Connect with us

Labarai

Muzahararorin Quds 2023/1444 A Nijeriya

Published

on

Fiye da garuruwa 50 ne suke gabatar da Muzaharar Quds a wannan shekarar ta 1444H/2023 a Nijeriya.

Muzaharar wacce, ake gudanar da ita a kowace Juma’ar karshen watan Ramadan, tun bayan fatawar Imam Khumaini (QS) a kan haka a shekarar 1979, inda ya yi kira ga daukar Juma’ar karshen watan Ramadan a matsayin ranar da duk al’ummar Musulmin duniya za su hadu wajen fitowa su bayyana goyon bayansu ga raunanan al’ummar Palasdinu da Yahudawan Sahayoniya suke zalunta a kokarinsu na mamaye yankin da kafa haramtacciyar kasar isra’ila.

A Nijeriya, tun a shekarar 1984 Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky take gudanarwa, a tsawon wadannan shekaru kusan 40 din, Muzaharar nuna goyon bayan Palasdinawan na kara habaka ne a kowace shekara, inda a farko ana yi ne a birnin Zariya kawai, daga baya aka koma yi a wasu birane kimanin 20 a fadin kasar, inda a yanzu a kan gudanar a birni da kauyuka fiye da 50, duk a ranar Juma’ar karshen Ramadan din.

Izuwa yanzu, wakilanmu daga garuruwa sun fara aiko mana da rahotonnin yadda Muzaharar tasu ta kasance. Gasu nan tafe a kasa:

 

1- ABUJA

Daga Ali Sajjad Tahir

Dubun dubatan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky ne suka fito Muzaharar Quds a ranar Juma’a 23 ga Ramadan, 1444 (14/4/2023) a birnin Abuja.

Muzaharar, wacce aka fara ta da misalin karfe 2 na rana daga masallacin Juma’ar Costom da ke Wuse Zone 3 a tsakiyar Abuja, ta kunshi ‘yan uwa maza da mata daga sassa daban-daban na kasar Nijeriya.

Fara muzaharar ke da wuya gamayyar jami’an tsaron ‘yan sanda da na soja suka fara bude mata wuta, amma cikin taimakon Allah ‘yan uwan suka dake suka cigaba da tafiya suna kabbarori tare da maimaita kalmar #FreePalestine.

Duk da harbe-harben da jami’an tsaro suka rika yi, muzaharar bata tsaya ba sai da ta je Beger, a yayin da ‘yan uwa suka raba musu hankali, tsiraru suka fuskanci waki’ar, mafi yawa kuma suka cigaba da muzaharar.

Izuwa yanzu muna da tabbacin an samu Shahidi guda daya, mai suna Shahid Yaqoub Umar, da kuma adadin wadanda aka raunata, sakamakon harbin da jami’an tsaron suka kara yi bayan an kammala muzaharar.

          Ga wasu daga hotunan da muka dauka:

 

2- KADUNA

Daga Muhammad Rabil

A garin Kaduna ma, ‘yan uwa sun fito Muzaharar Quds din, wadda aka faro ta da misalign karfe 2 na rana daga titin Kano Road, aka bi titin Ibrahim Taiwo Road, sannan aka isa Bakin Dogo, inda a nan ne wakilin ‘yan uwa na Kaduna, Malam Aliyu Tirmizi ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Sai dai ana fara Muzaharar, a daidai shataletalen Leventis da ke Kaduna,  jami’an ‘yan sanda suka bude wuta akan masu muzaharar, suka raunata wasu kwarorin ‘yan uwa. Sai dai hakan bai sa Muzaharar ta tsaya ba, sai da aka kaita inda aka tsara rufe ta.

          Ga wasu daga hotunan da muka dauka yayin Muzaharar:

 

3- BAUCHI:

Daga Nusaiba Ahmad

Dubun dubatan al’ummar Musulmi ne suka fito Muzaharar ta Quds a ranar Juma’a 23 ga Ramadan, 1444 (14/4/2023) a garin Bauchi.

Muzaharar ta faro ne a Fudiyyah da ke unguwar Shagari da misalin karfe 9:23 na safiya, inda ta bi hanyar bariki, ta zagaya ta shatale-talen kofar fada, ta mike babbar hanyar titin wunti, daga nan ta shiga ta titin tashar babiye, ta bi ta bakin kura, ta shiga kofa sannan ta zagayo ta yi burki a masallacin Ajiya da ke tsakiyar garin Bauchi.

