Connect with us

Tarihin Shahidan Harkar Musulunci

Shahid Khalid Yahya Gilima

Published

on

Shahid Khalid, daya ne daga matasa masu kokari da sadaukarwa ga Harkar Musulunci, kafin shahadarsa mamba ne a Mu’assasatu Abul Fadl Abbas, wacce aka assasata da nufin baiwa Jagora da Da’awarsa ta komawa ga addini kariya.

An haifi Shahid Khalid ne a garin Batagarawa da ke jihar Katsina a ranar Alhamis 14/6/1990 (daidai da 20 ga Zulkida 1410H).

Ya fara karatun Firamare a Staff Primary School da ke Polytechnic Kaduna, lokacin da aka yi waki’a a Poly sai aka kori wasu ‘yan uwa da ke aiki a Poly din, ciki har da mahaifin Khalid, wato Engr. Yahya Gilima, don haka sai aka dauke Khalid daga wannan makarantar aka mayar da shi Aunty Ni’imatu Nursery and Primary School da ke Tudun Wada inda ya cigaba da karatun Firamarensa.

Khalid yana aji hudu a wannan makarantar, sai aka yi wani fada a Kaduna a kan batun Shari’a, inda mahaifansa suka cire shi tare da ‘yan uwansa daga nan, suka mai da su wata makaranta da ke kusa da gidansu mai suna Future Leaders Primary School da ke Malali, a nan ya kammala karatunsa na Firamare.

Bayan kammala Firamarensa, an kai shi wata makarantar Sakandire mai suna Ulul Albab a Katsina, kasancewar a makarantar ana hadawa da karatun addini da na boko. Sai dai sakamakon rashin kulawa da yay a fuskanta a makarantan, dole mahaifansa suka dawo da shi Kaduna bayan ya kammala aji daya (JSS1), inda suka mayar da shi makarantar Uncle Bado Memorial Secondary School da ke Kaduna, a nan ne ya kammala Sakandirensa.

Da ya kammala Sakandire, sai ya tafi wata makarantar Computer a Kazaure jihar Jigawa, da ake ce ma “Informatics”, inda a nan ya yi ‘Introductory to Computer Studies’ na watanni takwas, ya ci jarabawa, ya koma ya yi National Diploma, nan ma ya ci, sannan ya dawo ya yi HND ita ma ya gama ya fita da kyakkyawar sakamako.

Ya so ya tafi Japan ya cigaba da karatunsa a lokacin, amma sai makarantar suka ce, idan mutum ya yi HND a wajensu suna tura shi kasar Singapore ne ya je ya yi Degree, shi kuma yace ba zai je can ba. A dalilin haka ya dan yi shekaru a gida bai cigaba da karatun ba. Sai ya cigaba da gyaran Computer a gida, kasancewar ya san cikinta da wajenta.

Daga baya iyayensa sun nuna masa muhimmancin cigaba da karatun a duk inda ya samu. A nan ne wani ya bashi shawarar ya je Ghana don ya yi Digirinsa a wata makaranta wacce take reshe ce ta Jami’ar Greenwich University ta Ingila. Nan Khalid ya nemi ‘admission’ kuma ya samu, ya tafi har ya kammala karatun, sai dai bai kai ga ganin sakamakonsa ba sojoji suka kashe shi a Zariya.

Mahaifiyarsa, Malama Jummai Ahmad Karofi ta bayyana shi a matsayin sadauki, wanda ya fi duk ‘ya’yan da ta haifa jarumta da karfi a jiki. Tace: “Khalid ya kasance tun yana yaro karami da ka ganshi kakkarfa ne, tare da hakan kuma Allah Ya saka masa hakuri sosan gaske, da kawaici da kau da kai, don abin da kai zai baka haushi har ka yi fada shi sai ka ga ba ya bata masa rai sam-sam.”

Ta kara da cewa: “Kuma duk cikin yaranmu ba wanda ke da dabi’ar saurin yin abokai kamarsa, duk garuruwan da muka zauna bayan haihuwarsa, shi ke fara kawo aboki gidanmu. Kuma shi abin duniya bai dame shi ba, haka zai dauki kayanmu na gida yana ba abokan nasa, ko da ka yi masa fada ba zai hana gobe ma idan ya ga mai bukata ya sake bashi wani abin ba.”

