Litattafai: Shaikh Zakzaky (H)
Littafin Watan RAMADAN Da Ayyukansa Na Shaikh Zakzaky

Wannan dan littafin na kunshe ne da fassarar hudubar Manzan Allah (S), wanda ya yi ga Sahabbansa gab da qaratowar watan Ramadan mai alfarma a lokacin rayuwarsa. Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya karanto hudubar ga almajiransa ya kuma fassara ta a yayin da yake gabatar da Tafsirin Alqur’ani mai girma a ranakun wata Alhamis da Juma’a, 28-29 ga watan Sha’aban- 1435, (26-27/6-2014).
Sauke Littafin A Nan: RAMADAN DA AYYUKANSA – Shaikh Zakzaky (H)

Litattafai: Shaikh Zakzaky (H)
TASIRIN DABI’U- Na Shaikh Ibraheem Zakzaky

GABATARWA:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai. Tsira da Aminci su qara Tabbata ga Fiyayyen HalittunSa, Annabin Rahama Muhammad (S) da Iyalan Gidansa Tsarkaka, da Sahabbansa Managarta. Mai karatu, a wannan karon muna xauke ne da jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen rufe taron qara wa juna sani na yini uku (Mu’utamar), wanda ya gabata a garin Talatan Mafara ta jihar Zamfara a shekarar 2008. Mun xauko jawabin ne daga shafin Intanet (Hausa) na Harkar Musulunci.
Ku sauke Littafin A Nan: TASIRIN DABI’U Na Shaikh Ibraheem Zakzaky
Litattafai: Shaikh Zakzaky (H)
ZALUNCI DA DANNIYA: INA MAFITA? Na Shaikh Ibraheem Zakzaky

GABATARWA:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Tsira da Aminci su kara Tabbata ga Fiyayyen Halittu, Annabin Rahama Muhammad (S) da Iyalan Gidansa Tsarkaka, da Sahabbansa Managarta. Mai karatu, a wannan karon muna dauke ne da dadadden jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a wani taron ‘yan boko, mai take Zalunci da danniya: Ina Mafita? Duk da cewa jawabin ya dade, amma kai ka ce a daidai wannan lokaci ya yi jawabin. Muna fata za a karanta jawabin cikin natsuwa da zurfafa tunani kan bayanan da Jagora (H) ya yi, domin lallai akwai abin la’akari mai girma.
Sauke Littafin A Nan: ZALUNCI DA DANNIYA_ INA MAFITA Na Shaikh Ibraheem Zakzaky
Litattafai: Shaikh Zakzaky (H)
KOYI DA RAYUWAR MANZON ALLAH (S) Na Shaikh Ibraheem Zakzaky

Mai karatu! A wannan karon muna xauke ne da jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar a wani taron ‘Maulidin Annabi (S)’ wato ‘Annual Maulud’ da lajanar “Resource Forum” ta shirya a ‘Arewa House’ da ke birnin Kaduna Nijeriya, a shekarar 1428 hijira, wanda ya yi daidai da shekarar 2008 miladiyya. Mun xauko jawabin ne daga shafin Intanet na Harkar Musulunci.
Ku sauke Littafin A Nan: KOYI DA RAYUWAR MANZO (S) Na Shaikh Ibraheem Zakzaky
-
Labarai3 months ago
Hotuna: An Kammala Tattakin Ranar Arba’een 1445 Lafiya A Abuja
-
Labarai8 months ago
Muzahararorin Quds 2023/1444 A Nijeriya
-
Tarihin Shahidan Harkar Musulunci6 months ago
WAKI’AR BUHARI; Shahid Mahmud Ibrahim Gwarzo
-
Waki'o'i A Harkar Musulunci3 months ago
Waki’ar Abacha (12/9/1996) A Takaice
-
Labarai4 months ago
Hotunan Zaman Ashura 1445 (2023) A Nijeriya
-
Labarai2 months ago
Muhimman Bayanan Sayyid Khamene’i A Yayin Ganawarsa Da Shaikh Zakzaky
-
Tarihin Shahidan Harkar Musulunci8 months ago
Shahidin Quds 1444H; SHAHID YAKUBU A. UMAR (KHALIFA)
-
Labarai4 months ago
Hotunan Muzaharorin Ashura 1445 A Nigeria