An kammala Muzaharar da misalin karfe 11:30ns, inda wakilin ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na Bauchi, Malam Ahmad Yusuf Yashi ya gabatar da jawabin rufewa.

Muzaharar garin Bauchi ta samu halartan ‘yan uwa daga garuruwan yankin Bauchi da dama, da suka hada da Liman Katagum, Alkaleri, Kafin Madaki, Ningi, Soro, Giyade, Kyangyare, Warji, Gubi da sauransu.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar Bauchi:

 

 

4- SOKOTO

Daga Halidu Shahid Usman

A garin Sokoto, muzaharar ta fara ne da misalin karfe 9 na safiya da masallacin Alhazai da ke bayan City Campus, ta biyo ta shataletalen Diploma, ta shiga unguwar rogo, daga nan ta isa Mabera, inda aka rufe ta a wajen gidan Shahid Qasim Umar Sokoto.

Dubun-dubatan ‘yan’uwa daga garuruwan yankin Sokoto da Kebbi da Zamfara ne suka halarci Muzaharar. A bana, al’ummar garin na Sokoto sun rika yabawa da Muzaharar, ba kamar yadda aka saba a baya inda su kan rika kokarin cutar da ‘yan uwa idan sun fito ba.

Wakilin ‘yan uwa na Sokoto, Shaikh Sidi Munir ne ya gabatar da jawabin rufewa. Daga nan aka kona tutar Amurka da ta haramtacciyar kasar isra’ila.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar Sakkwato:

 

5- NGURU

Daga Abubakar Abdullahi

Da misalin karfe 8:15 na safiya aka fara Muzaharar Quds a garin Nguru da ke jihar Yobe, inda dubban ‘yan uwa daga garuruwan Bambori, Garbi, Dogon Jeji, Dumur da sauransu suka halarta.

Muzaharar ta faro ne daga titin Kwamared Bashir Sharrif, ta bi ta layin FMC, aka mike titin masallacin FK, aka miko bakin kasuwa, aka bi ta layin Gimba, daga nan aka yi kwana a daidai shataletalen Mr. Lass aka mike zuwa babban masallaci da ke kofar Fadar Nguru aka rufe ta.

Wakilin ‘yan uwa na Da’irar Nguru, Malam Aliyu Saleh ne ya yi jawabin rufewa.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar Nguru:

 

6- MASHI

Daga Salahudden Bello Sheme

A garin Mashi ta jihar Katsina ma, ‘yan uwa Musulmin daga garuruwan Mani, Maduru, Doro, Mashi da sauransu sun fito Muzaharar Quds da safiyar ranar Juma’a 23 ga Ramadan 1444.

Muzaharar wacce aka fara ta daga Markaz din ‘yan uwa na Mashi da ke sabon layi da misalin karfe 8:20 na safiya, ta mike ta hau titin Mani, ta bi ta sabon titi ta shiga unguwar kashe-naira, sannan ta dawo ta kan babban titin Katsina/Daura, inda ta isa bayan gidan NEPA da ke rijiyar alkali kusa da kotu, aka rufe ta a nan da misalin karfe 9:30ns.

Daruruwan ‘yan’uwa maza da mata ne, dauke da tutoci da banoni da suke alamta dalilin fitowarsu Muzaharar suka gudanar da ita. A yayin da wakilin ‘yan uwa na Da’irar Doro, Malam Abdulkadir Nunu ya gabatar da jawabin rufewa. Sannan Malam Sadisu Abdullahi ya yi addu’ar rufewa.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar Mashi:

 

7- AZARE

Daga Lawal Bala

A garin Azare ta jihar Bauchi, an fara Muzaharar ne bayan sallar Juma’a, da misalin karfe 2:26 na rana.

Bayan tashinta daga babban masallaci na kofar Fada, sai aka bi ta titin Sule Katagum, aka bi layin hedikwatan ‘yan sanda, sannan aka shiga layin Babani Dun Buran, aka shigo ta unguwar tsakuwa, sannan aka dawo ta kofar gari, inda aka rufe ta Sule Katagum Road da ke Azaren.

Muzaharar ta kunshi ‘yan uwa daga Da’irorin Azare, Zaki, Gamawa, Misau, Zabi, Zadawa, Giade, Shira, Yana, Jama’are, Itas, Gadau, Raga, Udubo da sauransu.