Tace: “Tun yana yaro yana da kokarin ganin ya iya abu, a dalilin haka ya zama kusan komai yana iya yi musamman na kere-kere, shi ne kafinta, shi ne gyaran wuta, gyaran mota da su fanka idan sun lalace, duk ire-iren wadannan abubuwan dai. Yana da kiriniya sosai sadda yake yaro ta fuskacin komai zai dauka yace zai gyara shi ne ko da lafiyansa kalau, a kokarinsa nay a iya hada abin idan mai sauki ne, ko kuma ya gyara shi idan ya lalace.”

Tace: “Khalid ya dawo makarantar da ya yi a Ghana da kwanaki shida, suka tafi Zariya. Sun tafi tun ranar Juma’a ne, lokacin ana waki’ar Gabari, amma sai ranar Lahadi suka yi Shahada a Gyallesu, domin na gansu a Gyallesu ranar Lahadi da safe kafin a harbe ni. Tun daga nan dai zuwa yau ba mu san halin da Khalid da ‘yan uwansa biyar suke ciki ba, duk da dai mun samu labari daga wani da yace a gabansa aka harbi Khalid ya yi Shahada.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tarihin Shahidan Harkar Musulunci

WAƘI’AR GABARI; Shahid Sulaiman Abdullahi (Injiniya)

Published

on

Daga cikin tsayayyun Harisawa masu kula da hidimar Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) akwai Shahid Sulaiman Abdullahi, wanda ake masa lakabi da Injiniya.

An haifi Shahid Sulaiman ne a shekarar 1981, a garin Zariya da ke jihar Kaduna. Bayan fara tashinsa ba jimawa mahaifinsa ya rasu, sai aka saka shi a aikin koyon gyaran mota (Gareji).

Shahid Sulaiman ya fahimci Harkar Musulunci ne tun kafin waki’ar Abacha, ta sanadin yayanshi da Allah ya yi masa baiwar fahimtar Harkar tun da jimawa, sai ya rika yi ma kannensa karatun littafan addini kullum bayan sallar Asubah, cikinsu har da Shahid Sulaiman, wanda ta wannan dalilin ya fahimci Harka.

Kaninsa Malam Ayuba Abdullahi, ya shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa, rikon Shahid Sulaiman da gwagwarmaya da yadda ya bata lokacinsa, ya sa har garejin da yake aiki tare da cewa ya zama Oga a wajen, yana da masu kawo masa aiki sosai, amma bai cika samun zamansa ba, kusan ko yaushe yana wajen aikin Gwagwarmaya.

Yace: “Kuma yana ma aiki a wani Kamfani, amma sai da ta kai ma Kamfanin sun kira shi sun bashi zabi tsakanin aikin Kamfaninsu ko kuma aikin Gwagwarmaya, amma Shahid Sulaiman ya zabi aikin Gwagwarmaya.”

Ya kara da cewa: “Da yake lokacin waki’ar Quds na 2014 na samu rauni, sai wata rana yake min wasa cewa kai ka kama hanyar Aljanna ka dawo, amma ni idan na kama hanyar tafiya zan yi ba zan dawo ba. Kuma tun daga wannan lokacin na lura ya kara canza rayuwarsa, ya yawaita ibada da karatun Alkur’ani da kyautatawa, don haka Shahadarsa bata bamu mamaki ba.”

Shahid Sulaiman Haris ne, kuma yana cikin masu rakiya (escourt) din Jagora, Sayyid Zakzaky (H), shi ke lura da gyaran motocin gidan Malam ko idan za a yi tafiya. “Yana yawan rike babbar waya, saboda idan an yi tafiya da Jagora (H) wata mota ta kakare a hanya shi a kan barwa ya gyara ya taho da ita, to in abin zai ci kudi da yawa sai ya je ya sai da wayar tasa ya sai abin da zai gyaran in bai fi karfinsa bay a gyaro ya taho” Inji Malam Ayuba.

Yace: “Akwai wani tafiya da muka yi da shi zuwa Bidda, a hanyar dawowa motar ‘escourt’ daya ta lalace, sai aka tsaya aka bar masa motar don ya gyara, da yake Malam (H) ya tsaya a Dabai don ziyara, ana Dabai sai ga Shahid Sulaiman ya kariso da motar nan. Daidai za a bar Dabai sai motar da Jagora (H) ke ciki ta fara matsala, nan ma sai aka bar ma Shahid Sulaiman motar ya gyara ya taho da ita, muna kusa da Zariya sai gashi ya iso da motar ya gyarata, sai aka rika mamaki. Gaskiya Allah ya bashi wannan baiwar sosai.”

Shahid Sulaiman ya yi Shahada ne a garin Gabari, waki’ar da aka yi ranar Juma’a ana gobe za a yi waki’ar Buhari. Waki’ar da masarautar Zazzau ta shirya shi, ta tura ‘yan tauri su dira a kan ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky na garin Gabari.

Kaninsa Ayuba ya bayyana yadda Shahadarsa ta kasance. Yace: “Muna tare da shi a ranar Juma’a 11/12/2015 da safe, sai na ga kwayar idanunsa sun zama farare tas, muna magana da shi sai yake ce min, idan na ji an kira kan batun zuwa Gabari a sanar da shi, can da yamma sai aka fada min abin da ke faruwa a Gabari din, sai na kira shi, yace na jira shi. Bayan ya fito mun shiga mota, yana gaba ina baya, sai na ga ya waigo ya kalleni, sai muka hada ido muka yi dariya. Mun isa yamma ta yi sosai, lokacin masu harin ‘yan uwa sun yi galaba sosai a kansu, amma dama hadafin zuwanmu shine taimakon ‘yan uwan da aka dirawa.

“Muna zuwa, sai Shahid Sulaiman ya rika kokarin kora masu harin da kokarin kange su daga saran ‘yan uwa. Har nake ce mas aka daina shigewa mutanen nan don baka san wajen nan ba, ni na san illarsu, gashi bamu da yawa. Ai muna cikin maganar nan ma suka karo karfi suka kewaye mu, suka fara dukanmu da sanda da sara da takobi da jifa da duwatsu da sauransu, ana haka ne suka jefi Shahid Sulaiman a fuska da dutse ya fadi, sai kawai suka hau shi da sara. Ni ma a lokacin ne suka sare min yatsu suka fara lilo duk muka kwanta.

“Can da na mirgina na tashi, sai na ga shi sun zagaye shi suna saransa, a daidai lokacin ina nunfashi da kyar ba taimakon da zan iya masa, karshe nima sai wasu ‘yan uwa ne suka iya kawo min dauki suka dauke ni. A wannan lokacin suka shahadantar da Shahid Sulaiman.” Inji Ayuba.

Injiniya Sulaiman ya yi Shahada ya bar mata daya da yaya hudu, bayan shahadarsa ba jimawa aka haifa masa na biyar.

Ayuba ya kuma shaida mana cewa da yake sun shaku sosai da Shahid Sulaiman, kasancewar shi ke binsa a dakinsu, don haka kamar ya fi kowa jin radadin rashinsa, “Na sha na kasa bacci saboda tunaninsa, amma in baccin ya dauke ni sai na ganshi a mafarki yana bani hakuri, wani lokaci ya ce min na rika karanta masa suratul Khauthar. Nace masa wadanda suka maka wannan aikin fa? Sai yace min na rika karanta musu suratul Fiyl akan Allah ya dauka min fansa a kansu.” Inji shi.

Allah Ya girmama matsayinsa, Ya tsinewa makasansa albarka.

Continue Reading

Tarihin Shahidan Harkar Musulunci

WAKI’AR BUHARI; Shahid Mahmud Ibrahim Gwarzo

Published

on

Shahid Mahmud Ibrahim Yusuf yaro ne dan shekaru 16 a duniya a sadda ya yi Shahada, domin kuwa an haife shi ne a ranar 14 ga Disambar 1999, daidai da 5 ga watan Ramadan 1420H a garin Gwarzo da ke jihar Kano.

Yayansa Malam Tahir Ibrahim (Gwarzo) ya shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Da yake shi mahaifinmu Alaramma ne, yana da makarantar Tsangaya na karatun Alkur’ani da almajirai, to duk yawanci da muka taso karatun Qur’ani ne a ke farawa a gida, don haka shima Mahmud karatun Qur’ani ya fara yi tun tasowarsa din.”

Ya ce: “bayan karatun Mahmud ya dan fara yin nisa a gaban mahaifin namu, a lokacin yana zaune ne a garin Gwarzo ta jihar Kano, sai wani dalili ya sa mahaifin namu ya baro Gwarzo ya dawo wani kauye nan cikin Igabi ta jihar Kaduna da zama, don haka dawowarsa sai na ga dacewar ni kuma na dawo da yaron gidana a nan Zariya.”

