Connect with us

Labarai

Muzaharar Goyon Bayan Palasdinawa A Kaduna; An Samu Shahidai 2

Published

on

Da misalin karfe 11 na safiyar Ranar Alhamis 16/11/2023 (2/5/1445) ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Kaduna, suka fita Muzaharar nuna goyon baya ga raunanan al’ummar Palasdinawa da Yahudawan Isra’ila ke kashewa.

Muzaharar wacce ta kunshi mata da kananan yara, an faro ta ne daga Nepa Roundabout da ke tsakiyar garin Kaduna, ta isa gaban ofishin Hukumar kare hakkin ɗan Adam (Human Right Commission), sai ga jami’an ‘yan sandan Mopol nan, suna zuwa suka fara bude wuta, da harbi da bindiga da Tiyagas, inda suka jikkata gomomin ‘yan uwa, a yayin da biyu daga ciki zuwa yanzu suka cika sakamakon harbin.

Shahidan su ne; Shahid Sidi Anas Kaduna, wanda matashi ne dan kimanin shekaru 30, yana da mata da yarinya daya, sai kuma Shahid Muhsin Abubakar, wanda shi yaro ne dan kimanin shekaru 15 da haihuwa.

A yayin Muzaharar, yan uwa mata sun rike abubuwan da ke alamta jariran Palasdinawa da Isra’ila ke kashewa a tsakanin nan, musamman a hare-haren da Haramtacciyar ƙasar isra’ila din ke kaiwa a yankin Gaza a asibitoci, makarantu da gidajen al’umma, wanda yau kimanin kwanaki 40 kenan ana cikin wannan halin.

Ga wasu daga hotunan da wakilinmu Muhammad Rabil ya turo mana na yadda Muzaharar ta gudana.

— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)

Tuntuba: cibiyarwallafa@gmil.com

Website: www.cibiyarwallafa.org

#FreePalestine

#PalestinianLivesMatter

#PalestineWillBeFree

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini

Published

on

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2024, Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa dandalin daliban harkar Musulunci a Nigeriya, a gidansa da ke Abuja.

Kamar yadda Ofishin Jagoran ya Wallafa cewa an yi ganawar ne a ranar Litinin 26 Zuqadah 1445, wanda ya yi daidai da 3/6/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.