Connect with us

Labarai

Tattakin Arba’een 1445 Daga Yankin Kaduna

Published

on

Ranar Asabar 16 ga watan Safar 1445 (2/8/2023) ne ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Kaduna suka fara gudanar da Tattakin Yaumul Arba’een din Imam Husaini (AS), domin bayyana jaje da juyayi, da kuma isar da sako da bayyana Mazlumiyyar Imam Husaini (AS) da waki’ar Karbala mai radadi.

Tattakin na yankin Kaduna zuwa Zariya, ya cigaba a ranakun Lahadi da Litini, inda kuma ranar Talata ‘yan uwa suka nufi Abuja don yin Tattakin ‘yan uwa baki daya, wanda ‘yan yankin Kaduna da sauran yankunan da ke wannan barayin suka taso daga Suleja suka nufo Abuja.

An gudanar da Tattakin na yankin Kaduna lafiya, duk da barazanar jami’an tsaro da aka rika samu tun a ranar farkon fara Tattakin.

Ga wasu daga hotunan Tattakin Yankin Kaduna:

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Daliban Fudiya Masu Shirin Yin Sauƙar Alƙur’ani

Published

on

Kamar yadda shafin ofishin Jagoran (H) ya fitar da wasu hutuna dake nuna cewa; Ɗalibai daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin hardace Alkur’ani sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a jiya Laraba 15 ga watan May 2024 wanda yayi dai-dai da 7 ga watan Zul-Qada 1445 a gidansa dake Abuja

Ga Hotuna….

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Dawo Gida Nigeria Bayan Halartar Taro A Iraƙi

Published

on

Kamar yadda shafin Jagora (H) ya sanya wasu hotuna da yake ɗauke da saƙon dawowar shehin Malamin gida Nigeria a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu 2024.

Shafin ya wallafa cewa; Jagoran ya dawo gida ne bayan halartar taron ƙasa da ƙasa na nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu, wanda ya gudana a birnin Bagadaza, kasar Iraƙi a ranar Laraba 08 ga watan Mayu 2024.

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.