Ya cigaba da cewa: “bayan da aka dawo da shi Zariya, sai muka saka shi a makarantar Fudiyya, ya zama yana yin bangaren Firamare da kuma bangaren haddar Alkur’ani Mai Girma, wanda kuma yana aji uku ne (JSS-3) ya yi Shahada.”

Malam Tahir, ya shaidi Shahid Mahmud da kamewa daga shiga abin da bai shafe shi ba. “Idan yana waje in dai ba wani abu da aka sako shi ya yi magana ba, sam ko a cikin yara ba ka jin hayaniyar Mahmud. Kuma lallai ba mu san wani abokin fada ko a kawo karansa a ce ya yi fada da wani ba sam shi.

Yace, Mahmud ya kasance mai mayar da hankali sosai a kan karatunsa. “Har ma na san lokacin ya yi min alwashin cewan insha Allahu kafin shekara mai zuwa yana fatan da shi za a yi bikin yayen Mahaddata wanda za’a yi a nan Fudiyya ta Zaria. Amma Allah bai kai ga cika masa wannan burin ba ya azurta shi da kyakkyawar rabo na shahada.”

Malam Tahir ya bayyana cewa: “A lokacin da Mahmud ya yi Shahada duk mahaifansa biyu suna raye, ita mahaifiyarshi ma a lokacin shahadansa na san ni kaina da nake magana lokacin ina kwance a asibiti a Kano, sakamakon harbin da aka yi min a waki’ar, ta rika zuwa wajena ta gaishe ni har kusan sau uku, amma zuwa biyu ba ta tambaye ni labarinsa ba, sai a zuwanta na uku take tambayata ko akwai labarin Mahmud? Sai nace mata har yanzu bamu da labarinsa. Sai na ga ta yi shiru ta dukar da kai tana jan carbinta. Sannan tace min, Insha Allah in yana raye Allah ya bayyanar mana da shi kuma Allah ya bi masa hakkinsa. Ta yi ta addu’a a kan zaluncin da a ka yi mata.”

Ya ce: “matsayar mahaifinsu kuwa, lokacin da aka ce masa an kashe su, abin da ya ke cewa shine, ya tabbatar dansa addini ya ke yi, idan ya dawo ko ma in bai dawo ba, shi ya tabbatar ɗansa idan an kashe shi to an kashe shi ne a kan addini, don haka bai da damuwa.”

Yayarsa, Malama Zulaiha Ibrahim, ta labarta mana cewa: “ana saura ‘yan kwanaki zai yi shahada, bayan mun fito daga Fudiyya akwai wata jaka a hannusa da nace ya bani ina sonta. Sai yace ba zai bani ba, sai ya yi shahada. Yace idan ya yi shahada sai na je na ɗauka. Sai nace masa kai ne za ka yi shahada a hakan nan? Sai yace min to na tsaya na gani, in saurare shi na gani. Nace to Allah ya nuna mana.”

Tace: “To kawai an yi hakan da kwana biyu sai ga waki’a. To ranar waki’ar mun fito daga Fudiyya aka ce kar kowa ya fita. Sai yace shi gaskiya ba zai tsaya jira har sai an ba shi umarni sannan zai je ya ba jagora kariya ba. Sai nace masa ka bari kar ka fita. Sai yace shi lallai ba zai tsaya ba ya riga ya yi gaba. Sai nace masa to shikenan Allah ya taimaka. Yace amma dai a yayyafi juna. Sai nace Insha Allah.”

Ta cigaba da cewa: “bayan mun fito ne, su sun riga sun yi gaba, sai muka tafi Gyallesu muma. Shi Gyallesu ko Husainiyya ya tafi kai tsaye ban sani ba, amma da muka je Gyallesu, da yake an yi azumi, sai aka ce ya kawo mana abinci na je na amsa. Sai nace wata kawata ta je ta amso mana, sai ya zama dai karshen ganina da shi tun a Fudiyyah din nan ne, shikenan har yau da muke wannan maganar.”

Malam Tahir Ibrahim yace: “Bayan an tashe su daga Fudiyyah, wasu dalibai sun tafi Husainiyyah, wasu kuma suka nufi Gyallesu, to shi Shahid Mahmud na cikin wadanda suka tafi Gyallesu din, da yake yana aiki tare da ‘yan Abul Fadlul Abbas (AS), to kuma daga cikinsu wasu sun bani labarin cewa sun ga lokacin da aka harbe shi. An harbe shi a kirji har ma an ce wurin ya bude, kuma an ce an ga lokacin da aka dauke shi aka shigar da shi gidan Harisawa lokacin yana irin kakarin kamar zai yi Shahada haka a ranar Lahadi (13/12/2015) da safe.”

