Cikin Malaman Harkar Musulunci, wadanda Allah Ta’ala ya rabauta su da samun Shahada a waki’ar Buhari ta 2015 a Zariya, akwai Malam Muhammad Kabir wanda ake masa lakabi da “Alkanawi”.

Mai dakinsa, Malama Hasana Lawal, ta bayyanawa CIBIYAR WALLAFA cewa, an haifi Shahidin ne a unguwar Gwammaja da ke cikin birnin Kano a ranar Lahadi 30 ga watan June, 1963 (wanda ya yi daidai da 8 ga watan Safar, 1383H).

Tace, ya yi karatun Firamare da Sakandirensa duk a Karamar Hukumar Gwale ta jihar Kano. Daga baya ya samu gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda bayan fara karatu a fannin Polymer/Textile Engineering, suna cikin karatun kafin su gama aka sallame su, sakamakon wasu abubuwa da suka faru da ya shafi gwagwarmayar addini a lokacin. Bayan barinsu Jami’ar Ahmadu Bello, daga baya Malam Muhammad Kabir ya samu dama, inda ya tafi makaranta ya yi karatun addini a kasar Sudan.

Malam Muhammad Kabir ya fahimci Harkar Musulunci ne a jami’a a wajajen tsakiyar shekarun tamaninoni, lokacin yana matsayin dalibi. Kuma tun daga wannan lokacin ya cigaba da gwagwarmayar addini har zuwa karshen shekarar 2015 da sojojin Nijeriya suka Shahadantar da shi.

Shahid Kabir AlKanawi (da hula), tare da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarun baya.

Ta bangaren iyali, Shahid Alkanawi yana da mata daya ce, wanda suka haifi ‘ya’ya 11 da ita; mata shida da maza biyar, sai dai kafin Shahadarsa biyu daga cikin ‘ya’yan sun rasu, inda ya tafi ya bar ‘ya’ya tara a raye.

Kafin dawowarsa Zariya da zama baki daya, Malam Kabir Alkanawi ya zauna a Kano, inda har ya rike Amirancin ‘yan uwa na Kanon na tsawon shekaru. Kuma a nan ne ma ya yi aure.

Mai dakinsa, Malama Hasana ta shaidi halinsa da cewa: “rayuwarsa shi abin tausayawa ne da wannan, gaskiya ni lokacin da mu ka yi aure da shi shekaruna ba su da yawa, amma a tsawon wadannan shekarun da muka yi na shaide shi da yana da gaskiya da tausayi da rikon amana da sadar da zumunci.”

Ta cigaba da cewa: “Yana da tausayawa kananan yara da mata, don a rayuwar da na yi da shi, tun kafin ma ya fara samun yara, da yake akwai wata yarinyar kanwar shi da muka rike, ni tun zamana da shi yarinyar nan ko wane irin abu za ta yi bai taba saka hannu ya dake ta ba. Haka kuma yaransa da ya haifa su ma bai taba dukansu, sai dai ya yi musu nasiha idan sun yi laifi.”

Tace: “Kyawawan dabi’u da kulawarsa ta sa yawanci ayyukan gida ma shi yake yi, har wani lokaci ma idan nace ya bari mana zan yi wannan. Sai yace, a’a shi dai zai. Wani lokaci ma ina kwance abubuwan da ya kamata ace mace ne za ta yi, amma shi ya ke yin su kafin na tashi.”

Ta kara da cewa: “Ta fuskacin rikon amanarsa kuwa, ko da zai zama gida babu abin cefane baya iya taba kudin mutane da ke wajensa, sai dai yace mu yi hakuri, amma ba ya iya tabawa, ga kudi da yawa za ka gani a wajensa, amma zai ce ba zai taba wannan kudin ba, domin na al’umma ne.”

Babbar ‘yar Shahid Muhammad Kabir, mai suna Fatima, ta shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “(Mahaifinta) yana da mu’amala mai kyau da mutane, musamman ma ta fuskacin rikon amana, tun da a kafin Shahadarsa shine kamar “Mudir” na Islamic Center, to ko wani kudi ne in aka tashi taro shi a ke baiwa su, a matsayinsa na wanda aka ba mas’uliyar kula da wajen, to ko ya zo da kudin gida ne, ko da bai da wani kudin sai su, kuma akwai bukatar amfani da su, sam ba zai iya taba wannan kudin na Islamic Center ba, tunda daman kudin jama’a ne. Don haka ko wace bukata yake da ita, ya kan iya hakuri har sai ya samu kudinsa na kansa kafin ya biya ta.”

