Shahid Ali Mu’azu, da ne ga Malam Mu’azu Ishaq Mai fata. Sunan mahaifiyarshi Maryam Dalhatu. Shi kani ne ga Shahid Muhammad Mu’azu.

An haife shi ranar 14 ga watan Afrilun 1999 daidai da 27 ga watan Zulhijja, 1419H a cikin Karamar Hukumar Sabon-Garin Zariya da ke jihar Kaduna. Kuma ya yi tsawon rayuwarsa tun daga haihuwan shi har zuwa shahadarsa tare da mahaifansa a gidansu da ke Unguwan Jaba da ke Sabon-Gari.

Shahid Ali ya fara karatun Addini ne a Markazu Shahid Abubakar Madomawa da ke Unguwan Jaba, sannan kuma ya yi Kismul Tahfizul Kur’anil Karim ta Malam Mustafa Kismi, daga karshe kuma ya koma Darul Imam Mahdi (A.F) da ke ‘Yan awaki Muciya, wanda a nan ne ya samu albarkacin sauke Alkur’ani mai girma.

A bangaren karatun boko kuwa, Shahid Ali ya yi daga ‘Nursery’ har zuwa kammala Firamare a makarantar Ar-Rayyan Islamic Nursery and Primary School. Daga nan aka saka shi a makarantar Demonstration Secondary School da ke cikin ABU Samaru, a nan ya yi daga JSS 1 zuwa JSS 3. Sai kuma ya koma Goodwill International school, inda ya daura daga SSS 1 har zuwa SSS 3, yana ajin karshe na kammala sakandiren ne ya riski shahada, a lokacin yana dan shekara 17 a duniya.

Duk da yake yaro ne a shekaru, Shahid Ali ya rungumi gyaran waya da Kwamfuta da wasu kayan lantarki a matsayin sana’arsa. Allah ya bashi hazaka ta yadda duk yana wadannan gyaran ne ba tare da ya taba zuwa wani waje ya koya ba. Bayan wannan kuma da yake shi mai sha’awar harkan kasuwanci ne, ya kasance ya kan saro layukan waya da irin su ‘memory card’ yana sayarwa.

Da yake duk mahaifansa ‘yan Gwagwarmaya ne tun kafin su haife shi, don haka Shahid Ali ya taso ne a cikin Gwagwarmayar yunkurin tabbatar da addinin Musulunci wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke jagoranta. Saboda haka, za a iya cewa tun daga haihuwarsa har zuwa shahadarsa ya yi su ne a cikin Gwagwarmayar addini.

Kanwarsa Fatima Mu’azu ta shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Tun tasowar Shahid Ali sam bashi da wani buri da ya wuce ya rika aikin ba da kariya ga Jagoransa Sayyid Zakzaky Hafizahullah, da kuma kawo cigaba a cikin wannan Harka ta Musulunci. Don ganin hazaka da kokari irin nashi ne ma tun bai wuce shekaru 14 ba aka dauke shi a lajanar Mu’assasatu Abulfadl Abbas (AS), kuma duk da karancin shekarunsa ya bayar da gudummawa a Mu’assasar iyakar iyawarsa.”

Ta kara da cewa: “Ya kasance ya sadaukar da komai nashi ga wannan Harka, wanda ya hada da lokaci, dukiya da ma rayuwarshi gaba daya. Da yake suna ‘duty’ na ba da kariya ga Jagora (H) a gidan sa da ke Gyellesu, to ya kasance kusan can din ne ma ya koma kamar wajen da ya fi rayuwarsa, don duk lokacin da aka yi hutun makaranta to yana komawa can ne da zama baki daya.”

Shahid Ali baya ga wadannan ayyukan da yake na baiwa Harkar Musulunci gudummawa, har ila yau kuma ya rika ba da gudummawa wajen aikin yada sakon Harkar (media), musamman aikin mayar da jawaban Jagora (H) kwamfuta daga kaset mai zare. Sannan ya rika aiki da mawakan Wilayatul Haq, inda ya kan yi musu amshi wakokin gwagwarmaya da suke yi.

Fatima Mu’azu ta shaida mana cewa: “dama Shahid Ali na daya daga cikin wadanda aka raunata a harin da sojojin Najeriya suka kai ma muzaharar Qudus ta shekarar 2014. Sun harbe shi ne a hannun shi na hagu, wanda ya dauki tsawon fiye da watanni uku a asibiti yana jinyar hannun, a karshe kusan duka yatsun da suke hannun hagun nashi baya iya amfani da su yanda ya dac, amma wannan bai sa ya yi sanyi ko ya ja baya ba, sai ma kara kaimi da yayi, domin kuwa da samun saukin shi ya dawo ya cigaba da aikin ba da kariya ga Jagora (H). Kuma bayan aukuwar wannan (waki’ar Quds din) da shekara daya da ‘yan watanni kuma Allah Ta’ala Ya azurta shi da samun rabon shahada a gidan Jagora (H) a waki’ar Buhari ta 2015.”