Allah Ya karbi Shahadarsu. Ya girmama matsayinsu. Ya tsinewa makasansu albarka.

Continue Reading

Tarihin Shahidan Harkar Musulunci

Shahid Faisal Abdulƙadir Gilima

Published

on

Shahid Faisal Abdulkadir Gilima, daya ne daga matasa masu kokari, wadanda suke bayar da gudummawa ga Harkar Musulunci a Nijeriya a bangaren Mu’assasar Abul Fadl Abbas (RA).

An haif Faisal ne a garin Mubi ta jihar Adamawa, a ranar Laraba 15/5/1991 (daidai da 1 ga Zulkida, 1411H). Kasancewar mahaifiyarsa kanwa ce shakikiya a wajen dan uwa Engr. Yahya Gilima, don haka bayan rasuwar mahaifinsa a lokacin yana dan shekaru kimanin 12, sai ya dawo gidan Alhaji Gilima da rayuwa.

Lokacin da mahaifinsa ya rasu, bai kammala makarantar Firamare ba, don haka sai mahaifiyarsa Malama Amina ta tsaya a garin Mubi har sai da ya kallama Firamaren, sannan sai ta dawo wajen dan uwanta a Kaduna, inda ta danka masa rikon dan nata tun yana da shekaru 12 har zuwa lokacin da ya yi Shahada a ranar 13/12/2015 a Zariya, lokacin yana da kimanin shekaru 24 a Duniya.

Marikiyarsa, wacce ta mayar da shi tamkar daya daga ‘ya’yan da ta haifa, wato Malama Jummai Ahmad Karofi, ta bayyanawa Cibiyar Wallafa cewa; “Bayan ya dawo hannunmu da shaidar gama Firamarensa, sai muka saka shi a makarantar Sakandire mai suna Destiny School da ke unguwar Malali a Kaduna. Bayan ya kammala aji ukunsa a nan, sai muka komar da shi makarantar Federal Government College Kaduna, inda ya kammala karatun Sakandirensa a nan.”

Ta cigaba da cewa: “Daga nan, an nema masa ‘admission’ a Kaduna State Polytechnic, inda aka bashi ‘course’ din Lab Technology, amma sai ya nuna rashin sonsa ga wannan fagen, don haka daga sai muka bar shi da zabinsa, daga baya shi da kansa ya nema wa kansa ‘admission’ a Jami’ar KUDS Wudil ta jihar Kano, inda ya karanta Geography. Kuma yana ajinsa na karshe (400l) aka yi waki’ar Zariya, a lokacin ya gama karatun ma, yana kan rubuta ‘Project’ ne, suka tafi Zariya, inda kuma shikenan.”

Ta bayyana shi a matsayin yaro mai riko da addini, musamman saboda yadda ya shaku da yaronta mai suna Ibraheem, wanda shi ma ya kasance mai kokarin aikata addini tun suna yara, don haka sai ya zama Faisal na kokarin ganin ya yi koyi da yayansa Ibraheem a fagen ibada da kokari.

Tace, tun farkon assasa Mu’assasatu Abul Fadl Abbas a Zariya, da nufin taimakawa Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a ranar da aka yi taron assasata, a ranar ta yi magana da shugaban Mu’assasar, Sayyid Shahid Ahmad Zakzaky, inda ta bukaci a sanya ‘ya’yanta guda biyu; Faisal Abdulkadir da yayansa Khalid Yahya Gilima su zama daga mambobin Mu’assasar.

An shaidi Shahid Faisal da kokarin neman na kansa da rashin kasa. “Ya kasance yaro mai kokari da son neman na kansa, domin ko a sadda ya ke karatun jami’a ya kasance yakan saro yadiddika ya bada a dinka masa sun a maza, yana saidawa.” Inji Hajiya Jummai.

Faisal ya tafi Zariya tare da ‘yan uwansa hudu a lokacin waki’ar Buhari ta 12/12/2015, inda kuma tun daga ranar Lahadi 13 ga Disambar 2015 ba a sake jin labarinsa ba, don haka ana kaddara cewa yana daya daga cikin daruruwan Shahidan da sojojin Buhari suka Shahadantar a Zariya.

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.