Connect with us

Labarai

Shaikh Zakzaky Ya Karrama Mahaddaciyar Alkur’ani A Ranar Ghadeer

Published

on

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

A kokarinsa na nuna wa al’umma muhimmancin Alkur’ani Mai Girma, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karrama wata yarinya mai suna Narjis Adamu, ‘yar shekaru 11 a duniya da ta haddace Alkur’ani, a jiya Juma’a 18 ga Zulhijja 1444 (7/7/2023) a gidansa da ke Abuja.

Mahaifin yarinyar Malam Adamu Gwanimi daga Ningi ta jihar Bauchi, ya shaida wa Jagora (H) cewa, tana da kimanin shekaru 6 da haihuwa, ya ga ba ta mai da hankali kan karatun Alkur’ani ba, sai ya yi mata alkawarin cewa, matukar ta tsaya ta haddace Alkur’ani, to Insha Allah ya mata alkawarin zai kai ta ta ga Malam idan Allah Ya nufi fitowarsu. Yace a nan ne ta dage ta mai da hankalin da a cikin shekaru 5 ta haddace Alkur’anin.

Jagora ya yabawa yarinyar, tare da karrama ta da kyaututtuka, ciki har da kyautar Turba da kuma Tasbaha. Sannan ya ja hankalinta a kan kara ba da kokari da lizimtar karatun.

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana yadda wasu yara Allah Yake musu baiwar iya haddace Alkur’ani suna da karancin shekaru sosai. Yace, an fahimci cewa tun kan yara su fara iya magana suke iya fara haddace bangarorin Alkur’ani in har an lizimci karanta su a yayin da suke ciki, ko bayan an haife su. “In ana karanta Alkur’ani tun yara suna ciki yana shigansu.”

Jagora ya karkare da kira ga yara da iyayensu a kan yadda ya kamata a rika yi wa yara Tarbiya. Yace, wasa da dadi, ba a hana yaro wasa gaba daya, a yi wasa ne kadan sai a yi karatu da yawa. “Bai kamata a tarke yaro ace sai karatu kawai zai yi, in bai yi ba har a hada masa da bulala, ba a duka.” Ya jaddada.

Ya bayyana matukar jin dadinsa game da yadda mutanen wannan yanki, musamman kananan yara suke ta kokarin lizimtar Alkur’ani da kiyaye shi. Tare da addu’ar Allah Ya yalwata hakan a nan gaba.

@SZakzakyOffice
08/07/2023

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

ARBA’EEN 1445; Kimanin ‘Yan Uwa 1,000 Suka Halarci Karbala A Bana

Published

on

A wannan shekarar, an samu ninkuwan adadin maziyartan Imam Husaini (AS) daga bangaren ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a lokacin taron Arba’een din shekarar 1445 (2023), a makwancinsa da ke Karbala.

Ziyarar Arbaeen din, wadda a kowace shekara ‘yan uwa sukan faro ne da yin Tattaki da kafafunsu tun daga birnin Najaf har zuwa Karbala. A wannan shekarar ma, ‘yan uwan sun faro Tattakin ne a safiyar ranar Alhamis 14 ga watan Safar, 1445, bayan shafe yinnai shida suna tafiyar kafa, suka isa haramin Imam Husaini (AS) da ke birnin Karbala da misalin karfe 10 na daren ranar Talata 19 ga Safar.

Wakilin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a yayin Ziyarar ta bana, Shaikh (Dr.) Yusha’u Bin Shaikh, ya bayyana wa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Daga Najaf, mun faro Tattakin ne da ‘yan uwan da ba su kai mutum 100 ba, kamar mutum 60 zuwa 70 ne a ranar farko da aka fara Tattakin da safe, amma zuwa yamma adadin ya karu, haka ma washe gari Juma’a adadin ya dada karuwa, haka ma ranar Asabar da Lahadi, kullum adadin na dada karuwa ne.

“Sai ya zama a ranar karshe (Talata) da muka iso Karbala, mun taso (mun nufi Harami) da ‘yan uwa kusan 700 ne, kafin mu shiga Harami kuma mutane suna ta shiga ciki, har aka kai mutane kamar 800 zuwa kusan 900. To kuma bayan mun shiga Harami ‘yan uwa sun sake karuwa sosan gaske a cikinmu, wadanda dukansu ‘yan Nijeriya ne, da suka hada da masu karatu a nan Karbala, da wadanda suke yi a Najaf, da wadanda suka zo daga Iran, da ‘yan sauran wurare, da kuma mu ‘yan Nijeriya da muka zo musamman saboda ziyarar.”

