Connect with us

Labarai

Shaikh Zakzaky Na Taya Al’ummar Musulmi Barka Da Ranar Mauludin Imam Hasan Almujtaba (AS) 

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taya al’ummar Musulmi murna da zagayowar ranar da aka haifi babban jikan Manzon Allah (S), Imam Hasan Dan Ali Dan Abidalib (AS) wanda ya auku a ranar 15 ga watan Ramadan.

 

A yayin da yake gabatar da jawabi dangane da Imam Hasan (AS) bayan kammala Tafsirin Alkur’ani Mai Girma a ranar 15 ga watan Ramadan, Shaikh Zakzaky ya bayyana muhimmancin raya Mauludin Imam Hasan (AS) ko da ta hanyar shirya walima da raba abinci da tunatar da juna matsayinsa ne a tsakanin masoyansa.

Da yake karanto darajojin Imam Hasan (AS), Shaikh Zakzaky ya ambata cewa ana wa Imam Hasan lakabi da ‘Assibd, As-Sayyid, Al’amin, Alhujja, Attakiy, Azzakiy, Almujtaba, Azzahid, Al-Barr, Annaqi.”

Shaikh Zakzaky yace dangane da fadin Allah (T) a cikin Alkur’ani, ‘Fi ayyi suratun maaSha’a rakkabak.’ Imam Hasan (AS) yace: “Allah (T) ya sauwara Ali a tsatson Abudalib, a surar Manzon Allah (S), sai ya kasance Ali Bin Abidalib (AS) ne ya fi kowa kama da Manzon Allah (S). Husaini Bin Ali kuma ya fi kowa kama da Fatima (SA). Ni kuwa sai na zama na fi kowa kama da Sayyida Khadijatul Kubra (SA).”

Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa:” yayin da aka haifi Imam Hasan, Sayyida Zahra ta zo da shi wajen Babanta (S) nannade a kyallen Haririn da Jibril ya taba kawowa Annabi daga Aljanna. Sai Manzon Allah (S) ya saka masa suna Hasan, ya kuma yanka masa rago.”

Imam Hasan Almujtaba (AS) shine limamin Musulmi na biyu, bayan Amirul Muminin (AS) a cikin jerin Wasiyoyin Manzon Allah (S) kuma Halifofinsa Tsarkaka a bayansa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

ƁANGAREN JAWABIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) KAN GWAGWARMAYAR IMAM KHOMEINI (QS)

Published

on

“Har ma an ce wani lokaci wadansu daga cikin mabiya Imam sun ga kisan da Shah yake yi ya yi yawa, suka je suka samu Imam, suka ce Ya Imam, mutumin nan fa kisan da yake yi zai iya karisar da al’umma. Ba yadda za a yi a dan sassauta? Kisan fa ya yi tsanani.

Suna yin wannan maganar, sai Imam yace musu su kawo masa ‘list’ na mutanen da za su iya gudanar da Gwamnati in an kafa. Su suna kokarin yadda za a sassauto, shi kuma ga matakin da ya je. Yace musu wannan al’amari na Allah ne, kuma zai tabbatar da shi.

Ka ga wannan al’amari irin na Imam Malam. Tsayuwa Kyam! Shima Genaral Huyser a cikin littafinsa yake cewa; Kuma sai su ga mutumin nan ya dauki wani ‘dangerous step’ wanda ba yadda za a yi mutum ya dauki wannan ya yi nasara, amma shi sai ya yi nasara.

Alal misali, su soja suna harbin mutane. Abin da aka saba ‘normally’ idan wasu suka zo suna harbinku, ku ma dole ku samu ko da duwatsu ne ku harbe su ko? To shi Imam sai yace a’a, a basu ‘flower’ ne. Shi kuma flower yana da daraja a wajen mutumin Iran, mu nan bamu san ma’anar flower ba, amma ‘yan Iran sun sani…..

Cikin ‘slogans’ din (mabiya Imam) har da cewa “Haba sojojinmu, me yasa kuke harbinmu? Haba sojojinmu, me yasa kuke kashemu?” Shi kuma Imam (QS) ya yi jawabi, a ciki yake cewa: “Haba soja, in ka yarda ka zama bawan wasu, maimakon ka yi wa kasarka hidima? Yanzu mutanenka za ka kashe maimakon ka yi musu aiki?” Imam yace: “Ka yar musu da ‘uniform’ dinsu, ka bar masa barikin, gudu kawai ka koma kauyenku.”

To, su ba su dauka soja zai ji wannan maganar ba. Sai kawai sojoji suka fara daina harbin. In an turo su aiki, sai kawai su yar da ‘uniform’ su bi mutane kawai. In an dora kamar soja 600 su je, in aka dawo sai a ce kamar soji 50 ba su dawo ba. in aka sake zuwa kuma sai a ce yanzu kuma 100 ba su dawo ba.

Sai suka fara cewa to yadda za a yi yanzu, da yake ba sa saka hula, da wuyar gaske ka ga hula a kan mutanen Iran, in dai ba Malami ba da yake sa rawani, don haka sai suka ce duk sojoji a rika musu wani irin aski. Sai suna musu wani aski a gewaye kai a bar gashi a tsakiyar kan. Su mutane suna zuwa ne da ‘shirt’ da wando, soja na dirowa yace ya zama nasu in ya cire ‘uniform’ sai su bashi ‘shirt’ sai ya zama dan gari.

To shine sai suka ce yanzu duk soja ya yi aski ta yadda za a gane shi, da anga wani soja ya zama dan gari sai a harbe shi. To da samarin (masu Muzahara) suka ji hakan sai kowa ya yi irin askin soja. Ko soja ya diro yanzu kansa iri daya da na mutanen gari, ba wani bambanci. Yana dirowa kawai daga mota sai a bashi ‘shirt’ da wando ya saka, ya cire bot ya sa takalmi kawai ya zama mutamin gari.

To, wannan ya daure musu kai. Sai (a ga) soja kawai ya fara kuka ya shiga cikin mutane. Sai suna mamakin wai wane irin abu ne wannan? Sai Imam ya dauki mataki wanda ba a saba ana daukan irin wannan matakin a yi nasara ba, amma sai a ga ya yi nasara.

Shi Huyser a littafinsa yana cewa wai, “rai goma yanzu zai yi maganin rai 100 nan gaba.” Ya yi ta maimaita wannan. Wato a kashe rai 10 yanzu maimakon a kashe 100 nan gaba. Ya yi ‘justifying’ kashe mutane da suke yi, domin kashe su yanzu kadan za a kashe, in aka kyale su za su yi karfin da dole sai an kashe da yawa. Kai kace ‘the only thing’ da za su yi kawai shi ne duk mai ra’ayin ‘revolution’ su kashe shi. To kuma abin ya girma, in ma kana ganin daidaiku ne yanzu ya zama sai dai in za ka kashe al’ummar gaba daya, sai ka mallaki itatuwa.