Malam Sa’id Aliyu ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Ga wasu daga hotunan da muka dauka:

 

8- POTISKUM

Daga Ibrahim El-Tafsir

Dubban ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky na yankin Potiskum, wadanda suka hada ‘yan uwa daga Da’irorin Potiskum, Gashua, Jaji Maji, Damaturu, Fika, Gadaka, Nafada, Dambam, Dagauda, Bulkacuwa, Dawasa da sauransu, su ma sun fito Muzaharar Quds a wannan rana, domin nuna goyon bayansu ga raunanan al’ummar Palasdinu.

An faro Muzaharar ne daga makarantar Fudiyya Potiskum, inda zagayen Muzaharar ya karade kusan duk manyan titunan cikin garin Potiskum, a karshe aka rufe ta a filin wasa na Government Day Potiskum.

‘Yan uwa reras a cikin sahu, dauke da tutocin Palasdin, da banoni da kuma fastoci na #FreePalestine da #ReleaseShaikhZakzakysPassport, a yayin da mawakan Harka Islamiyya ke tafe suna raira wakokin ‘yanto masallacin Quds mai alfarma.

Duk da yanayi na rashin lafiya da wakilin ‘yan uwa na Potiskum. Malam Ibrahim Lawal yake ciki, ya samu halartar Muzaharar. Sai dai Malam Musa Fika ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

          Ga wasu daga hotunan Muzaharar:

 

9- LAFIA

Daga Saleh Haruna Nass

A garin Lafia ta jihar Nasarawa ma, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun bi sahun sauran al’ummar duniya wajen gudanar da Muzaharar Allah wadai da zaluncin isra’ila a kan Palasdinawa a yau Juma’a 23 ga Ramadan 1444.

Da misalin karfe 2:33 na rana bayan kammala sallar Juma’a, ‘yan uwan da suka fito daga Da’irorin yankin Lafia kamar Doma, Agyaragu, Nasarawn Eggon, Makurdi, Azara, Shendam, Yelwa Shandam da Akwanga, suka fara gudanar da Muzaharar daga masallacin Gabas da ke hanyar Makurdi, aka bi ta babban titi, aka zagayo ta hanyar Doma, sannan aka dawo aka rufe ta a kofar sarkin Lafiyan Bare-bari.

Walikin ‘yan uwa na Lafia, Malam Muhammad Nura ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Ga wasu daga hotunan da muka dauka:

 

10- KATSINA

Daga Bin Yaqoub Katsina

Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Katsina da kewaye su ma sun gudanar da Muzaharar ta Quds a ranar Juma’a 23 ga Ramadan 1444.

An fara Muzaharar ne daga babban masallacin Juma’ar Katsina, da misalin karfe 2:18 na rana, jim kadan bayan idar da sallar Juma’ar. Daga nan aka nufi Mobile, aka isa shataletalen tsohuwar tasha, aka shiga sabon layi, sannan aka bi ta kerau, daga nan kuma aka isa tsohon filin wasanni na Katsina inda aka rufe ta a nan.

Muzaharar ta kunshi ‘yan uwa daga Da’irorin Katsina, Charanci, Rimi, Abukur, Jibiya, Kudan Daga, Dutsen Safe, Kwarin Tama, Shinkafi Kaita, Kayauki, da sauransu, inda kuma ta shafe kusan awa biyu tana gudana kafin a rufe ta. Wakilin ‘yan uwa na Katsina, Shaikh Yakubu Yahya ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar:

 

 

11- ZARIYA

Daga Ali Ibrahim Yareema

A garin Zariya ta jihar Kaduna ma, dubun-dubatan ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky ne suka fito Muzahar ta Quds a ranar Juma’a.

An fara Muzaharar ne daga masallacin Juma’a na Gwargwaje da misalin karfe 2:30 na rana, inda ta bi ta kofar Kuyan Bana, ta ratso kasuwar Zariya, ta taho zuwa Babban Dodo, inda aka rufe ta a nan.

‘Yan uwa daga yankin Zariya da suka hado Da’irorin Funtua, Kudan, Kidandan, Soba, Zariya da sauransu ne suka gudanar da Muzaharar, wacce ta shafe kusan awa daya da rabi kafin a rufe ta, inda wakilin ‘yan uwa na Zariya, Shaikh Abdulhamid Bello ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar:

 

12- GOMBE

Daga Nasir Miji

Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na yankin Gombe ma sun gudanar da Muzaharar ta Quds, wadda ta aka faro ta daga babban masallacin Juma’a na kofar sarkin Gombe jim kafan bayan idar da sallar Juma’a.