Ya cigaba da cewa: “Ko da yake, har ma da wasu ‘yan kasashen Afirka, musamman ‘yan kasashen Yammacin Afirka, sun zo sun jonu da tawagarmu ta almajiran Sayyid Zakzaky (H), don haka lokacin da muke shiga cikin Haramin, an yi kiyasin an shiga da mutane kusan mutum dubu daya ne. Wanda adadin ya karu a kan na shekarun baya da aka saba zuwa.”

Ba’adin ‘Yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) a cikin Haramin Imam Husaini (AS) a lokacin Arba’een din bana

Dr. Yusha’u ya kuma bayyana cewa: “Lokacin da muka zo shiga cikin Ataba, ana ta maganar cewa wai ba a shiga da hotuna ko alami na wani mutum (shaksiyya) ayyananniya, amma mu ko da muka shigo, muka doshi cikin Ataba din, muka je bakin Haramin, sai ga shi su da kansu (masu kula da wajen) suna kiran sunan Jagora, suna gaisuwa da jinjina ga ‘yan uwa a kan irin wannan salo da suka zo da shi a yayin wannan ziyarar tasu ga Abi Abdullah (AS).”

‘Yan uwa suna rike da hoton Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a cikin Haramin Imam Husaini (AS)

Yace: “Dama tun a kan hanya ma, idan muna tafiya, mukan ga idan an jero sunayen manya-manyan Malaman duniya, sai kaga an saka har sunan da Jagoranmu (H). Akan hanyar Najaf zuwa Karbala a wajaje daban-daban mun ga an rubuta sunan Jagora (da hotunansa). Kuma idan suka tashi rubutawa, ba kawai Shaikh suke sakawa masa ba, suna rubuta Ayatullah Shaikh Ibraheem Al-Zakzaky ne.” Yace, “Wannan wani abu ne da ke nuna girmamawa da karramawa ga su Jagora (Allah Ya kara musu lafiya da kariya).”

Nisan da ke tsakanin Najaf zuwa Karbala, tafiya ce ta kimanin Kilomita 78, sai dai kuma su ‘yan uwa sun faro Tattakin ne daga cikin garin Najaf, inda suka shafe wasu Kilomitoci kafin zuwansu inda ake fara kirga Kilomita, sannan kuma bayan isa Karbala, sun cigaba da tafiya da kafa har suka isa Harami, wanda haka yasa za a iya cewa, sun yi tafiya ne na kusan Kilomita 100 da kafarsu don wannan ziyarar.

“Duk da cewa, a wajen Tattaki ba ana kirga Kilomita ba ne, akwai abin da ake kirgawa, ana kirga Amudai ne, ‘Amudi’ kamar wani falwayar wutan lantarki ne, wanda ake sakawa tsakanin nan zuwa nan, su ne ake kira Amudai, kuma su ake kirgawa a matsayin nisan tafiya.” Inji Dr. Yusha’u.

Ya cigaba da cewa: “Amma dai kamar kirgenmu da muka saba na Kilomita, an ce tsakanin Najaf da Karbala kamar 78. To kuma kamar yadda na fada, idan aka hada da inda babu kirgan a Najaf, da kuma inda kirgan ya kare a Karbala, -inda babu Kilomita ko Amudai-, idan aka hada su za a kiyasta za su kai kilomita 10 zuwa 15, kuma idan muka dauka 15 din ne su, za mu ce an taka kusan kilo mita 100 a cikin wadannan yinnai guda shidan kenan.”

Dangane da shigar maziyartan ‘yan uwan cikin Haramin Imam Husaini (AS), Malam Yusha’u ya bayyana cewa: “Lokacin da aka bamu na shiga Harami karfe 10:00 na dare ne, amma sakamakon cinkoso da yawan mutane da aka samu, mun dade a kan layi kafin a kira mu, sai bayan karfe 11:00 na dare muka shiga cikin Haramin don sallama ga Imam Husaini (AS).”

Ya bayyana yadda tawagar ‘yan uwa ta ke tasiri ga tawagogi da sauran mutane da suka fito daga kasashe ta fuskaci daban-daban. Yace: “Idan suka ga tawagar ‘yan Nijeriya ne, tambayar da suke yi shine yaya Jagora yake? Ya Shaikh Zakzaky? Ya lafiyarsa? A wane hali yake ciki a yanzu? Da yawansu da sun gammu tambayarsu kenan akan Jagora da lafiyarsa da halin da yake ciki a yanzu haka. Bayan mun basu amsoshi, sai su yi ta yi masa addu’o’in samun lafiya da damar fita don zuwa neman lafiya a inda ya dace a kasar waje.”

Ya kuma bayyana yadda manyan Malamai daban-daban suke shaukin haduwa da Jagora (H), da yadda suke fatan Allah Ta’ala Ya bashi lafiya ta yadda wata rana zai samu halartan Ziyarar Haramin Imam Husaini (AS) a lokacin Arba’een musamman.

“Ataba Abbasiyya”, wadda ke kula da adadin masu shigowa ziyara a kowace shekara daga kasashen duniya, a bana ta bayyana fiye da mutum Miliyan 22 ne suka halarci taron Arba’een din Imam Husaini (AS) a Karbala.

Ga wasu daga hotunan Tawagar ‘Yan uwan a yayin da Ziyarar ta bana:

Continue Reading

Labarai

Maukibin Shaikh Zakzaky A Hanyar Karbala; Me Ya Ƙunsa?

Published

on

A wannan shekarar ta 1445 (2023), kamar sauran shekarun da suka gabata, Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gudanar da Maukibinsa, don hidima ga masu Tattakin Yaumul Arba’een zuwa Haramin Imam Husaini (AS) da ke Karbala, a kasar Iraq.

Maukibi, wata rumfa ce da ake shiryawa don saukan baki a yayin da suke gudanar da tafiyar kafa a lokacin Arba’een din Imam Husaini (AS). Akwai Maukibobi daban-daban da masu hidima ga Imam Husaini (AS) daban-daban daga sassan duniya suke samarwa, su rika ciyar da mutane abinci, da kuma basu wajajen hutu, da yi musu kyaututtuka a yayin da ake Tafiyar Arba’een a Iraqi.

A wannan shekarar ta 1445 Hijiriyya, Ofishin Jagora Shaikh Zakzaky (H) ya shirya Maukibobi guda biyu ne don wannan hidimar ga maziyartan Imam Husaini (AS); na farko shi ne wanda yake a Amudi na 1117 da ke kan hanyar Najaf zuwa Karbala; sai na biyu yana Amudi na 820 da ke kan hanyar Bagdad zuwa Karbala.

Me Aka Gudanar A Maukibobin Jagora (H) A Bana?

Wakilin Ofishin Jagora a daya daga Maukibobin, Shaikh Yahya Aljafari ya shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa, ayyuka kashi biyu Maukibobin suka gudanar a wannan shekarar, su ne; ayyukan hidimtawa masu tattakin, da kuma isar da sakon Harka Islamiyya da manufarta da bayani a kan Jagoranta.

A bangaren Tablig (Isar da sako), ya bayyana cewa, Maukibin ta buga rubutaccen Ziyarar Arba’een a dan karamin takarda mai aminci, dauke da hoton Jagora (H) a jiki, inda aka rika raba dubban kwafinsa ga maziyartan da ke wucewa, da nufin su yi amfani da shi idan sun isa Haramin Imam Husaini (AS), ladan kuma ya je ga Jagoranmu (H) da Shahidai masu girma.

Bayan wannan, Maukibin ya rika la’akari da mutanen da suka zo daga yankunan Turawa, da kuma masu jin yaren Ingilishi, inda ya rika raba musu kyautar rubutaccen littafin Taqaitaccen Tarihin Harkar Musulunci, wanda Malama Zeenah Ibrahim ta wallafa a cikin harshen Turanci. Yace, mutane da yawa sun nuna jin dadinsu ga samun wannan littafin na tarihin Harka, musamman wadanda suke da kishin ruwan fahimtar wani abu da ya shafi Shaikh Zakzaky da da’awarsa.

Ya bayyana bangare na uku na Tablig din da Maukibin ya rika yi a wannan karon. Yace, “shi ne yin bayani da baki ga maziyarta a kan halin da Sayyid Zakzaky (H) yake ciki, da halin da Harkar Musulunci take ciki, da kuma halin da Musulunci da sauran al’amura suke tafiya a Nijeriya.”

Yace, da yawan maziyarta daga yankuna, suna jin sunan Shaikh Ibraheem Zakzaky ne kawai, amma ba su san shi ko ayyukansa ba. Wasu ma suna dauka yanzu haka ya yi Shahada, kamar yadda sukan zo su ce, Allah Ya karbi Shahadar Shahid Zakzaky. Sai an yi musu bayani a kan cewa yana nan raye tukunna, kuma ga irin halin da azzaluman mahukuntan kasarsa suka bar shi a ciki, ga kuma irin dakewarsa da kuma tsayuwa a kan manufa da hadafinsa na kawo gyara a cikin al’umma, wanda shi ne irin hadafin Imam Husaini (AS) a lokacin waki’ar Karbala.

An kuma rika saka wakokin juyayin Ashura da aka yi da yaruka uku; Hausa, Larabci, da Farisanci, inda maziyartan suka rika sauraro. Tare da kunna Bidiyon da ya shafi Waki’a da daddare don isar da sako ga al’umma baki daya.

