Shahid Muhammad Mu’azu, mahaddacin Alkur’ani mai girma, matashi ne dan shekara 19 a saddda ya yi Shahada, sunan mahaifinsa Malam Mu’azu Ishaq Maifata, mahaifiyarshi kuma Malama Maryam Dalhatu.

An haife shi ne ranar 12 ga watan Afrilun 1997 (daidai da 5 ga Zulhijja, 1417H) a cikin Karamar Hukumar Sabon-Garin Zariya da ke jihar Kaduna. Kuma ya yi tsawon rayuwarshi tun daga haihuwa har zuwa shahadarshi tare da mahaifansa a gidan su da ke Unguwan Jaba da ke Sabon-Gari.

Shahid Muhammad ya fara karatun shi na Addini ne a makarantar Markazu Shahid Abubakar Madomawa da ke Unguwan Jaba, sannan kuma ya yi Qismul Tahfizul Qur’anil Karim ta Malam Mustafa Kismi. Daga karshe kuma ya koma Darul Imam Mahdi (AF) da ke unguwar ‘Yan awaki Muciya, wanda a nan ne ya samu albarkacin haddace Alkur’ani mai girma, da kuma litattafai da dama na Addini.

Bangaren karatun boko kuwa, Shahid Muhammad ya yi ‘Nursery’ har zuwa kammala Firamare a makarantar Ar-Rayyan Islamic Nursery and Primary School. Daga nan aka saka shi a wata makaranta mai suna Progress International School, inda ya yi JSS 1 zuwa JSS 2, sai aka mayar da shi makarantar Demonstration Secondary School da ke cikin ABU, a nan ya karasa karatun shi na Sakandire baki daya.

A shekaran 2015 ne ya samu gurbin karatu (admission) a fannin “Water Resources and Environmental Engineering” a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, wanda ya fara karatun kenan ba su kai ga kammala zango na farko (First Semester) ba a aji daya ya samu shahada. Sannan kuma ya yi wata makaranta ta koyon Kwamfuta, da kuma koyon gyaran waya da sauran kayayyakin lantarki.

Shahid Muhammad duk da kasancewarsa mai mayar da hankali ga karatu, bai kuma zauna haka ko ya dogara da wasu ba, ya rika yin sana’o’i daban-daban wanda yake taimakon kansa da iyayensa da su. Ya yi sana’ar gyaran wayar salula, sannan kuma ya yi aikin zaman jiran shago na siyar da kayan abinci a kasuwan Sabon gari.

A bangaren rikonsa da Gwagwarmaya kuwa, da yake mahaifan Muhammad su ma ‘yan Gwagwarmaya ne, don haka tun tasowar shi ya taso ne yana Gwagwarmaya shima, saboda haka za a iya cewa tun daga haihuwa har zuwa shahadarsa ya yi su ne cikin wannan Gwagwarmaya ta yunkurin tabbatar da addinin Musulunci da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke kira a kai.

Tun bayan tasowar Muhammad aka dauke shi aiki a lajanar Mu’assasatu Abulfadl Abbas (AS), wanda a nan ya sadaukar da komai nashi wajen aikin da suke yi na baiwa Jagora (H) kariya. Kasancewar a lokacin kusan ko yaushe yana makaranta ne- in ba yana boko ba to yana Islamiyya, to haka nan kullum idan ya je makarantar nan ya dawo komai gajiya kuma komai dare haka zai kama hanya ya tafi Gyallesu domin ‘duty’ da suke yi don baiwa Jagora (H) kariya a matsayin sauke wazifa.

Har ila yau, Shahid Muhammad Mu’azu ya rika aiki a bangaren bangaren ‘media’, inda ya ke taimakawa wajen juya jawaban Jagora (H) daga kaset irin na da (mai zare) zuwa Kwamfuta.

Kanwar Shahid Muhammad, mai suna Fatima Mu’azu ta shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Shahid Muhammad ya kasance mutum ne mai kirki, kunya da kuma tausayi. Yana tausayin musamman mahaifiyarshi, lokacin in ya zo ya ga tana aiki yana son ya taimaka mata da aikace-aikacen gida, duk ranar da yake gida to lallai bai barin ta ta yi aiki, sai dai ya yi mata ko kuma ya taya ta su yi tare.”

Ta kara da cewa: “Yana da zumunci da ‘yan uwanshi sosai, don haka kawai ya ke samun lokaci ya shirya ya je ya gaishe da ‘yan uwan mahaifanshi. Sannan ya kasance yana da son karatu sosai, dan shi in dai mutum na son ya burge shi ne to ya kasance yana son karatu, shikenan za su shirya. Haka ma kannenshi lokacin shi ne ya ke kara karfafa musu guiwa yana sa su su yi karatu.”

Tace: “Kuma da yake shi mahaddacin Alkur’ani, to ya kasance yana da dabi’ar yawaita karatun Alkur’ani. Don ko sadda suka kammala haddan nasu ma idan ya zo gida haka zai samu mahaifiyar shi ya ce, “Mama yanzu idan da za a tambaye ki a ce miki danki ya haddace Alkur’ani za ki ce eh?” Sai ta ce mishi “Eh mana, tunda ka haddace zan ce ka haddace!” Sai ya ce “A’a, ai ba ki tabbatar ba tunda baki taba gwada ni kin gani ba, ya kamata ki gwada ni ne ki tabbatar na yi din sannan ki amsa eh na yi.”