‘Yan gidansu, sun shaide shi da dabi’un kamala da suka hada da dauriya, jarumta da kuma hakuri. “Ya kasance mutum me dauriya da hakuri, ba shi da yawan surutu, sannan yana da gaskiya da rikon amana, da kuma kyauta. Sannan ya kasance yana da sha’awar yin kasuwanci sosai, ba don komai ba sai dan ya dogara da kan shi kuma ya taimaki Addinin Allah.” Inji mahaifiyarsa.

Malama Hasana, ta kara da cewa: “Ali yaro ne mai kunya sosai, dan ko hada ido da mutane bai cika son yi ba, tun yana jariri yana da wata dabi’a; sam baya son wata ko wani su ga tsiraicinsa, tun lokacin bai iya magana ba idan ba wando a shi za ta ga ya takura sosai, har ya zo ya zama bayan bakin shi ya bude sai ya rika fada mata a saka mishi kaya. Haka kuma idan sun fita unguwa da shi ba ya taba yin abun da ya san cewa zai sa a cire ko a canja mishi kaya a cikin mutane, yana jira ne har sai sun koma gida sannan. Wannan dabi’ar ta kunya ta cigaba masa har zuwa girman shi, har shahadarsa.”

Ta cigaba da cewa: “Ali ya kasance yana da yawan fara’a da tausayin kannensa. Kuma ba shi da abokin fada sam, don haka ba a taba kawo karanshi wai cewa ga shi ya yi ba daidai ba. Mutum ne mai hazaka da fikira sosai, domin duk karatun da a ka yi masa a makaranta yana haddacewa ne, sau daya idan aka koya mai abu shikenan zai iya, don haka ko da yaushe yana zuwa na daya ne a ajin su. Kuma malamanshi ma sun shaidi cewa a aji sam ba ka jin surutu ko hayaniyarsa, amma da zaran an yi tambaya shi ke fara daga hannu ya bada amsa.”

Mahaifinsa Malam Mu’azu Ishaq ya shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa: “Gaskiya wannan yaro (Shahid Ali) bamu san komai a dangane da shi ba sai dai alkhairi, don gaskiya mutum ne mai kyawawan dabi’u da tausayi da biyayya a gare mu.”

Babban burin Shahid Ali Mu’azu a rayuwa shine ya wanzu cikin ba da kariya ga Jagoran Harkar Musulunci, kuma Allah Ya cika masa wannan burin a yayin da ya azurta shi samun shahada a gidan Sayyid Zakzaky (H) a yayin harin da sojojin Najeriya suka kai masa a waki’ar Buhari ta 2015, wacce ta kasance ranar 1 ga Rabi’ul Auwal din 1437H.

A ranan Asabar din (12/12/2015) da sojoji suka zo Husainiyyah lokacin shi ma Shahid Ali yana Husainiyyah din, sai aka saka shi ya raka su Shahid Sayyid Ali Haidar da Shahid Sayyid Humaid zuwa gida, tunda a lokacin can Gyallesu din lafiya lau ne, to haka ne yasa ya zama waki’ar ta riske shi a Gyallesu ne har ya samu rabon Shahada.

Mahaifansa sun shaida mana cewa, wata ‘yar uwa daga cikin wadanda ke gidan Shaikh Zakzaky a lokacin waki’ar, Amma Maryam Shelleng ta shaida musu cewa, daidai lokacin da sojoji suka hauro cikin gidan Sayyid Zakzaky (H) ne suka harbe shi a kai, lokacin yana tsaye daidai kofar da take kaiwa zuwa filin da lilo yake a gidan. Wannan kuma ya faru ne a ranan Lahadi, 13/12/2015.

Shahid Ali ya yi shahada ya bar mahaifansa biyu a raye, sai yayar shi guda daya mace, da kannen shi guda uku. Akwai yayan shi kuma Shahid Muhammad Mu’azu, wanda shi ya yi shahada ne tun ranan Asabar, tazarar kwana daya tsakanin Shahadarsu. Amincin Allah da yardarsa a gare su.

Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
cibiyarwallafa@gmail.com
12/11/2022 (17/4/1444H).

No responses yet

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *