Connect with us

Labarai

Yadda Jagora Shaikh Zakzaky Ya Halarci Masallacin Juma’a A Tehran

Published

on

Dubun dubatan al’ummar Musulmi ne suka halarci babban masallacin Juma’a da ke Jami’ar Tehran, babban birnin kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau Juma’a 28 ga Rabiul Auwal 1445 (13/10/2023).

Jagoran Harkar Musulunci Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi a masallacin, inda mahalarta suka rika raira take daban-daban na goyon bayan gwagwarmayar Musulunci da jinjina ga Shaikh Zakzaky a matsayin gwarzo addini, jarumi, tsayayyen dan gwagwarmaya.

A yayin jawabinsa, Jagoran ya mika godiya ga Allah Ta’ala, tare da gaisuwa a jinjinarsa ga musamman Sayyid Qa’id Khamenie (H), da al’ummar Iran, bisa goyon baya da tsayuwarsu a kan gaskiya da tafarkin gwagwarmaya da taimakon raunana.

Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah sun isa birnin Tehran a ranar Laraba da ta gabata, domin samun damar ganin kwararrun likitoci don duba lafiyarsu daga jinyar da suka shafe shekaru takwas suna fama da su, tun bayan harin sojojin Nijeriya a kansu a karshen shekarar 2015.

A jiya Alhamis, Jagoran ya ziyarci Haramin Imam Khumaini (QS) da ke Tehran. Kuma tun bayan zuwansu mutane daban-daban da bangarori daban-daban suke aika bukatar damar ganawa ko ziyartansu.

Ga wasu daga hotunan sallar Juma’ar na yau da muka samu.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini

Published

on

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2024, Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa dandalin daliban harkar Musulunci a Nigeriya, a gidansa da ke Abuja.

Kamar yadda Ofishin Jagoran ya Wallafa cewa an yi ganawar ne a ranar Litinin 26 Zuqadah 1445, wanda ya yi daidai da 3/6/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.