A bangaren Hidimtawa Maziyartan Imam Husaini (AS), Malam Aljafari ya bayyana cewa, Maukibin ofishin na Shaikh Zakzaky (H) ya samar da A.C (abin sanyaya yanayin muhalli), sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi a kasar Iraqi, inda ya ba maziyartan da ke wucewa dama su rika shiga suna kwanciya, ko su zauna su huta a ciki, har ma wasu sukan kwana a wurin. Yace, wannan ya sa sun rika yi wa Jagora (H) addu’a ta musamman da rokon sakayyar Allah Ta’ala a gare shi.

Maukibin ya kuma rika tanadan ruwan sanyi, da ‘Juice’ (lemun ruwa), da irin su Alkaki (cake), wanda a kowace rana ana rabawa maziyartan da ke wucewa a lokuta biyu daban-daban a kalla. Yace, wannan ma ya rika faranta ran maziyartan, saboda yadda suke samun ruwan da sanyin kankara mai dadi, alhali ana fuskantar tsananin zafin rana.

Maukibobin Sun Rika Samun Maziyarta Daban-Daban Daga Sassan Duniya

Da yake a wannan shekaran an samar da Maukibi guda biyu ne, akwai na hanyar Bagdad zuwa Karbala, wanda shi ne hanyar da mafi yawan Larabawa da mutanen Iraqi suke bi, sai kuma hanyar Najaf zuwa Karbala, wanda ya tattaro maziyartan da suka fito daga kasar Iran da wasu daga cikin mutanen Iraq, da kuma sauran mutane daga dukkan kasashen duniya. Don haka Maukibobin guda biyu sun rika samun baki, da sukan ziyarce su, su karbi hidimarsu, ko kuma su yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky addu’a kafin su wuce.

A yayin da wasu suka rika tsayawa suna tambaya a kan Shaikh Zakzaky, da manufar Da’awarsa, da kuma irin halin da ya rika ratsowa na jarabawowi a tsawon shekarun da ya shafe yana kira.

Daga muhimman bayin Allah da suka ziyarci Maukibin Jagora (H) da ke Amudi na 1117 a hanyar Najaf zuwa Karbala akwai Ayatullahi Ramazani (H), wanda shi ne shugaban Mazma’u Ahlulbait (AS), wanda ya tsaya ya tambayi bayani dangane da Shaikh Zakzaky (H) ya yi masa addu’a da isar da sakon gaisuwa gare shi. Da kuma sauran bayin Allah daban-daban maza da mata daga kasashe daban-daban.

Haka ma a Maukibin da ke Amudi na 820 a hanyar Bagdad zuwa Karbala, ya rika samun maziyarta daban-daban, musamman kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya daga kasashen daban-daban na duniya, ciki har da matasan Kungiyar Muqawamatul Islamiyya da ke Bagdad, da kuma takwarorinsu na yankin Azerbaijan, wadanda har karrama Maukibin Shaikh Zakzaky (H) din suka yi, tare da gabatar da kyauta gare su.

Maukibin Sayyid Zakzaky (H) ya zama wa mutanen Duniya wani amintaccen kafa na sanin mene ne sahihin halin da Jagora da Harkar Musulunci suke ciki a wannan lokacin.

A bana, “Ataba Abbasiyya”, wadda ke kula da lissafin adadin maziyartan da suka shigo Iraqi ta sananniyar hanya don ziyarar ranar Arba’een, ta bayyana cewa sun haura kimanin mutum Miliyan 22.

Ga wasu daga hotunan ayyukan Maukib din na Jagora (H) na hanyar Najaf zuwa Karbala:

Ga wasu daga hotunan ayyukan Maukib din Jagora (H) na hanyar Bagdad zuwa Karbala:

Continue Reading

Labarai

Hotuna: An Kammala Tattakin Ranar Arba’een 1445 Lafiya A Abuja

Published

on

A yau Laraba 20 ga watan Safar 1445H (6/9/2023) wacce ta dace da ranar Arba’een din Imam Husaini (AS), almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun gudanar da gagarumin Tattaki don juyayin ranar Arba’een din, tare da isar da sako da bayyana Mazlumiyar Imam Husaini (AS), a birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.

A safiyar yau, wasu matasa zalla sun fara gudanar da Tattakin ne daga Kasuwar Wuse zuwa Berger da ke tsakiyar birnin Abuja. Sannan da misalin karfe 10:00 na safe kuma kashi na biyu na masu Tattakin, wanda ya hado ‘yan uwa maza da mata daga sassa daban-daban na kasar nan, suka faro Tattakin daga Arab Junction da ke Kubwa, aka nufo cikin garin Abuja.

An kammala Tattakin lafiya da misalin karfe 11:20 na safiya, duk kuwa da barazanar jami’an tsaro da suka rika saka shingayen bincike da kokarin kama masu shiga birnin domin yin Tattakin.

Ga Wasu Daga Hotunan Tattakin Da Wakilanmu Suka Dauko Muku:

Hotuna: Muhammad Rabil

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.