Tace: “Ta bangaren zumunci kuwa, shi yana da yawan zumunci, kowa nashi ne, ko da kuwa kai makiyin shi ne zai ziyarceka saboda ya sada zumunci da kai. Sannan kuma yana da girmama mutane, hatta wadanda ya fi su shekaru ko ilimi da sauransu, tunda yawanci wadanda na ke ganin suna tare da shi lokacin za ka ga ma samari ne, amma ba zai nuna wai girman kai ba ko ya ji cewa wannan karamin yaro ne, kowa yana zama tare da shi su yi mu’amala.”

Fatima ta kara da cewa: “Mun godewa Allah sosai, tunda a rayuwarmu da shi ko abu ne muke bukata idan muka tambaye shi baya taba ce mana babu kai tsaye, ko da kuwa bashi da shi din ne, to zai yi mana magana mai dadi ne, ya kuma ce mana idan ya samu zan yi muku insha Allah. Sannan kuma ko laifi yaro ya yi a gida bai taba dukan shi ba sai dai ya yi masa nasiha ko ya yi barazanar kamar zai dakeka din hark a tsorata ka bari, amma dai bai taba duka ba gaskiya.”

Lokacin da matsaloli suka yawaita a Kano a karshen shekarar tis’inoni, sai Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya tura Malam Muhammad Mahmud Turi a matsayin wakilin ‘yan uwa na Kano, sai ya dawo da Malam Kabir Kanawi Zariya, inda ya cigaba da kula da Cibiyar Fudiyya (Fudiyyah Islamic Center) da ke Danmagaji a Zariya.

Sai ya zama Malam Kanawi ya cigaba da kula da wannan Cibiyar, wacce a cikinta akwai dakin karatu, da wajen tarurrukan ilimi, kuma a nan ne Jagora (H) ya fara gabatar da karatun Tafsirin Alkur’ani da Nahjul Balagha da Majlisosin karatu da Daurori da sauran tarurrukan Harkar Musulunci kafin a samar da Husainiyyah Bakiyatullah.

Baya ga kula da wannan wajen da yake yi, ya cigaba da koyarwa a makarantar Fudiyyah da ke Zariya, har da bangaren kananan yara. “Har ma mutane suna mamaki a lokacin da yake koyarwar, idan suka ga yana fama da yara suna ta surutu a aji ko wasa, amma ba ya iya dukansu sai dai ya masu nasiha.” Inji Matarsa.

Tace: “Wasu lokuta zai dawo gida yace kansa yana ta ciwo, yace saboda hayaniyar yara shi kuma ba zai iya dukansu ba. Yakan ce, shi yaro ana yi masa nasiha ne ba duka ba in dai ana son a tarbiyantar da shi ne.”

Da take bayani dangane da shahadarsa kuwa, Malama Hasana ta shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Na san ya fita a ranar Waki’ar (12/12/2015) sun tafi yin sallar Magribaini a gidan Malam Zakzaky (H), ya dawo wajen karfe 9nd ya dauki abinci da bargo da tabarmi don ya kai ma bakin da suka zo daga garuruwa su yi amfani da su. Da ya kai masu kuma sai ya kara dawowa gida, ya zo ya yi sallah, ya yi addu’o’i, ya ajiye kwamfiyutarsa a gidan sai ya koma Gyallesu (gidan Malam). To tun daga nan dai rabuwarmu da shi.”

Tace: “Da Asubahin ranar Lahadi ya kirani, yace ga fa halin da suke ciki a saka su a cikin addu’a domin maharani nan suna nufin Malam ne kawai, sai dai Allah Ta’ala ya bamu sabati. To daga nan dai bai kara kirana ba sai wurin 11ns a ranar, lokacin ma gaskiya ina jin karan harbi, yake cewa ga su nan fa sun riga sun shigo gidan Malam (H), sai dai a yafe masu a taimaka masu da addu’a kuma Allah ya bamu sabati gaba daya. Tun daga nan ban kara jinsa ba kuma, tun da ko an kira wayar ma baya shiga.” Inji Malama Hasana.

Ta kara da cewa: “Gaskiya dai tun daga wannan lokacin ba mu sake jinsa ba, kuma dai ba mu samu wani da ya zo ya tabbatar mana da cewa ya ga sadda aka harbe shi ko wani abu mai kama da hakan ba, ni dai a ta bangare na.”

– Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
Email: cibiyarwallafa@gmail.com
11/11/2022 (16/4/1444)

One response

  1. Gaskiyar magana ta fadi gaskiya akan Mahaifinta nasha ganin shaheed kabir Alkanawy yana tafiya a kasa zuwa fudiyyah Islamic center tunda daga gyallesu har zuwa dan magaji Allah ya qarbi shahadarsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *