja har aka samu Shahidi nan take mai suna Yakubu da kuma wani mutumin gari da suka harba ya cika daga baya.

Yace: “A bara muke cewa, an shafa duk duniya ba inda aka yi harbi a Muzaharar Quds sai a Kaduna da Zariya. To bana ma duk duniya ba inda aka yi harbi sai a Abuja da Kaduna. Sai ka ji an nuna muzaharorin Quds a ko ina a duniya (an tashi lafiya), wai amma nan (kasar) harbi ake yi. Ba ko hankali a ciki, kuma ka ga su ba su damu ba. Misali, don meye idan mutum yana Muzahara sai ka harbe shi?”

Shaikh Zakzaky yace, akwai wadanda su a wajensu kullum mu ke yin laifi in an harbe mu. Yace: “har wani yana cewa akan ‘passport’ mutum zai je ya ba da ransa? Nace haba Malam, wa yace maka saboda ‘passport’ ne? Ba ka san cewa an je an samu wasu suna Du’a’u Kumail a markaz dinsu an bude musu wuta ba? Shi kuma mene ne suka yi? A Potiskum an je an samu ‘yan uwa suna addu’a an bude musu wuta. A nan Kaduna ana zaman Ashura a cikin wani gida, ba a ranar Ashuran bane, zaman Ashura ake yi a ranar 3 ga wata, suka je suka balle kofa suka shiga suka bude musu wuta. To su kuma saboda me aka kashe su?”

Ya cigaba da cewa: “mu da aka je har gida muna kwance aka cimmana aka bude wuta, mu kuma mun yi laifi ne da muna zaune a gidan? Aka cinna wuta aka kona gidan aka baje shi, shima ya yi laifi ne? Yanzu da meye za mu magance wannan laifin? Kar mu rayu? Ko mu koma iska mu je mu zauna? Ina tambaya ne.”

Yace: “Yanzu mutum bashi da hankalin da zai gane cewa akan addini suke wannan al’amari (na kashe mu)? Ai mujarradin kai ma’abocin addini ne ka yi musu laifi kawai. Su a tunaninsu kashewa kawai za su yi ba wani abu da ya dame su. Kuma duk maganar nan da ake yi, yadda ka san kana magana da kututturan dabino haka nan suke, sam ba abin da ya dame su, tunaninsu kawai kisa ne. Basu taba yi ya amfane su ba, amma kuma ba za su bari ba.

“Su mutanen nan basu damu ba, basu san cewa akwai sakamako ba, suna tsammanin wai idan an yi kisa ba komai. Suna cewa ma wai ba abin da zai faru. Ai Allah ba azzalumin kowa bane, ba wanda ya taba kisan kai ya gama lafiya. Ko da ka ga wadannan mutanen tun ranar da suka yi kashe-kashen nan komai ya birkice musu, ka ga wannan bakinsa ya murgude murya tana fita dakyar, ka ga wani kyakkyawa ya zama mummuna kamar dodo, mai farin ciki ya zama mai bakin jini, ya zama mujiya har da rana ana harbinsa, ko ta ‘helicopter’ ya bi sai an harbi ‘helicopter’ din, ko dai ba a same shi ba an dai harba. Mai farin jinin da yake a garin da in ya je tururuwan a ganshi har mutuwa ake yi, sai gashi yanzu jifansa ake yi. To ya ka gani? Ba sakamako ne ba? Kadan kenan, saura mummunan karshe a duniya, da gamuwa da azabar jahannama da fushin Allah yana nan zuwa.”

Yace: “Kamar yadda kullum nake fadi kullum, lallai fa kar mutum ya fidda rai, ba fa za za mu fidda rai ba, domin alkawari ne na Allah kuma Allah baya saba alkawari. Tabbatan addini lazim ne, kamar ya tabbata insha Allahul Azeem. Kuma al’amura ba sun rika lalacewa kenan ba, za su gyaru ne. Kar ku dauka an rika lalacewa kenan, tunda alal akalla dai akwai wasu mutane da ko sun qaranta, suna cewa a gyara ko?”

A karshen jawabinsa, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi kira ga ‘yan uwa a kan kaucewa fadawa tarkon makiya na husuma da juna. Yace: “To kuma don Allah ‘yan uwa, a kauce wa irin abin da ake jefa mu a kai na maganganu, la’alla yamu-yamu ne tsakaninmu ne, ko kuma tsakaninmu da wasu. Don Allah a kauce wa wannan.”

Ya kara da cewa: “Yamu-yamu dama kullum na kan wa ‘yan uwa magana nace in dai za ku yi aiki tare akwai matsala fa, haka abin ya gada. Za ka ji wani kai kana abinka tsakani da Allah, wani kuma bashi da wani aiki sai suka, wai kai dan bani na iya ne, kana wani nuna ka fi kowa ne, kai kaza-kaza. Oho dai, kana yi don wane ne? To ka yi abinka idan don Allah kake yi, amma idan domin shi (mai sukan) kake yi, sai ka bari tunda ya kwazzabeka ya dame ka, amma idan don Allah kake yi sai ka cigaba da abinka, ladanka na wajen Allah.” Ya jaddada.

Yace: “Haka kuma a kiyayi tankawa wadannan mutane. Na san ban ce a yi shiru kan komai ba, akan yi magana idan tana da tasiri, domin Allah Ta’ala ya kare Annabinsa, hatta a abubuwa kanana.”

“Saboda haka, idan abu ya cancanci a yi magana, to ana iya yi amma da hikima. Ba irin yadda suke yi ba, su suna yi ne ma da nufin su tunzura mutane, su fada musu zazzafan magana su saka musu bakin ciki. Suna so suma su yi irin wannan ne. Idan aka yi haka ya musu daidai. To sai a yi musu da hikima ne.” Inji Shaikh Zakzaky.

Ya cigaba da cewa: “Kuma ma ba kowa ne zai yi ba, idan wani ya yi ya wadatar. Idan suka yi raddin, aka samu aka yi raddi na hankali ai ya wadatar, ba kuma kowa kwayam ba, sai su bamu aiki. Su dama suna so su bamu aiki ne.

Yace, kullum suna so so ya zama da mu da su ne ana ta ta yin (rigima). Na’am, ba mu ce muku ba a raddi ba, amma raddin dai a yi shi da hikima. An fahimta ai? Saboda ko me ma muke muna kokari ne mu shiryar da mutane, ba muna neman su jefamu a cikin tarkonsu ne a yi ta fada ba, mu sai mu yi musu da hikima.”

A karshe, Jagora ya yi fatan Allah Ta’ala ya kiyaye mu da kiyayewarsa, Ya taimake mu da taimakonsa, Ya hada kawukan Musulmi.”

Ya jaddada fatan hadin kan Musulmi. Yace: “hadin kan Musulmin nan al’amari ne mai muhimmanci. Duk yadda za ka yi dan uwanka Musulmi dan uwanka ne, ko ya fitar da kai a Da’irar Musulunci kana nan a da’irar, tunda addinin Musulunci ba nasa bane, ballantana ya sa ka ko ya fitar da kai, kuma Aljanna ba kayansa bace, wuta ma ba kayansa bace ballantana ya jefaka.”

Yace: “Don suna jefa bayin Allah ma a wuta, ba su da wani aiki sai wancan su ce yana wuta, aikin kenan. To duk ba kayansu bane, da kayansu ne sai su yi yadda suke so, amma kayan Allah ne, shi kuma addini na Allah ne, kuma alkawari ne na Allah insha Allahu duk da aikin makiya, abin da Allah Ta’ala ya yi nufin zai auku na tabbatan addini kamar ya auku insha Allahul Azeem.”

Ya karkare da cewa: “Muna kuma lokacin fata ne, kuma wannan fatan dai yana nan tare da mu, muna fatan Allah ya hakkakar mana da wannan fatan insha Allahu.”

@SZakzakyOffice
30/04/2023

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Daliban Fudiya Masu Shirin Yin Sauƙar Alƙur’ani

Published

on

Kamar yadda shafin ofishin Jagoran (H) ya fitar da wasu hutuna dake nuna cewa; Ɗalibai daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin hardace Alkur’ani sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a jiya Laraba 15 ga watan May 2024 wanda yayi dai-dai da 7 ga watan Zul-Qada 1445 a gidansa dake Abuja

Ga Hotuna….

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Dawo Gida Nigeria Bayan Halartar Taro A Iraƙi

Published

on

Kamar yadda shafin Jagora (H) ya sanya wasu hotuna da yake ɗauke da saƙon dawowar shehin Malamin gida Nigeria a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu 2024.

Shafin ya wallafa cewa; Jagoran ya dawo gida ne bayan halartar taron ƙasa da ƙasa na nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu, wanda ya gudana a birnin Bagadaza, kasar Iraƙi a ranar Laraba 08 ga watan Mayu 2024.

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.