Da misalin karfe 2:30 na rana ne aka fara Muzaharar, wanda dubban ‘yan uwa daga Da’irorin Bajoga, Dukku, Kwadon, Kumo, Filiya, Lakum, Pindiga, Talasse, Fikayel da sauransu ne suka halarta. ‘Yan uwan sun rika tafiya suna raira taken nufin ‘yanto masallacin Quds daga hannun Yahudawan sahayoniya, da kuma kira ga gwamnatin Nijeriya kan ta sakewa Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibrahim fasfo dinsu, domin su fita kasar waje neman lafiya.

Muzaharar ta samu ado da tutocin Palasdinu, inda aka rika jan tutocin Amurka da ta isra’ila a kasa, sannan kuma da hotunan Jagora da na iyalansa gami da na Shuhada masu girma. Daga masallacin Juma’a ta mike ne zuwa shataletalen cikin gari, sannan ta mike ta titin sabon layi, ta shiga ta kasuwa ta fito ta Idi, inda aka rufe ta a nan.

Wakilin ‘yan uwa na Gombe, Shaikh Muhammad Adamu Abbare ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar da misalin karfe 4:30 na yamma.

Ga wasu daga hotunan da muka samu:

 

13- KANO

Daga Muhammad Hadi (Jadda)

A birnin Kano ma, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun gabatar da Muzaharar ta Quds a ranar Juma’ar, inda aka faro ta daga masallacin Juma’a na Fagge, aka bi ta titin Wafa, aka bi ta titin Katsina Road ta isa shataletalen Hajj Camp, daga nan aka juya aka bi da ita ta kofar Mazugal inda ta isa filin Dalar Gyada aka rufe ta a muhallin.

Muzaharar ta Kano, kamar sauran garuruwa, ta kunshi nuna goyon bayan al’ummar Palasdinu da kuma kira ga gwamnatin Nijeriya kan ta baiwa Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah ‘Passport’ dinsu, don su samu damar fita waje neman lafiya.

Muzaharar ta kunshi dubun-dubatan ‘yan uwa daga ‘zones’ takwas din da ke yankin Kano, wadanda suka hada da Kura, da Birnin Kudu, da Gumel, da Gwarzo, Durbunde, da Ringim da sauransu. Wakilin ‘yan uwa na Kano, Dakta Sunusi Abdulkadir ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Ga hotunan da muka dauko:

 

14- DANDUME

Daga Haidar Mahmud, da Nazifi Ayuba

A garin Dandume ta jihar Katsina ma, ‘yan uwa sun gabatar da Muzaharar ta Quds da safiyar wannan ranar.

Muzaharar wadda ta kunshi maza da mata rike da hotuna da banoni gami da tutocin Palasdinu da na kira ga gwamnatin Nijeriya ta saki ‘Passport’ din Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah, ta taso ne daga makarantar Fudiyyar Dandume ta hau titin Abdu Yaro, ta nufi shataletalen babban titin cikin gari, daga nan ta karade lungu da sakon garin, ta dawo bayan asibitin kasuwar mata inda aka rufe ta a nan.

Wakilin ‘yan uwa na Dandume, Malam Abdullahi Khamis ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar. Inda bayan kammala jawabinsa, aka kona tutar Amurka da ta isra’ila, sannan aka yi addu’a aka sallami jama’a.

Ga wasu daga hotunan da muka dauka:

 

15- JOS

Daga Ibrahim M. Tahir

Su ma ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na garin Jos ba a bar su a baya ba, a wannan Juma’ar ta karshen watan Ramadan 1444, sun bi sahun al’ummar duniya, wajen fitowa Muzaharar nuna goyon bayansu ga raunanan al’ummar Palasdinu, da kuma yin Allah wadai da haramtacciyar kasar isra’ila da ke kashe Palasdinawa tun fiye da shekaru 80 da suka wuce.

Muzaharar ta garin Jos, wacce ta kunshi ‘yan uwa daga Da’irorin yankin Jos, kamar Rinji, Barikin Ladi, Gumau, Jos da sauransu, ta faro ne da misalin karfe 2:15 na rana, bayan idar da sallar Juma’a a babban masallacin Juma’ar Jos, inda aka faro ta daga ‘yan dankali aka gangara ta cikin kasuwar New Market aka bulla babban titin Bauchi Road, sannan aka shiga ta layin sarki, aka sake dawowa ta layin mangoro inda ta isa bakin babban masallacin Juma’a da ke tsakiyar garin.

Wakilin ‘yan uwa na Jos, Shaikh Adamu Tsoho Ahmad ne ya gabatar da jawabin rufe Muzahar.