To sai ya zama suna mamakin wai wane irin mutum ne wannan? (Imam kenan). An yi an yi ya ƙi ‘confromise’ kawai, yana ta cewa lallai kawai kasa kasarsu ce, Amurka ta fita abar musu kasarsu kawai!

To har ma da kisa ya yi yawa, sai Imam Khomaini yace shi ma zai zo, ga shi nan zai zo a hada har da shi a kashe. To, wannan cewa zai koma Tehran, abin ya firgitasu.

Suka yi ‘meeting’ a kan ya za a yi ne? Wasu suka ce a hana shi sauka a filin jirgin saman Tehran, sai dai ya sauka a wani waje. Aka ce mutanensa ba za su yarda ba, za a yi rigima. Wasu suka ce a rufe ‘airpot’. Aka ce ba zai rufu ba ai.

Har ma a lokacin mutane suka fara cewa to da can muna ‘confromise’, amma yanzu in kuka hana Imam dawowa za mu fito da bindiga. To, sun san dama akwai bindigogi, amma ba a yi harbi ba, kuma a lokacin ko ba komai dama sojoji da yawa sun balle.

To, ana cikin wannan ma sai aka ce ma’aikatan ‘airforce’ da yawa sun balle. Soja kana iya samun wanda bai yi makaranta ba ya je ya yi soja, amma da ka ji an ce ‘airforce’ dole wanda ya yi karatu ne yake aikin, sojan sama wasa ne? ka san dole kasan kan gadon jirgi ko? Ba kawai za a ce maka kai sojan jirgin sama ne alhali baka sani ba. Kafin ka zama sojan sama dole sai ka yi karatu.

Saboda haka sojojin jirgin sama a cikin ‘military’ su suka fi ilimi, don su wayayyu ne, ‘minimum qualification’ din da za ka zama sojan sama dole ilimi ne mai zurfi. Sabanin zama ‘ordinary soldier/Army’ wanda yake kila ko firamare ka yi ko sakandire, ko ma a da ko baka iya rubutu da karatu ba kana iya yi, amma banda ‘airforce’.

To su ‘airforce’ a wannan lokacin suka sallama, sai suka je suka yi mubayi’a kawai, suka ce sun bi. Sai ya zama Shah ya rasa ‘airforce’. Saboda haka sai ya nemi sojan kasa su far wa ‘airforce’.

Shah ya taba sa ‘curfew’ (dokar hana fita), tun Imam Khomaini yana Paris. Kun san yadda ake ‘curfew’, a nan kasar suna yi suce sun hana kowa fita. To nan ma sun yi haukar da ba mu taba ji ba a duk duniya, sun saka ‘24 hours curfew’. A tarihin bil’adama ban taba jin an yi dokar hana fita na awa 24 ba, sai a Nigeriya da yake mahaukata ne. Wai kuma gwamnatin da aka zaba ne take wannan abin. Wai ‘24 hours curfew’ wannan hauka har ina? ‘The biggest’ hauka!

To, shi ne Shah ya saka ‘curfew’, yace daga 4 na yamma zuwa 12 na tsakar rana ba fita, wato ya ba da damar fita na awa hudu kenan a rana kawai, ka fito karfe 12 na rana, ka koma gida karfe 4 na yamma sai kuma gobe. Ba a taba jin irin wannan dokar ba a Iran kafin wannan lokacin.

Lokacin Imam yana Paris, da ya samu labarin (an saka dokar), sai yace to kar mutane su bi wannan dokar! Sai ya zama don biyayya ga Imam ba ma wanda ya kwana a gida. Ba batun ‘curfew’ ba, a kan titi mutane suka fito suna kwana. Lokacin kuma ana sanyi, amma mutane kowa ya fito ya kwana a titi.

To, lokacin da Shah ya so ‘Army’ su je su far wa ‘Airforce’, sai ya zama ba ta yadda za su bi, don mutane ne a kan titian. Kuma ‘Airforce’ din da mutanen gari suka je suka fafata da Army din, dole aka mai da su aka aje su a bariki.

Kama-kama ana nan dai al’amari ya zama dole suka bari Imam Khomaini ya koma. Kuma aka masa gagarumar tariya, irin tariyan da ba a san irinsa ba a tarihin da muka sani izuwa yanzu. Na’am, an san Manzon Allah (S) ya shiga Madina da gagarumar tariya, ana ‘dala’ar Dadaru alaina min saniyatil wada’i.’

Kuma Annabi Isa Almasihu (AS) ya shiga birnin Qudus a kan jaki, wanda aka rika masa waka, wanda aka ce har wasu Malaman gari suna cewa ka ji abin da mutane ke cewa? Ka hana su fadi, sai duwatsun gari su ma suka amsa.

To an ga tariya irin wannan wanda yake akwai a Bible, Isaiah ya fadi cewa an nuna masa mahayin jaki da mahayin rakumi, to mahayin rakumin shine Annabi Muhammad (S), don da rakumi ya shiga Madina. To ban sani ba ko Isaiah an nuna masa mahayin jirgin sama ba? (Dariya). Kila ya ga wani ya sauka a jirgin sama, ya ga tariya gagaruma. Domin shi Imam Khomaini a jirgin sama ya sauka.

Wani abin mamaki dangane da halin da ake ciki din nan, ana zaman dar-dar, jirgi ya dago daga Paris kuma ba a san abin da zai faru ba, shin za su harbi jirgin ne, ko za su hana shi sauka ne? Me zai faru? Duk mutane na firgice. Wani yace, da ya ji ance jirgin Imam ya taso firgita ya yi, yace ya za a yi ne yanzu Imam yana sama?

Amma aka ce Imam yana hawa jirgi, ya je ya zauna wajen ‘first class’ din nan, dama nan suka samar masa. Yana hawa kawai sai ya kwanta ya yi bacci abinsa. A natse kawai shi yake. Haka nan ya sauka akai gagarumar tariya.

Na takaice muku labari, domin kafin dawowar Imam kusan komai ya tsaya a Iran ma baki daya, mutane sun tsai da komai, masu sai da kalanzir sun ki sayarwa, masu kwashe shara ba kawai kwashe sharan ne basu yi ba, sun ma zuba sharan ne a hanya, ko ina biji-biji, komai ya tsaya cak! Amma da aka ce Imam zai dawo, to ko lomar tuwonka ne ya fadi a kan kwalta kana iya dauka ka ci abinka, saboda tsaftace muhalli da aka yi. Aka sa sabulu da soso aka wanke tituna, ko ina fes, aka doddora fulawowi.

Gagarumar tariya wanda aka ce a lokacin jama’ar da suka tare shi sun kai kimanin mutum miliyan shida. Wasu hotuna suna nan, wasu ‘black and white’ wasu ‘colored’, za ka ga gagarumar tariyar da akai ma Imam (QS).

Da ya sauka, farkon saukansa ya yi nufin daga nan ya wuce Bahijti Zahra ne, makabartan da aka bizne Shahidan da akai ta kashewa. Saboda haka hanyar ta gagara biyuwa daga ‘Airport’ zuwa Bahijti Zahra, saboda dafifin mutane, kowa yana son idonsa ya hango Imam.

Wasu don zari ma har sun hau kan motar da yake ciki ne ma suka zauna, da kyar ake hango Imam. Mutane dandazon mutane, titi ya cika da mutane ba zai yiwu motar tai tafiya ba. Karshe aka ga mota ba za ta tafi ba, mutane sun yi dafifi an rasa yadda za a yi da su. Saboda haka akai tunanin sai dai a zo da ‘helicopter’. Aka yi ta Koran mutane aka samu ‘space’ da kyar sannan aka zo da ‘helicopter’ ya hau ya tafi.

Ko da ya je can ma in da zai sauka ya gagara, saboda mutane suna ta cewa ina Imam zai je? Aka fada musu. A guje mutane suka kama hanyar Bahijti Zahra. Sun je sun cika ko ina yaba-yaba, aka rasa inda ‘helicopter’ zai sauka. Akai ta Koran mutane, wasu suka cire ‘belt’ dinsu suna ta juya shi haka, har aka samu wajen da ‘helicopter’ zai sauka.

Sannan kuma Imam a jawabinsa na farko ya yi wasu jawabai irin dai yadda ya saba. Yana cewa; “Haba Kanar, Haba Major, Haba Janaral, yanzu ka yarda ka zama bawan wasu kasa ka rika kashe mutanenka?”

Kuma lokacin ma gwamnatin Shah tana nan ya dawo. Sun yi yunkurin cewa ma za su kai hari a inda Imam yake, a wannan lokacin ne kuma ya zama lallai al’amari ya zama fafatawa sosai, aka jera kwana 10 cur, tun daga 1 ga watan Febrairu 1979 har zuwa 11 ga wata, kwana goma cur a jere fafatawa ne kawai ake yi, harbi kawai kake ji.

Zuwa ranar 11 ga watan Febrairu an yi ‘declairing’ karshen mulkin Shahanci da kuma tabbatar Daular Musulunci. Don haka ne ma suke kiran wadannan kwanaki goma din da ‘layalul ashr’ (10 days of layalil ashr). Wato daga 1 zuwa 10 ga watan Febrairu (da aka yi ta fafatawa), ranar 11 ga wata aka ayyana gwamnatin Shah ta tafi.”

— Bangaren jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin taron tunawa da Imam Khumain (QS) da aka gudanar a Husainiyya Baqiyyatullah Zariya a shekarar 2014.

@SZakzakyOffice
03/06/2023

Continue Reading

Labarai

SHEHU DAN FODIYO JAN-LAYINMU NE – Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ja kunnen masu cin mutunci da aibata Mujaddadin addinin Musulunci a nahiyar nan, Shehu Usman Dan Fodiyo (RA) da cewa, su fahimci cewa Shehu Usman jan-layi ne a wajenmu.

Shaikh Zakzaky, wanda aka haska jawabinsa na rufe taron Makon Dan Fodiyo da dandalin Dalibai na Harkar Musulunci suka shirya a karshen makon da ya gabata a Sakkwato, ya bayyana cewa: “Don mutane su sani, mu fa Shehu Usman Dan Fodiyo a wajenmu shi ne ‘khaddul ahmar’, wato Jan-Layi, shi ne ake ce ma ‘red line’ da Ingilishi.”

Ya jaddada cewa: “Mu Shehu Usman Dan Fodiyo jan layi ne a wajenmu, da zaran ka taba shi to mu ainihin shaksiyyarmu ne kake nema ka rusa gaba daya. ‘Personality’ dinmu kake neman ka rusa gaba daya, kamar kana nema ka nuna babu mu ne ma, ko ba a yi mu ba ma sam-sam. Domin shi ne alamin da ya yi duk cikanmu.”

Shaikh Zakzaky yace: “Duk cikanmu Dan Fodiyo ne, kuma tinkahonmu Dan Fodiyo ne, saboda haka babu yadda za ka taba Dan Fodiyo ya zama ba ka rusa mu bane. Don haka wani abu ne da ba za mu taba amsa ba. Kuma duk wanda muka ji ya taba Shehu Usman Danfodiyo ko yaya ne, to mun san abin da yake nufi, yana nufin ya rusa mu ne, da asalinmu, da tarihinmu, da komai namu. Yana so ya nuna mana cewa yanzu mu bayi ne, ba mu san komai ba tun fil-azal, yanzu kuma yana neman hanyar da zai zo ya dora mana wani abu ne daban ba addini ba, ba kuma abin da muka gada ba.”

Ya cigaba da cewa: “Tunda shi Shehu Usman Dan Fodiyo (RA) ya ga yanayi ne da ake zaune a ciki da ya sabawa addinin Musulunci, sai ya yi kira ga addini, addinin kuma ya kafu. To idan wani yanzu ya zo yana neman yace shi wani abu ne daban, to me yake nufi? Zai rusa addini kenan ko? Ya kafa wani abu daban.”

Yace: “Ba mu san ma me yake so ya kafa ba, tunda ba za a sauwala a komar da mu Nasara ba ai ko? Wani bai isa ya malkwaya yace, ai yanzu mun koma Nasara ba. Kuma wani ba zai koma yace ya maishe mu Yahudu ba… To abin da yake nufi ya maishe mu, ko me me yake so ya maishe mu, zai maishe mu bayin wasu ne, ba bayin Allah Ta’ala ba. Wannan kuma ba zai taba yiwuwa ba!”

Shaikh Zakzaky yace: “Na kuma tabbatar har ga Allah, babu wani mutum ko shi wane ne da zai ce shi Musulmi ne, kuma yana da’awa da sunan addinin Musulunci, ya ke magana a kai, yace wai zai taba shaksiyyar Danfodiyo! Ta ina za ka yi wannan? Mutumin da ya yi kira izuwa ga addini, addini ya kafu, ta ina kai za ka zama Musulmi kuma ka taba shi? Ba dai da sunan addini ba.”

Yace: “Idan ka ce mana da sunan kai Bahaushe ne, to me kake so a yi? A koma irin abin da ake a kai da can kafin Shehun ya bayyana? Za a koma bori da maita da tsafi ne? Su ne za ka yi kira gare shi?”

Tun da farko, sai da Shaikh Zakzaky ya fara da bayani a kan yadda addinin Musulunci ya sanya mutane baki daya da dukkan kabilu da bangarorinsu a matsayi daya, inda ya nuna cewa, wani na fin wani ne kawai da gwargwadon tsoron Allah dinsa. Yace, ba wai Hadisi bane, Ayar Alku’ani ne Allah Ta’ala yace da mu: “Wanda ya fi a cikinku a wajen Allah Ta’ala shi ne wanda ya fi taqawa.” Yace, ta nan ne ake sanin wanda ya fi wani.”

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kuma kawo fadin Manzon Rahma (S) da ke cewa: “Babu bambanci tsakanin Balarabe da Ba’ajame sai da taqawa.” Don haka yace duk mutane daya suke a wajen Allah, a kokarinsa na nuna rashin muhimmancin fadace-fadace da sunan kabilanci ko abin da ya yi kama da shi da wasu ke kokarin haddasawa a tsakanin nan.

Shaikh Zakzaky ya yi martani ga wadanda ake amfani da su da sunan su Hausawa ne za su yaki Fulani, ko wasu da ake bayyana su a matsayin su Fulani wai za su yaki Hausawa da cewa: “yanzu an zo an kitsa mana wani irin gaba, ance wai akwai wasu mutane sunansu Hausawa, akwai wasu mutane sunansu Fulani, wai kuma abokanan gaba ne. Rana tsaka aka akawo mana wannan. Kuma wannan ya zo ne a tunanin Bature, ba tunaninmu ba ne.”

Yace, sarakunan Hausa wadanda suka yaki Shehu, tun a wancan lokacin su ne suka yi kokarin nuna Shehu Usman Dan Fodiyo a matsayin Fulani, a maimakon su ambace shi da mai kokarin kira zuwa ga addini. “Maimakon su rika ce ma (almajiran Shehu) dakarun Jihadi, ko (su ce) ga masu kira zuwa ga addini nan, sai suka ce musu Fulani.”

Ya kuma bayyana cewa, ba Shehu Usman ne ya fara yakar sarakuna ba, su ne suka yake shi, shi kuma ya kare kansa. “Kuma wane ne ya yaki wani tsakaninsu da Shehu? Su suka yaki Shehu. Shi Shehu Wa’azi yake yi, yana karantarwa ne yana wa’azi. Su ne suka yi tunanin cewa za su kawar da shi. Kuma ko da suka yi kokarin kawar da shi ya yi musu hijira ne, -ya gudu ya kyale su, amma suka bi shi da yaki. To a lokacin ne tunda yake sun bullo da abin da yaki ne, shi ne shi kuma wajen kare kansa, sai Allah Ya dora shi birbishinsu, har Allah Ta’ala ya bashi nasara a kansu daya bayan daya, har aka kafa daula ta Musulunci.”

Yace: “In ya so wani ya kira (daular) duk abin da ya ga dama, amma Musulunci shi ne asasinta, shi ne abin da aka kafu a kai, ba Fulatanci ba. Da Fulatanci ne abin ai da sai a ce yanzu an hana magana da wani harshe banda Fulatanci. Ko ba haka bane? Sai ya zama kowa ya narke Hausa ma kawai yake yi tunda yake kasar Hausa ce, kuma dama shine harshen wajen (tun a wancan lokacin).”

Ya kara da cewa: “Kuma za a ga duk da yawan rubuce-rubucensu a lokacin sun yi ne da harshen Arabiyya, don shi ne harshen aiki. Lallai Hausa ba ta taba zama harshen Hukuma a hukumance ba, harshen magana ce kawai a lokacin, domin duk wasu rubuce-rubuce na aikin hukuma da Arabiyya aka rika yi.”

Shaikh Zakzaky ya jaddada bayanin da ya saba yi a kan cewa a gane Hausa ba kabila bace ballantana a samu wasu mutane su ce su ne kabilar Hausawa, balle kuma su ce za su yaki wata kabilar.

Yace: “Hausa kasa ce, babu wata Kabila mai suna Hausa. Ita kasar ita ce Hausan. Duk wadanda suke zaune a wajen su ne Hausa, kuma suna da kabiloli daban-daban, suna da harsuna daban-daban. Harsuna daban-daban a tsakaninsu da shigowar baki daga waje ne, sai wani harshe sabo ya bayyana sunansa Hausa.

“Saboda haka Hausa da farko muna iya cewa kasa ce, sannan kuma suka zama mutanen da ke zaune a wannan kasar, na uku kuma ya zama harshen mutanen kasar, na hudu kuma ya zama al’adun mutanen kasar. Saboda haka su wane ne Hausawa? Hausawa su ne mazauna kasar Hausa, masu magana da harshen Hausa, suke da al’adun Hausa. Amma ba kabila bane.”

Ya tambayi masu cewa Hausa kabila ce da cewa: “Su ‘ya’yan wane ne?” Yace: “Ba ‘ya’yan mutum daya bane, sun fito ne daga Gabas da Yamma da Kudu da Arewa. Me ya hada su? Zaman wuri daya da harshe daya. Saboda haka su Fulani da suke zaune a kasar Hausa, su ma Hausawa ne? Eh! Nufawa suma Hausawa ne? Eh! Yarbawa ma da suke kasar Hausa Hausawa ne? Eh!” Ya tabbatar.

Ya cigaba da cewa: “Ba ku ga ma suna da abin da suka kira Hausa bakwai ba? Da kuma wasu bakwai din ba zan kira sunan da suke fada da ba, a dayan bakwan ai sun ce har da Nufawa da Yarbawa ko? Da Jikum ma Hausawa ne. Duk wanda suke zaune a kasar Hausa suke magana da Hausa sunansu Hausawa, sawa’un suna da harshe banda Hausa ko ba su da shi.” Inji Shaikh Zakzaky.

Ya jaddada cewa: “Wani abu muhimmi wanda kowa dole ya san shi, shi ne, Hausa ba jini bane. Babu jinin Hausa. Jinin Hausa ne babu sam! Domin idan kace min (akwai) jinin Hausa, sai nace ‘ya’yan wane ne? Babu wani wanda yace su ‘ya’yan ko Bayajidda ne, (domin) dama akwai kasar Hausa kafin Bayajidda ya zo, Bayajidda ya samar da gidan sarauta ne a kasar Hausa.”

Shaikh Zakzaky yace: “Garuruwan da suka fi muhimmanci a lokacin guda bakwai, aka tura jikokinsa (ko yayansa) suka samar da wadannan garuruwan, amma dama akwai garuruwan, ba su suka kafa su ba. Sannan bayan nan kuma wasu garuruwan ma da suka zo suka yi karfi suka zama su ma suna magana da Hausa din ne.”

Yace: “Saboda haka, ba daidai bane wani mutum yace mana wai shi yana da jinin Hausa ba. Babu wani jinin Hausa sam-sam! Babu shi sam-sam.” (Ballantana a yi fadan kabilanci da sunansa).

Jagoran, ya bayyana rikicin da ake kokarin tayarwa a matsayin aikin makiya. Yace: “Wannan bakar gaban da Bature ya shuka (tun bayan da ya ci kasar nan da yaki), shi ne yanzu ya sake dago da shi, yake nema ya haddasa fitina a tsakanin al’ummar nan da sunan cewa, akwai wasu mutane sunansu Hausawa, akwai wasu mutane sunansu Fulani. Har ma yanzu akwai wasu sayayyun shafuka da suke surutai, yanzu zamanin internet da sauki ya zama kowa ya zama rediyo da talabijin din kansa, yanzu akwai wasu shafuffuka da suke bayyana, ba su da wani aiki sai antaya ashar da jafa’i da cin mutunci, wai su Hausawa ne suna zagin Fulani.

“Ko da yake na ga ma wasu, akwai wadanda suke kiran kansu Fulani suma suna zagin Hausawa. Nakan ce to duk cikanku an saka ku ne. Na ga ma a cikin zage-zagen ma har ana hadawa da zagin wasu kabilu banda Fulani din. Nace to duk wadannan abubuwan da suke yi an biya su ne akan su yi, an kuma saka su ne su yin.”

Shaikh Zakzaky ya yi nasiha ga duk masu jin cewa akwai wata sabani da ya kamata ta haifar da gaba alhali suna amsa sunan Musulunci, inda ya bayyana Musulunci a matsayin wani abu da ke dinke sabani da husuma.

Ya kawo kissoshin yadda Manzon Allah (S) ya samu kabilun Aus da Hazraj suna fada da junansu shekara da shekaru a Madina, amma da zuwansa da Musulunci ya hada kansu suka dunkule suka zama abu guda. Yace: “Shi addinin Musulunci hada mutane yake yi dama.”

Yace: “Kuma ko lokacin da Shehu Usman ya kafa daula, ba kowa ne ya zama Musulmi ba. Dama can ba ya samu kowa a matsayin Musulmi bane, amma kuma da yawan mutane sanadiyyar daularsa sun Musulunta. Amma wadanda ba su Musulunta din ba ma, ba an tilasta su ne aka ce sai sun zama Musulmi dole ba, amma sun zauna lafiya a wannan daular. Kuma haka nan al’amarin yake ko a lokacin Manzon Rahma (S).”

Jagora yace: “Yanzu ma idan muna maganar (komawa) addini, sai su ce kana nufin kowa zai zama Musulmi ne? Nace, to wa ya ce maka haka nan? Abin da muke cewa, shi addinin Musulunci ne zai yi iko. Shi yana da nizami, shi tsararren abu ne da ba mu muka yi ba, Allah ne ya aiko da shi. Abin da muke cewa kenan. Kuma idan shi addinin ya kafu to wanda duk yake ciki idan Musulmi ne, zai zama lazim ya yi aiki da addinin Musulunci, idan kuma shi ba Musulmi ba ne, idan ya Musulunta shikenan ya zama daidai da mu, idan ma bai Musulunta yana addinin duk da ya ga dama, zai dai zauna yana da hakki, sauran al’umma suna da hakki.”

Ya kuma amsawa masu cewa kasar ba ta zallan Musulmi bane, inda suke inkarin yiwuwar kafuwar daular Musulunci da cewa: “sai muce, in dai kasa tana nufin cewa mutanen wajen ace kowa (ya zama) Musulmi ne, to bai taba aukuwa ba a tarihi. Ko da daular Musulunci ta kafu ta mamaye duk duniya, ba kowa ya zama Musulmi ba, ba kuma kowa aka tilasta ma ya zama Musulmi ba. Kuma ko da aka yi daular Shehu Usman Danfodiyo, ba kowa ne ya zama Musulmi ba, kuma ba a tilastawa kowa ya zama Musulmi ba. Ba a tilastawa wani zama Musulmi. Saboda haka ba yadda za a yi kace mana wai ba zai yiwu a yi Musulunci ba sai idan kowa ya zama Musulmi. (Mu) ba abin da muka ce maka kenan ba.”

Ya cigaba da ba da amsa ga masu cewa ai kasa ba ta Musulmi kadai bace, da cewa: “Kasar ta su waye su kadai? “Da za mu tambaye ku, kasa ta waye? Mu amsa a wajenmu kasa ta Alah ce. Wa ya yi sama da kasa? Wa ya halicci mutane? Wa ya dora mutane a doron kasa? Allah Ta’ala ne. To kasar ta waye kenan? Kasa ta Allah ce. Ba kuma inda Allah Ta’ala ya yanka yace nan wajen na ba masu addini kaza, nan na ba masu addini kaza. Ba inda aka yi haka, kasa ta Allah ce, wanda yace, ‘Shi ne ya ajiye mana kasa sassauka, mu bazu a sassanta daban-daban mu ci arzikinsa.”

Jagora Shaikh Zakzaky ya karkare jawabinsa da nuna yadda makiya addini suka yi kokarin canza ma’anar jihadin Shehu Usman, inda suka yi kokarin nuna ya kafa daular Fulani ne bayan ya ci Hausawa da yaki, a maimakon daular addinin Musulunci. Da yadda suka nunawa mutane kamar Shehu ya bar gadon Sarauta ne, ba na Malunta da addini ba. Wanda ya bayyana wannan a matsayin makamin da makiya suka dauka na haddasa gaba a wannan lokacin.

“Lallai wannan da’awa (ta Harka Islamiyya) tana kokarin ta dawo da martaban da’awar Shehu Usman Dan Fodiyo, a san waye Shehu, me ya aikata? Sannan kuma a cigaba daga inda da’awarsa ta tsaya, ma’ana a cigaba da wannan da’awar har a je bakin ruwa ta Kudu da ta Yamma insha Allahul Azeem, a samu daula kwakkwara da sunan addinin Musulunci, wadda za ta hada al’umman nan gaba daya ta dunkule su karkashin tutar “La’ilaha Illallah, Muhammadur Rasulallah”. Kuma insha Allahu wannan kamar ya auku, don alkawari ne na Allah.” Ya karkare jawabinsa.

Continue Reading

Labarai

Ziyarar Sallah; JAGORA YA GANA DA WAKILAN ‘YAN UWA

Published

on

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin ranar Asabar 9 ga watan Shawwal 1444H (29/4/2023) ne Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da wasu daga wakilan ‘yan uwa da na bangarorin Harka a gidansa da ke Abuja.

A yayin ziyarar ta barka da Idil Fidr, baya ga taya murna, har wa yau, Jagora ya gabatar da nasihohi ga maziyartan. “Zan fara da taya mu murnar kammala azumin watan Ramadan din wannan shekara, da kuma (murnan) ganin wannan Idi na karamar Sallah.” Inji shi.

Shaikh Zakzaky (H) fara jawabinsa ne da bayani a kan halin da aka jefa kasar nan a ciki, inda ya bayyana mamakinsa kan yadda wannan al’ummar take cikin baganniyar rashin gane mene ne ya jefa ta cikin wannan halin, ballantana ta yi tunanin mene ne mafita? Yace: “Tun shekarun baya mun sha maganar cewa idan kana batun matsala, kowa ya san matsala, amma meye musabbabin matsala, mene ne kuma magani? Nan ne za ka ji maganganu mabambanta, wannan ya ce kaza, wancan ya ce kaza.”

Yace: “Bara ina cewa kullum ka tambayi mutane meye mafita? Sai su ce maka to a jira sai an yi zabe. Sai an zabi shugaba mai adalci, sai ya gyara, sai a huta. Har nace to ba irin wannan ne kuka yi ba shekarun baya? Sai da kuka darje waliyi zanqalele, kuma yanzu ya kwashe shekara takwas yana ta muku gyara, sannan kuma sai kuna wayyo-wayyo?” Ya kara da cewa: “har a bara nake cewa to wa ya sani, idan aka sake irin wannan? Suna cewa sai a jira 2023. Yanzu gashi 2023 din ta yi, har ma an yi zaben ko? Nake cewa to yanzu wa ya sanar da ku ko ma sai kun sake cewa wayyo? Wa ya sanar da ku ko ma sai kun ce ina ma tsohon waliyin nan ya dawo?”

Shaikh Zakzaky yace: “Ba haka nake fata ba, amma tana iya yiyiwu ya zama hakan ai. Wa ya tsammaci abin da ya faru yanzu zai faru? Ai da mutane sun dauka mafita suka samu ko? To sai suka ga abin da suka samu. To wa ya sanar da su ko nan gaba abin da za su gani sai sun sake cewa wayyo? To, wayyo kam gaskiyar magana, yana da wahalar gaske a bar wayyo din nan, har sai ranar da aka gane cewa wai mene ne asalin lalacewar nan, kuma mene ne mafita?”

Jagora yace: “wadanda su basu san addinin Musulunci ba, ba su wa Allah karya ba, su gara su. Su iyakan rayuwar duniyar nan suka sani, basu san ma akwai lahira ba. Iyakanta kenan a wajensu. Su gara ma su, kila ma duniyar tasu ta musu kyau. Amma mu mun san cewa ita rayuwar nan gidan gwaji ce, an dora mu ne a doron kasa don a gwada mu na gajeren lokaci. Abin da muka aikata a wannan rayuwa shi za a dauka a duba a rubuta, shi ne za a bamu sakamakonsa a rayuwa mai zuwa –rayuwa ta dindindin.

A nan ne ya shiga bayani a kan yadda aka mai da hankali ga duniya maimakon lahira, inda ya kawo kawo wani hadisin Manzon Rahma (S) da yake cewa, “Da duniyar nan ta kai darajar fiffiken sauro da kafiri bai sha ruwa ba.”

Yace: “Duniya tana da hadari. Ina iya cewa ma ta fi Lahira, domin a nan ake samun lahirar. Idan mutum ya bar duniyar bai sami lahirar a nan (cikinta) ba, to ba zai je can (lahirar) ya samu ba, saboda a can ba zai yi Istigfari a amsa masa ba, ba zai yi sallah ko addu’a a amsa masa ba, an gama. Sakamako ne kawai (ake riska a lahira). Ka ga ashe ta fi hatsari kenan, saboda duk muhimmancin lahirar nan a nan (duniya) ake nemanta.”

Ya yi bitan yadda babanmu Annabi Adamu (AS) ya rika koyar da mu kan yadda ya kamata mu koma inda muka fito. Yace, “aka ce yayin da Mala’ikan mutuwa ya zo daukar ran Annabi Adamu (AS), sai ya same shi a rana. Sai yace masa ya zo daukar ransa ne. Sai Adam yace masa, to ka bari na koma inuwa. Sai yace to. Sai ya koma inuwa. Sai Mala’ikan mutuwa yace masa, mene ne bambanci tsakanin a dauki ranka a rana da kuma a nan inuwa? Sai yace, ina son na koyawa ‘ya’yana ne cewa rayuwar duniyar nan gaba daya kamar ka tashi daga rana ne ka koma inuwa.”

Jagora yace, ina ma mun koyi darasi daga babanmu? Mun dauki nan (duniya a matsayin) wajen bidan can (lahira) don rayuwar dindindin? Amma sai wasu suka shantake. Wasu iyakan abin da suka sani kenan, kuma nan ne hankoronsu.

Ya cigaba da cewa: “Idan mutum bai san addini ba, ya zama abin da ya sani kenan (duniya), to kila ma ace shi gara shi. Amma mu Allah Ta’ala ya yi mana tagomashi, mun san cewa, an zo da mu nan ne domin a gwada mu, kuma aka aiko mana da fiyayyen halitta, fiyayyen Manzonni, ya zama mu ‘yan al’ummarsa ne.

“Daraja bayan daraja. Bayan an samar da mu daga rashi, aka yi mu mutane, aka yi mu Musulmi, aka yi mu ‘yan al’ummar Manzon Rahma (S), ni’ima bayan ni’ima. To, sai kuma muka zo muka shantake muka ce da mu da wanda bai san wannan ba, wai duk mu daya ne, wai muna neman mafita. Wai rayuwa bata da dadi, (ta ya za) a gyara. To, idan shi bai san mafita ba ai yana da dalili ko? To mu me za mu ce?

“Mu aka zo aka same mu a nizamin da yake bisa addini aka ce mana ga wannan ku koma kai. Sai muka koma a kansa muka zauna, kuma muka shantake muka ce ai komawa ga abin da muke a kai tun farko na (Musulunci) ma ba ma zai yiwu ba. Wai ba zai yiwu ba sam-sam. Haka za mu cigaba da rayuwa a yadda muka ga kanmu, illa iyaka kawai. Wai ba fata. To lallai akwai fata, mu mun san cewa ba muna zaune ne a lokacin da ba fata ba sam-sam. Mun san cewa akwai alkawarin Allah Ta’ala wanda baya saba alkawari.”

Jagora ya bayyana yadda Allah Ta’ala ke cika alkawarinsa, inda ya bayyana bayyanar Imam Mahdi (AS) a matsayin mai ceton al’umma a matsayin wani abu da ba makawa sai ya auku. Yace: “Mu muna da kyakkyawan fata (kan bayyanar Imam Mahdi (AJ). Abin da ake nufi da ‘Intizar’ kenan, wato ana dakon zuwansa ne. Dakon zuwan nan nasa aiki ne, ba kuna zaune ne ku shantake ku rike hannu kuce kuna jiran ya bayyana ba. A’a, za ku yi aiki ne don bayyanarsa har ya zo, kuna nan da rai ko baku nan. Ballantana kuma idan baku nan alkawari ne cewa wadansunku za a dawo da su da rai su rayu su taimaka masa a wannan zamanin. Ka ga Alhamdulillahi muna da dalilin da za mu tsaya kyam a tafarki.”

Har wa yau, a bangaren jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya nuna takaicinsa a kan yadda aka shagaltar da al’ummar Musulmi da junansu. Yace: “Ana nan an ba mu (al’ummar Musulmi) aiki, wanda ya kamata ace mu ne muka zama mafitan al’ummar nan gaba dayanta, amma sai aka ba mu aiki na fada da junanmu.”

Yace tun ba ma a wannan lokacin da ake da ‘social media’ ba. “Wannan hanyar sadarwa din, ya ba da damar kowa ya zama rediyo da talabijin din kansa kai tsaye, saboda haka yanzun nan za ka ji maganganu, ka ji kowa yana fadin abin da ransu ya ga dama, kuma za ka ga duk hankoron Musulmi shine su yi fada da junansu, su rarraba kawukansu su yi fada da junansu. Ita gaskiya a wajensu ita ce wacce ta zo ta inda suke bukatarta.

“Ba ma gaskiya ba, mutum dai yana da kungiyarsu da malamin kungiyar, to duk abin da malamin kungiyar ya fada daidai ne, ko karya ya yi ya yi daidai, kuma ko ya yi ba daidai ba sai sun kare shi. Kuma duk abin da wani ya fada idan ba dan kungiyarsu bane to ba daidai bane.”

Yace: “To haka ake yi? Haka gaskiya take? Ita gaskiya ba kana saninta bane sannan ka ce ita ce wannan? Ko ma waye ya fade ta sai kace haka nan ne. Ko da mutum ba gaskiya yake fada ba a mafi yawan bayanansa, sai ya fadi gaskiya (a wani lokaci) me za ka ce? Wannan abin da ya fada gaskiya ne. Amma yanzu ba haka bane, su gaskiya za ta zo musu ne ta inda suke so, ala dole sai a kungiyarsu, kuma duk abin da wasu suke fada kawai basu da wani aiki sai jafa’i. Wani ma yana jira ne kawai yana ganin ko hoto ya gani ko wani abu, yanzun nan a irin ‘comment’ din nan sai ya yi ashar. Shi ba sauraro yake ba, tunda ba na kungiyarsu bane, ashar kawai zai yi, zagi ne kawai na cin mutunci.

“To kuma sai ya zama yanzu shaidan ya samu hanyar ba Musulmi aiki. Sai wani can ya bullo da wata magana, sai yace shi bai yarda da kaza ba. Sai cacacaca, ya zaka ce baka yarda da kaza ba, kai dan kaza. Da mai yi da sassauci da mai kunduma ashar da mai jafa’i, caicaicai. Can kuma sai shaidanin yan sake kunno wata kuma, sai a sake. A yi raddi a yi raddin raddi, a yi raddin raddin raddi, aikin kenan. Haba don Allah. Yanzu shaidan ya same ku haka ai shikenan ya kare, yanzu ya baku aiki, baku da wani aiki sai jifa’i. ga abin da ya kamata ya zama shi ya dame mu, amma ba shi ya dame mu ba.”

Ya jaddada cewa: “Wannan abu da ban-takaici, ka ga ga abin da ya kamata ya zama shi ya dami al’umma, amma sam ba shi ya dame su ba, su ba su damu ba. Makiya sun riga sun gano mu ta nan.”

A bangarorin jawabinsa, ya yi bayani a kan yadda aka yi kokarin haddasa fada tsakanin al’ummu da musamman tsakanin Hausawa da Fulani a kasar nan, da kuma yadda aka mai da kashe-kashe ya zama ruwan dare. Har ya zama yanzu jami’an tsaron kasar ma da aka basu bindiga domin su kare rayukan mutane sun mayar da rayukan mutanen abin kashewa.

A nan ne ya yi bitan yadda jami’an tsaro suka budewa ‘yan uwa Musulmi wuta a Kaduna gab da Ramadan, inda bisa umurnin gwamnan Kaduna aka kashe mutane shida. Da kuma yadda jami’an tsaro suka kashe wani dan uwa mai suna Musa Yakubu a ranar da kotu ta kori karar shari’ar Fasfo a Abuja. Ya kuma yi bayani a kan irin shirin da jami’an tsaro suka yi da yadda suka budewa ‘yan uwa wuta a Muzaharar Quds din bana a Kaduna da Abuja har aka samu Shahidi nan take mai suna Yakubu da kuma wani mutumin gari da suka harba ya cika daga baya.

Yace: “A bara muke cewa, an shafa duk duniya ba inda aka yi harbi a Muzaharar Quds sai a Kaduna da Zariya. To bana ma duk duniya ba inda aka yi harbi sai a Abuja da Kaduna. Sai ka ji an nuna muzaharorin Quds a ko ina a duniya (an tashi lafiya), wai amma nan (kasar) harbi ake yi. Ba ko hankali a ciki, kuma ka ga su ba su damu ba. Misali, don meye idan mutum yana Muzahara sai ka harbe shi?”

Shaikh Zakzaky yace, akwai wadanda su a wajensu kullum mu ke yin laifi in an harbe mu. Yace: “har wani yana cewa akan ‘passport’ mutum zai je ya ba da ransa? Nace haba Malam, wa yace maka saboda ‘passport’ ne? Ba ka san cewa an je an samu wasu suna Du’a’u Kumail a markaz dinsu an bude musu wuta ba? Shi kuma mene ne suka yi? A Potiskum an je an samu ‘yan uwa suna addu’a an bude musu wuta. A nan Kaduna ana zaman Ashura a cikin wani gida, ba a ranar Ashuran bane, zaman Ashura ake yi a ranar 3 ga wata, suka je suka balle kofa suka shiga suka bude musu wuta. To su kuma saboda me aka kashe su?”

Ya cigaba da cewa: “mu da aka je har gida muna kwance aka cimmana aka bude wuta, mu kuma mun yi laifi ne da muna zaune a gidan? Aka cinna wuta aka kona gidan aka baje shi, shima ya yi laifi ne? Yanzu da meye za mu magance wannan laifin? Kar mu rayu? Ko mu koma iska mu je mu zauna? Ina tambaya ne.”

Yace: “Yanzu mutum bashi da hankalin da zai gane cewa akan addini suke wannan al’amari (na kashe mu)? Ai mujarradin kai ma’abocin addini ne ka yi musu laifi kawai. Su a tunaninsu kashewa kawai za su yi ba wani abu da ya dame su. Kuma duk maganar nan da ake yi, yadda ka san kana magana da kututturan dabino haka nan suke, sam ba abin da ya dame su, tunaninsu kawai kisa ne. Basu taba yi ya amfane su ba, amma kuma ba za su bari ba.

“Su mutanen nan basu damu ba, basu san cewa akwai sakamako ba, suna tsammanin wai idan an yi kisa ba komai. Suna cewa ma wai ba abin da zai faru. Ai Allah ba azzalumin kowa bane, ba wanda ya taba kisan kai ya gama lafiya. Ko da ka ga wadannan mutanen tun ranar da suka yi kashe-kashen nan komai ya birkice musu, ka ga wannan bakinsa ya murgude murya tana fita dakyar, ka ga wani kyakkyawa ya zama mummuna kamar dodo, mai farin ciki ya zama mai bakin jini, ya zama mujiya har da rana ana harbinsa, ko ta ‘helicopter’ ya bi sai an harbi ‘helicopter’ din, ko dai ba a same shi ba an dai harba. Mai farin jinin da yake a garin da in ya je tururuwan a ganshi har mutuwa ake yi, sai gashi yanzu jifansa ake yi. To ya ka gani? Ba sakamako ne ba? Kadan kenan, saura mummunan karshe a duniya, da gamuwa da azabar jahannama da fushin Allah yana nan zuwa.”

Yace: “Kamar yadda kullum nake fadi kullum, lallai fa kar mutum ya fidda rai, ba fa za za mu fidda rai ba, domin alkawari ne na Allah kuma Allah baya saba alkawari. Tabbatan addini lazim ne, kamar ya tabbata insha Allahul Azeem. Kuma al’amura ba sun rika lalacewa kenan ba, za su gyaru ne. Kar ku dauka an rika lalacewa kenan, tunda alal akalla dai akwai wasu mutane da ko sun qaranta, suna cewa a gyara ko?”

A karshen jawabinsa, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi kira ga ‘yan uwa a kan kaucewa fadawa tarkon makiya na husuma da juna. Yace: “To kuma don Allah ‘yan uwa, a kauce wa irin abin da ake jefa mu a kai na maganganu, la’alla yamu-yamu ne tsakaninmu ne, ko kuma tsakaninmu da wasu. Don Allah a kauce wa wannan.”

Ya kara da cewa: “Yamu-yamu dama kullum na kan wa ‘yan uwa magana nace in dai za ku yi aiki tare akwai matsala fa, haka abin ya gada. Za ka ji wani kai kana abinka tsakani da Allah, wani kuma bashi da wani aiki sai suka, wai kai dan bani na iya ne, kana wani nuna ka fi kowa ne, kai kaza-kaza. Oho dai, kana yi don wane ne? To ka yi abinka idan don Allah kake yi, amma idan domin shi (mai sukan) kake yi, sai ka bari tunda ya kwazzabeka ya dame ka, amma idan don Allah kake yi sai ka cigaba da abinka, ladanka na wajen Allah.” Ya jaddada.

Yace: “Haka kuma a kiyayi tankawa wadannan mutane. Na san ban ce a yi shiru kan komai ba, akan yi magana idan tana da tasiri, domin Allah Ta’ala ya kare Annabinsa, hatta a abubuwa kanana.”

“Saboda haka, idan abu ya cancanci a yi magana, to ana iya yi amma da hikima. Ba irin yadda suke yi ba, su suna yi ne ma da nufin su tunzura mutane, su fada musu zazzafan magana su saka musu bakin ciki. Suna so suma su yi irin wannan ne. Idan aka yi haka ya musu daidai. To sai a yi musu da hikima ne.” Inji Shaikh Zakzaky.

Ya cigaba da cewa: “Kuma ma ba kowa ne zai yi ba, idan wani ya yi ya wadatar. Idan suka yi raddin, aka samu aka yi raddi na hankali ai ya wadatar, ba kuma kowa kwayam ba, sai su bamu aiki. Su dama suna so su bamu aiki ne.

Yace, kullum suna so so ya zama da mu da su ne ana ta ta yin (rigima). Na’am, ba mu ce muku ba a raddi ba, amma raddin dai a yi shi da hikima. An fahimta ai? Saboda ko me ma muke muna kokari ne mu shiryar da mutane, ba muna neman su jefamu a cikin tarkonsu ne a yi ta fada ba, mu sai mu yi musu da hikima.”

A karshe, Jagora ya yi fatan Allah Ta’ala ya kiyaye mu da kiyayewarsa, Ya taimake mu da taimakonsa, Ya hada kawukan Musulmi.”

Ya jaddada fatan hadin kan Musulmi. Yace: “hadin kan Musulmin nan al’amari ne mai muhimmanci. Duk yadda za ka yi dan uwanka Musulmi dan uwanka ne, ko ya fitar da kai a Da’irar Musulunci kana nan a da’irar, tunda addinin Musulunci ba nasa bane, ballantana ya sa ka ko ya fitar da kai, kuma Aljanna ba kayansa bace, wuta ma ba kayansa bace ballantana ya jefaka.”

Yace: “Don suna jefa bayin Allah ma a wuta, ba su da wani aiki sai wancan su ce yana wuta, aikin kenan. To duk ba kayansu bane, da kayansu ne sai su yi yadda suke so, amma kayan Allah ne, shi kuma addini na Allah ne, kuma alkawari ne na Allah insha Allahu duk da aikin makiya, abin da Allah Ta’ala ya yi nufin zai auku na tabbatan addini kamar ya auku insha Allahul Azeem.”

Ya karkare da cewa: “Muna kuma lokacin fata ne, kuma wannan fatan dai yana nan tare da mu, muna fatan Allah ya hakkakar mana da wannan fatan insha Allahu.”

@SZakzakyOffice
30/04/2023

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.