Connect with us

Labarai

Muhimman Bayanan Sayyid Khamene’i A Yayin Ganawarsa Da Shaikh Zakzaky

Published

on

Jagoran juyin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Khamene’i ya gana da Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, matarsa, da ‘ya’yansa a ranar Asabar 14/10/2023 (29 Rabi’ul Auwal 1445).

A yayin ganawar, Imam Khamene’i, ya bayyana cewa, karfin Musulunci na karuwa a dukkan sassan duniya, duk da kokarin bata shi da makiya ke yi ta hanyar yada karairayi a kansa, da nuna shi a mummunan kama, kuma hakan sakamako ne na kokarin ‘yan gwagwarmaya.

Da yake bayani dangane da yanayin Palasdinu, musamman Gaza, Jagoran ya bayyana cewa: “Daya daga tabbacin bayyanar karfin Musulunci a wannan lokaci, za a iya ganinsa a cikin abin da ke faruwa a Palasdinu.”

Yace: “Abubuwan da suka bayyana a Palasdinu a cikin kwanakin nan, musamman jefa bama-bamai, da shahadantar da mata da yara da mazaje, yana raunata zukatan al’umma.” Ya kara da cewa: “Amma duk da haka, ta wani bangaren al’amarin ya bayyana karfin da Musulunci ke da shi a Palasdinu. Insha Allah, wannan gwagwarmayar da aka fara a Palasdinu zai cigaba har ya kai ga samun cikakken nasarar Palasdinawa.”

Ya kuma bayyana cewa: “Jamhuriyar Musulunci tana kara karfi a kowace rana tun sadda aka samar da ita, kuma za ta cigaba da karfi a nan gaba.”

Yace, motsin Musulunci na karuwa a kullum a dukkan sassan duniya. “A yau, Harkar Musulunci na mamaye dukkan sassan duniya, kamar su Afirka, Asia, Europe (Kasashen Turai) da Kudancin Amurka. Da yardar Allah, nasarar wannan gwagwarmaya zai cigaba da karfafa matuka.”

A yayin ganawar, Jagoran Juyin Musulunci ya bayyana jin dadinsa bisa ganawa da Shaikh Zakzaky da iyalansa, ya kuma jinjina musu cewa: “Ku babban misali ne na wadanda suka dake a fagen jihadi a tafarkin Allah, kuma ina fatan ku cigaba da wannan dakewar.”

Shaikh Zakzaky da matarsa, su ma sun nuna matukar farin cikinsu, a yayin da suka bayyana cewa farin cikin da suka ji ba ya misaltuwa. “Muna fatan cewa, da addu’o’inku, da kokarinku da kuma karfafawarku ga al’ummar Musulmi, Musulunci zai cigaba da mamaye dukkan sassan duniya Insha Allah.” Inji Sayyid Zakzaky.

Ga wasu daga hotunan ganawar da muka samu daga shafin khamenei.ir

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini

Published

on

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2024, Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa dandalin daliban harkar Musulunci a Nigeriya, a gidansa da ke Abuja.

Kamar yadda Ofishin Jagoran ya Wallafa cewa an yi ganawar ne a ranar Litinin 26 Zuqadah 1445, wanda ya yi daidai da 3/6/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.