Ga wasu daga hotunan da muka dauko:

 

16- SAMINAKA

Daga Ibrahim Almustapha

A garin Saminaka ta jihar Kaduna ma, ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun gudanar da Muzaharar Quds don nuna goyon baya ga raunanan al’ummar Palasdinu da isra’ila ke zalunta, a ranar Juma’a 23 ga Ramadan 1444H.

Muzaharar wadda ta kunshi ‘yan uwa daga Da’irorin yankin Saminaka da suka hada da Lere, Ramin Kura, Garu, Mariri, Agaji, Kayarda da sauransu, ta fara ne da misalin karfe 3:00 na rana daga Fudiyyar hayin gada, inda ta miko babban titin garin, bayan shafe kusan awa biyu ana tafiya, ta iso cikin tashar mota (‘yan katako) inda aka rufe ta a nan.

Bayan isowarta muhallin rufewa, an gudanar da wakokin neman ‘yancin Palasdinawa, da kuma kira ga gwamnatin Nijeriya kan ta saki ‘Passport’ din Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah don su fita waje neman lafiya. Daga bisani, wakilin ‘yan uwa na Da’irar Saminaka, Shaikh Yusuf Abubakar ya gabatar da jawabin rufewa.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar:

 

17- YOLA

Daga Shafi’u Saleh

A garin Yola, babban birnin jihar Adamawa, ‘yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun bi sahun al’ummar duniya, wajen gudanar da Muzaharar Allah wadai da mamayar haramtacciyar kasar isra’ila ga al’ummar Palasdinu.

Muzaharar wadda aka fara ta da misalin karfe 2:25 na ranar Juma’a, da gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, duk da tsananin zafin rana da kuma azumi da ake yi.

An fara Muzaharar ne daga babban masallacin Juma’a na Nasarawo, aka ratsa babban titin Muhammad Mustapha, aka bi ta bakin kasuwar Jimeta aka komo ta hanyar Zaranda street, sannan aka ratsa titin Wukari street inda aka rufe ta a kofar shiga makarantan Sakandiren gwamnatin jihar (Capital School).

Malam Usman Sa’ad ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar. Inda bayan nan aka kona tutar Amurka da isra’ila kurmus, sannan aka gabatar da Malam Dalhatu Musa ya rufe da addu’a.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar da muka samu a shafin Adamawa Press Team:

 

18- GUSAU

Daga Lawal Maigari

Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a garin Gusau ta jihar Zamfara ma sun gudanar da Muzaharar ta Quds a ranar Juma’ar karshen Ramadan.

An fara Muzaharar ne da misalin karfe 3:20 na rana daga Masallacin Kanwuri, inda aka bi titin gidan sarki, aka hau hanyar tsohuwar kasuwa, daga nan aka isar da ita shataletalen Bello Barau aka rufe ta.

‘Yan uwa daga Da’irorin Kauran Namoda, Tsafe, Talatar Mafara da Gusau ne suka halarci Muzaharar, wadda Malam Shu’aibu S. Kaya ya gabatar da jawabin rufe ta, Malam Sada Muhammad Ladan kuma ya yi addu’ar rufewa.

Ga wasu daga hotunan Muzaharar:

 

 

19- BIRNIN KEBBI

Daga Alhussaini Nasir

A Birnin Kebbi ma, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun jagoranci Muzaharar ta Quds don nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu a ranar Juma’a 23 ga Ramadan, 1444.

Muzaharar wacce ta kunshi ‘yan uwa daga Da’irorin yankin Kebbi da suka hada Gwandu, Jega, Andarai, Gwadangaji da sauransu, an fara ta ne bayan idar da sallar Juma’a daga babban masallacin Juma’a na garkar sarki da ke cikin Birnin Kebbi, inda aka bi da ita babban titin tsakiyar gari, a karshe aka rufe ta a shataletalen Rabin Atiku.

Wakilin ‘yan uwa na Birnin Kebbi, Malam Umar Bello ne ya gabatar da jawabin rufe Muzaharar.

Ga wasu daga hotunan yadda Muzaharar ta gudana:

 

Za mu cigaba da dorawa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini

Published

on

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2024, Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa dandalin daliban harkar Musulunci a Nigeriya, a gidansa da ke Abuja.

Kamar yadda Ofishin Jagoran ya Wallafa cewa an yi ganawar ne a ranar Litinin 26 Zuqadah 1445, wanda ya yi daidai da 3/6/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.