Tace: “Haka zai dauko Alkur’ani ya rika bin ta da shi yana rokon ta gwada shi. Ya kan ce ta janyo masa kowace aya da ta so ya cigaba ta ji. Idan ta karba tana ja mishi kuma sai ta ji lallai ko ina ta janyo mishi yana dauka ne ya cigaba. To sai ta ce “Alhamdulillah!” Shi ma kuma ya ji dadi. Kuma a lokacin ba ita kadai ya ke ma hakan ba, har ‘yan uwan shi da abokai in sun zauna haka zai ce a ja mishi don a tabbatar, don shi yana jin dadi a gwada shi, saboda ya samu tabbacin cewa eh lallai haddan nashi ta zauna a kan shi.”

Fatima tace: “Yaya Muhammad ya kasance haziki, yana sha’awan kere-kere, don ko gab da zai yi shahada ma ya fara kera wata na’uran sanyaya daki, amma bai kai ga kammalawa ba Allah Ya azurta shi da rabon shahada.”

Mahaifinsa, Malam Mu’azu Ishaq ya shaide shi da cewa: “Gaskiya wannan yaro (Shahid Mu’azu) ba mu san komai dangane da shi ba sai alkhairi, don gaskiya mutum ne mai kyawawan dabi’u da tausayi da biyayya a gare mu.”

Yace: “Abubuwa da yawan gaske sai daga baya ma nake gane irin gudunmawar da ya ke yi min, musamman tun da mu ‘yan kasuwa ne aike zuwa PZ a ko wane lokaci na ce a je a yi min ‘transfer’ (a banki) haka zai karba ya je ya yi babu bata lokaci. Abubuwa da yawa gaskiya yana tallafa mana. Mun shaide shi cewa yaron kirki ne, kuma ba mu san komai a kan shi ba sai dai alkhairi.” Ya jaddada.

Mahaifiyarsa, Malama Maryam Dalhatu ta bayyanawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Kamar yadda mahaifinshi ya yi bayani a kan irin yanayin dabi’unshi, to kuma abin da zan kara shine. ya kasance yana da rikon amana gaskiya, yana da gaskiya da kuma rikon amana. Don ni dai ban taba jin wani karya ya gudana a bakin shi ba, duk abin da zai fada maka to lallai gaskiya ne.”

Tace: “Kuma yana da rikon amana, duk abin da ka bashi ba zai taba tabawa ba, haka ko aiken shi a ka yi. Wani lokacin in mahaifin shi ya aike shi ko da ya dawo da canji, in nace ya yi amfani da shi in yana bukata, sai ya ce, a’a, ai bai ce in yi amfani da shi ba. Ba zai taba taba wannan kudin ba in dai ba shi ne ya ce masa ya bar shi ba, amma ko ni na ce ya bar shi ma ba zai yi amfani da shi ba, zai ajiye mai ne. Kuma don (mahaifin su) ya aike shi bai zama dole sai da abin hawa ba, da kafarsa ma yackan tafi ya je ya dawo, sannan kuma idan an samu ragi a kan yadda a ka bashi haka zai kawo ya ce gashi an samu ragi, ba tare da ya noke ba.”

Ta karkare da cewa: “Gaskiya tsakani da Allah ban taba jin wani karya ko ha’inci ko cin amana daga Muhammad ba, ban taba ji ba a duk rayuwarsa tunda yake har ya yi shahada.”

Shahid Muhammad ya yi shahada ne ranan Asabar 12 ga Disambar 2015 a Husainiyyah Baqiyyatullah, a waki’ar Buhari, wacce ta auku a ranar 1 ga Rabi’ul Auwal, 1437H.

A wannan ranan Asabar din da sojoji suka kai hari Husainiyyah, ana kyautata tsammanin cewa lallai yana daya daga cikin wadanda aka fara budewa wuta a kofar Husainiyyah. Domin kuwa kaninsa Shahid Ali (kafin ya yi shahada washe-garin ranar da ya yi) ya shaidawa babbar yayarsu cewa, ya ganshi a kofar Husainiyyah kafin a fara harbin, amma kuma tun bayan da aka yi harbin bai shiga cikin Husainiyyah ba sannan kuma ba a same shi ko a waya ba. Don haka ana kyautata zaton cewa yana cikin shahidan farko da aka fara samu a wannan waki’a, wanda su Sayyid (H) suka fadi cewa, bayan sojojin sun harbe su sun kwashe su ne suka kai su Bariki suka karasa su.

Da yake matashi ne Shahid, ya yi Shahada ya bar mahaifansa biyu a raye, sai yayar shi guda daya da kannen shi guda hudu, a cikin kannen nashi ne akwai Shahid Ali Mu’azu, wanda shi kuma ya yi shahada a ranan Lahadi 13/12/2015, -wato washegarin ranan da shi Shahid Muhammad ya yi shahada kenan.

Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
cibiyarwallafa@gmail.com
11/11/2022 (16/4/1444).

No responses yet

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *