Connect with us

Labarai

Maukibin Shaikh Zakzaky A Hanyar Karbala; Me Ya Ƙunsa?

Published

on

A wannan shekarar ta 1445 (2023), kamar sauran shekarun da suka gabata, Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gudanar da Maukibinsa, don hidima ga masu Tattakin Yaumul Arba’een zuwa Haramin Imam Husaini (AS) da ke Karbala, a kasar Iraq.

Maukibi, wata rumfa ce da ake shiryawa don saukan baki a yayin da suke gudanar da tafiyar kafa a lokacin Arba’een din Imam Husaini (AS). Akwai Maukibobi daban-daban da masu hidima ga Imam Husaini (AS) daban-daban daga sassan duniya suke samarwa, su rika ciyar da mutane abinci, da kuma basu wajajen hutu, da yi musu kyaututtuka a yayin da ake Tafiyar Arba’een a Iraqi.

A wannan shekarar ta 1445 Hijiriyya, Ofishin Jagora Shaikh Zakzaky (H) ya shirya Maukibobi guda biyu ne don wannan hidimar ga maziyartan Imam Husaini (AS); na farko shi ne wanda yake a Amudi na 1117 da ke kan hanyar Najaf zuwa Karbala; sai na biyu yana Amudi na 820 da ke kan hanyar Bagdad zuwa Karbala.

Me Aka Gudanar A Maukibobin Jagora (H) A Bana?

Wakilin Ofishin Jagora a daya daga Maukibobin, Shaikh Yahya Aljafari ya shaidawa CIBIYAR WALLAFA cewa, ayyuka kashi biyu Maukibobin suka gudanar a wannan shekarar, su ne; ayyukan hidimtawa masu tattakin, da kuma isar da sakon Harka Islamiyya da manufarta da bayani a kan Jagoranta.

A bangaren Tablig (Isar da sako), ya bayyana cewa, Maukibin ta buga rubutaccen Ziyarar Arba’een a dan karamin takarda mai aminci, dauke da hoton Jagora (H) a jiki, inda aka rika raba dubban kwafinsa ga maziyartan da ke wucewa, da nufin su yi amfani da shi idan sun isa Haramin Imam Husaini (AS), ladan kuma ya je ga Jagoranmu (H) da Shahidai masu girma.

Bayan wannan, Maukibin ya rika la’akari da mutanen da suka zo daga yankunan Turawa, da kuma masu jin yaren Ingilishi, inda ya rika raba musu kyautar rubutaccen littafin Taqaitaccen Tarihin Harkar Musulunci, wanda Malama Zeenah Ibrahim ta wallafa a cikin harshen Turanci. Yace, mutane da yawa sun nuna jin dadinsu ga samun wannan littafin na tarihin Harka, musamman wadanda suke da kishin ruwan fahimtar wani abu da ya shafi Shaikh Zakzaky da da’awarsa.

Ya bayyana bangare na uku na Tablig din da Maukibin ya rika yi a wannan karon. Yace, “shi ne yin bayani da baki ga maziyarta a kan halin da Sayyid Zakzaky (H) yake ciki, da halin da Harkar Musulunci take ciki, da kuma halin da Musulunci da sauran al’amura suke tafiya a Nijeriya.”

Yace, da yawan maziyarta daga yankuna, suna jin sunan Shaikh Ibraheem Zakzaky ne kawai, amma ba su san shi ko ayyukansa ba. Wasu ma suna dauka yanzu haka ya yi Shahada, kamar yadda sukan zo su ce, Allah Ya karbi Shahadar Shahid Zakzaky. Sai an yi musu bayani a kan cewa yana nan raye tukunna, kuma ga irin halin da azzaluman mahukuntan kasarsa suka bar shi a ciki, ga kuma irin dakewarsa da kuma tsayuwa a kan manufa da hadafinsa na kawo gyara a cikin al’umma, wanda shi ne irin hadafin Imam Husaini (AS) a lokacin waki’ar Karbala.

An kuma rika saka wakokin juyayin Ashura da aka yi da yaruka uku; Hausa, Larabci, da Farisanci, inda maziyartan suka rika sauraro. Tare da kunna Bidiyon da ya shafi Waki’a da daddare don isar da sako ga al’umma baki daya.

A bangaren Hidimtawa Maziyartan Imam Husaini (AS), Malam Aljafari ya bayyana cewa, Maukibin ofishin na Shaikh Zakzaky (H) ya samar da A.C (abin sanyaya yanayin muhalli), sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi a kasar Iraqi, inda ya ba maziyartan da ke wucewa dama su rika shiga suna kwanciya, ko su zauna su huta a ciki, har ma wasu sukan kwana a wurin. Yace, wannan ya sa sun rika yi wa Jagora (H) addu’a ta musamman da rokon sakayyar Allah Ta’ala a gare shi.

Maukibin ya kuma rika tanadan ruwan sanyi, da ‘Juice’ (lemun ruwa), da irin su Alkaki (cake), wanda a kowace rana ana rabawa maziyartan da ke wucewa a lokuta biyu daban-daban a kalla. Yace, wannan ma ya rika faranta ran maziyartan, saboda yadda suke samun ruwan da sanyin kankara mai dadi, alhali ana fuskantar tsananin zafin rana.

Maukibobin Sun Rika Samun Maziyarta Daban-Daban Daga Sassan Duniya

Da yake a wannan shekaran an samar da Maukibi guda biyu ne, akwai na hanyar Bagdad zuwa Karbala, wanda shi ne hanyar da mafi yawan Larabawa da mutanen Iraqi suke bi, sai kuma hanyar Najaf zuwa Karbala, wanda ya tattaro maziyartan da suka fito daga kasar Iran da wasu daga cikin mutanen Iraq, da kuma sauran mutane daga dukkan kasashen duniya. Don haka Maukibobin guda biyu sun rika samun baki, da sukan ziyarce su, su karbi hidimarsu, ko kuma su yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky addu’a kafin su wuce.

A yayin da wasu suka rika tsayawa suna tambaya a kan Shaikh Zakzaky, da manufar Da’awarsa, da kuma irin halin da ya rika ratsowa na jarabawowi a tsawon shekarun da ya shafe yana kira.

Daga muhimman bayin Allah da suka ziyarci Maukibin Jagora (H) da ke Amudi na 1117 a hanyar Najaf zuwa Karbala akwai Ayatullahi Ramazani (H), wanda shi ne shugaban Mazma’u Ahlulbait (AS), wanda ya tsaya ya tambayi bayani dangane da Shaikh Zakzaky (H) ya yi masa addu’a da isar da sakon gaisuwa gare shi. Da kuma sauran bayin Allah daban-daban maza da mata daga kasashe daban-daban.

Haka ma a Maukibin da ke Amudi na 820 a hanyar Bagdad zuwa Karbala, ya rika samun maziyarta daban-daban, musamman kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya daga kasashen daban-daban na duniya, ciki har da matasan Kungiyar Muqawamatul Islamiyya da ke Bagdad, da kuma takwarorinsu na yankin Azerbaijan, wadanda har karrama Maukibin Shaikh Zakzaky (H) din suka yi, tare da gabatar da kyauta gare su.

Maukibin Sayyid Zakzaky (H) ya zama wa mutanen Duniya wani amintaccen kafa na sanin mene ne sahihin halin da Jagora da Harkar Musulunci suke ciki a wannan lokacin.

A bana, “Ataba Abbasiyya”, wadda ke kula da lissafin adadin maziyartan da suka shigo Iraqi ta sananniyar hanya don ziyarar ranar Arba’een, ta bayyana cewa sun haura kimanin mutum Miliyan 22.

Ga wasu daga hotunan ayyukan Maukib din na Jagora (H) na hanyar Najaf zuwa Karbala:

Ga wasu daga hotunan ayyukan Maukib din Jagora (H) na hanyar Bagdad zuwa Karbala:

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Ɗalibai A Ranar Tunawa Da Imam Khomeini

Published

on

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2024, Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa dandalin daliban harkar Musulunci a Nigeriya, a gidansa da ke Abuja.

Kamar yadda Ofishin Jagoran ya Wallafa cewa an yi ganawar ne a ranar Litinin 26 Zuqadah 1445, wanda ya yi daidai da 3/6/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Labarai

An Yi Biki Sauƙar Al’ƙur’ani Karo Na 13 A Kano

Published

on

Harkar Musulunci a Nigeria ƙarƙashin Jogarancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta yi gaggarumin taron bikin saukar Al’ƙur’ani mai girma karo na 13.

Taron an yi shi ne a ranar 17 ga watan Mayu wanda yayi dai-dai da 10 ga watan Zul-Qada a cikin garin Kano, wanda ya samu a dadlin mahaddata 348 daga wasu ba’adin fudiyoyin harka da ke faɗin Nigeria da suka sauƙe ƙur’ani.

An gudanar da taron ne a ƙofar gidan Sarkin Kano, tare da halartar manya manyan baki daga garuruwa da dama.

Ga wasu hotuna na taron….

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.