Connect with us

Labarai

Tattakin Arba’een 1445 Daga Yankin Kano

Published

on

Ranar Litini 18 ga watan Safar 1445 (4/8/2023) ne ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daga yankunan Da’irorin Azare, Maiduguri, Potiskum da Kano da yankunansu, suka gudanar da Tattakin Yaumul Arba’een din Imam Husaini (AS) a kan hanyar Kano zuwa Zariya, domin bayyana jaje da juyayi, da isar da sako, da kuma bayyana Mazlumiyyar Imam Husaini (AS) da waki’ar Karbala mai radadi.

Tattakin na yankin Kano zuwa Zariya, a bana an kasa shi ne zuwa zangonni biyar; Zango na farko su ne suka faro daga garin Kano zuwa garin Karfi, sai zangon Kura, zangon Tudun Wada, zangon Ruma, da kuma zangon Zabi da ke cikin garin Zariya, duk cikansu an fara Tattakin ne a safiyar Litini din aka isa inda aka shirya rufewa kafin karewar yinin.

An gudanar da Tattakin na yankin Kano lafiya, inda ya samu halartan dandazon ‘yan uwa masoya Imam Husaini (AS). Ya kuma kayatu sosai, saboda yadda lajanoni daban-daban suka yi shiga ta musamman, tare kuma da irin Maukibobin da aka shirya don hidimtawa masu Tattakin da abinci da sauran kyaututtuka Tabarrukan.

Bayan jawabin rufewa wanda Shaikh Abubakar Maina Potiskum da Shaikh Sunusi Abdulkadir Koki suka gabatar, sai ‘yan uwa da dama suka kama hanyarsu zuwa Abuja don gudanar da Tattakin wanda za a hadu da dukkan ‘yan uwa daga ko ina a fadin kasar a gudanar da shi ranar Talata 19 zuwa 20 ga Safar 1445H.

A Ranar Lahadi, kwana guda kafin a fita Tattakin na yankin Kano, an gudanar da ziyarori zuwa makwantan Shahidan Tattakin yankin, wadanda gwamnatin Umar Abdullahi Ganduje ta kashe su a shekarar 2016 da 2017 a lokutan Tattakin Yaumul Arba’een din Imam Husaini (AS).

Ga wasu daga hotunan Tattakin Yankin Kano:

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Daliban Fudiya Masu Shirin Yin Sauƙar Alƙur’ani

Published

on

Kamar yadda shafin ofishin Jagoran (H) ya fitar da wasu hutuna dake nuna cewa; Ɗalibai daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin hardace Alkur’ani sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a jiya Laraba 15 ga watan May 2024 wanda yayi dai-dai da 7 ga watan Zul-Qada 1445 a gidansa dake Abuja

Ga Hotuna….

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Dawo Gida Nigeria Bayan Halartar Taro A Iraƙi

Published

on

Kamar yadda shafin Jagora (H) ya sanya wasu hotuna da yake ɗauke da saƙon dawowar shehin Malamin gida Nigeria a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu 2024.

Shafin ya wallafa cewa; Jagoran ya dawo gida ne bayan halartar taron ƙasa da ƙasa na nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu, wanda ya gudana a birnin Bagadaza, kasar Iraƙi a ranar Laraba 08 ga watan Mayu 2024.

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Ziyarci Haramin Imam Ali (As) A Najaf

Published

on

Shafin Ofishin Jagoran Harkar Musulumci Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), sun wallafa wasu hotuna a yau 12 ga watan May 2024 da yake nuna cewa shehin malamin ya ziyarci Haramin Imam Ali (As) da yake birnin Najaf a ƙasar Iraƙi.

Ga Hotuna…

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.