Connect with us

Labarai

Jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) A Ranar Quds 2023/1444

Published

on

Bismillahir Rahamanir Raheem.

Wasallallahu Ala Sayyidina Wa Nabiyina wa Habibi Qulubina Abil Qasimi Mustapha Muhammad wa ala alihid Dayyibinad Dahirinal Ma’asumiyn, Siyma Baqiyatullahi fiyl ard, Sahibul Asr waz Zaman arwahuna lahu fidah.

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa barakatuh.

Zan so a wadannan ‘yan mintoci, na yi magana dangane da ranar Quds ta duniya, wacce ake yi a ranar Juma’ar karshe na watan Ramadan. Juma’ar karshe a wannan karon an zabi ya zama 23 ga watan Ramadan ne, domin idan aka ce ranar 30 ga watan Ramadan, tana iya yiwuwa ta zama 1 ga watan Shawwal, tana iya yiwuwa kuma ta zama ita ce Juma’ar karshen idan watan ya kammala kwana 30. Amma akwai yiwuwa rannan ya zama 1 ga watan Shawwal din, don haka ranar 23 za ta zama ranar Quds ta duniya.

Wannan karon kuma Alhamdulillahi kusan dai yadda muke da labari, kusan duk duniyar Musulmi an dauki azumi kusan a lokaci guda ne ranar Alhamis, wanda ya mai da ranar 23 din ta fado a Juma’a.

 

RANAR QUDS DIN BANA YA DACE DA LOKACIN JAJEN AMIRULMUMININ (AS)

To, wannan Quds Day din ta zo mana a daidai lokacin jaje, ko da yake Quds Day ma duk jaje ne, amma dai wannan karon kususan ya zo mana a daidai lokacin jajen shahadar Amirulmuminin (AS), wanda aka sare shi da takobi a masallaci ranar 19 ga watan Ramadan a daidai lokacin sallar Alfijir, kuma ruhinsa tsarkakka ta bar gangar jikinsa izuwa rahamar Allah a ranar 21 ga watan Ramadan, a yammacin wannan yini.

Mu kan yi jaje a wadannan kwanuka, tun daga 19 har 21 ga watan, kai har ma karshen watan duk mu a wajenmu lokacin jaje ne. To, ya zama wannan karon Quds Day dinmu ya zo da jajen Shahadar Amirulmuminin (AS). Sai na kara cewa: “A’azamallahu ujurana bi musabina bi Amirulmuminin (AS).” Ina taya dukkaninmu jaje kan wannan al’amari.

To, Qud Day kamar yadda nace shima kansa ranar jaje ne, domin bara nake cewa da yake Juma’ar karshe din ta fado ranar 28 ga Ramadan ne, ya yi mana daidai da ranar da abin da ya faru, a wancan lokacin shekara 8, yau shekara 9 da suka wuce kenan, wanda ya zama muma rannan Quds din mu sai ya zama da jaje, saboda haka sai ya zama duk lokacin ranar Quds mu kan tuna da shahadar shahidanmu.

 

RANAR QUDS RANA CE TA ‘TADAMUN’ DA PALASDINAWA

To, Quds Day, ko nace Ranar Quds, ko “Yaumul Quds al-Alamiy”, ranar ce da aka sanya domin yin ‘Tadamun’ idan wannan Kalmar an fahimceta, Tadamuni da al’ummar Palasdinu, da Ingilishi ana cewa ‘solidarity’, wato muna tare. Za mu ce masa Tadamuni din, tunda Bahaushe ya kan dauki kalmomin Arabiyya ya yi amfani da su. Tadamuni da al’ummar Palasdinu, wanda suke fama da kuntatawa shekara kusan 80 a madadin dukkan al’ummar Musulmi.

Domin inda suke zaune, waje ne mai tsarki, wanda Allah Ta’ala ya ajiye Masjidul Aqsa, wanda Allah Ta’ala ya ba da labarinsa da cewa, ya yi tafiyar dare da bawansa daga Masjidul Haram zuwa Masjidul Aqsa, wanda ya yi albarka a geffensa, domin ya nunawa bayansa Ayoyinsa. Ta nan ne Allah Ta’ala ya dauki Manzonsa (S) daga Masjidul Haram zuwa Masjidul Aqsa, daga nan kuma yi mi’iraji zuwa saman bakwai.

