Connect with us

Labarai

Tattakin Arba’een 1445 Daga Yankin Pambegua

Published

on

Ranar Lahadi 17 ga watan Safar 1445 (3/8/2023) ne ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daga Da’irorin da suka fito daga jihohin Adamawa, Taraba, Gombe, Bauchi, Plateau, Nassarawa da wani yanki na jihar Kaduna, suka gudanar da Tattakin Yaumul Arba’een din Imam Husaini (AS) daga Yankin Pambegua zuwa hanyar Zariya, domin bayyana jaje da juyayi, da isar da sako, da kuma bayyana Mazlumiyyar Imam Husaini (AS) da waki’ar Karbala mai radadi.

Tattakin na yankin Pambegua zuwa Zariya, ya samu halartan dubun-dubatan ‘yan uwa maza da mata daga da’irorin da suka fito daga jihohin da aka ambata. An kuma fara shi ne da misalin karfe 7 na safe, inda aka kammala shi da misalin karfe 1:00 na ranar Talatan, bayan an shafe wasu kilomitoci ana gudanar da shi.

An gudanar da Tattakin na yankin Pambegua lafiya, duk da wata motar ‘yan sanda guda daya da ta rika bin masu yinsa tun daga inda aka taso har zuwa inda aka rufe. Bayan jawabin rufewa wanda Shaikh Ahmad Yusuf Yashi Bauchi ya gabatar, sai ‘yan uwa da dama suka kama hanyarsu zuwa Abuja don gudanar da Tattakin wanda za a hadu da dukkan ‘yan uwa daga ko ina a fadin kasar a gudanar da shi ranar Talata 19 ga Safar 1445H.

Ga wasu daga hotunan Tattakin Yankin Pambegua:

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini

Published

on

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2024, Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa dandalin daliban harkar Musulunci a Nigeriya, a gidansa da ke Abuja.

Kamar yadda Ofishin Jagoran ya Wallafa cewa an yi ganawar ne a ranar Litinin 26 Zuqadah 1445, wanda ya yi daidai da 3/6/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.