 

MASJIDUL AQSA NE ALQIBLAR MUSULMI NA FARKO

Kuma nan ne alkiblar farko na al’ummar Musulmi. Domin lokacin da Manzon nan (S) yake yake Makkah yana duban Baitul Muqaddas ne, don haka yakan hada Masjidul Haram da Baitul Muqaddas a lokaci guda, don yakan tsaya a kusurwar da ke tsakanin Hajarul Aswad da Hijr-Isma’il, wannan kusurwan da ke da kofar Ka’aba. Don idan mutum ya tsaya a nan ya budi Ka’aba, to a lokaci guda kuma yana duban Masjidul Aqsa ne. To, sai ya kasance yana haka nan.

Lokacin da ya koma Madina, sai ya zama wannan ba zai yiwu ba, tunda Madina din tana Arewa da Makkah ne, ita kuma Masjidul Aqsa din tana Arewa ne kuma da Madina, saboda haka ba zai yiwu Manzon Allah (S) ya dube su a lokaci guda ba, sai ya cigaba da duban Arewa a yayin salla, har izuwa lokacin da Aya ta sauka tace a dubi Masjidul Haram, sai ya juya ya fuskanci Ka’aba. Wannan sanannen abu ne ga dukkan Musulmi sun san da wannan, har ma ana ce ma Aqsa dayan qibloli guda biyu a wajen Musulmi.

Wannan kuma waje ne da Allah Ta’ala ya albarkata, kamar yadda yace “Allazi barakna haulahu linuriyahu min ayatina.” Waje ne da Allah ya albarkaci wannan muhallin. Kuma kowane Annabi yana da sila da wannan muhalli. Nan ne mahijirtan Annabi Ibraheem (AS).

Su al’ummar Musulmi da yake addininsu addini ne, ba wai na yankin wata kasa, ko wadansu al’ummu ko wata qabila ba, addini ne na Allah Ta’ala izuwa ga bil’adama baki daya, saboda haka suna ganin wannan muhalli ne da tsarkin da Allah Ta’ala ya yi masa. Na’am, bai kai Masjidul Haram ba, don Masjidul Haram dama tun farko shine farkon dakin ibada wanda Allah Ta’ala ya ajiye. “Inna awwala baitin wudi’a linnasi lallazi bi bakkata”, wannan shine asali.

Kuma ko su ma Isra’ilawa a littafansu in sun duba sun san da Masjidul Haram, kuma sun san shi ya kamata suma su duba, kuma sun san da matsayinsa. To amma don nuna cewa addinin nan (Musulunci) cigaban addinin Annabi Ibraheem (AS) ne, kuma cigaban addinin Musa da Isa (AS) ne, saboda haka sai Manzon nan aka nuna masa ya fara duban Masjidul Aqsa, sannan daga baya kuma aka juya zuwa Masjidul Haram, wanda yake nufin daga yau, yanzu duk al’umma an ce su juya su kalli Masjidul Haram. Saboda haka matsayin Masjidul Aqsa yana nan a zukatan Musulmi a matsayin wuri mai tsarki wanda suke girmamawa a matsayinsa na daya daga cikin Alkiblolinsu guda biyu.

 

HALIN DA MUHALLIN QUDS YAKE CIKI

To, wannan muhalli shine wasu suka je suka kama, suka ce kasar su ce ta gado wai wadda Allah ya basu. Ba su tsaya nan ba, suka kuma ce duk wanda yake wajen ma a yadda suka rubuta wai Ubangijin nasu yace suna iya kashe wadanda suke wannan muhallin domin wajen nasu ne. Saboda haka yau an kwashe kusan shekara 80 kullum suna ta’asa, kullum suna miyagun ta’asa a kan al’umma, na kashe-kashe da baje garuruwa da kauyuka, da yadda suka tambatsa al’ummar Palasdinu a sassan duniya daban-daban, kuma har yanzu ba a kyale su ba kullu yaumin.

Tun ma kafin su kafa haramtacciyar kasar da suka kira isra’ila suke yin barna a cikin Palasdinu din, har izuwa lokacin da suka ayyana cewa yanzu sun kafa wata kasa haramtacciya a cikin Palasdinu. Duniya ta yarda akwai wani dan bangare sunansa Palasdinu ma, amma duk da haka yau da kullum su wadannan mutane basu san da zaman wani Palasdinu ba, barna suke yi.

To kuma birnin Quds wanda yake birni mai tsarki, an dade ya zama maziyartar al’ummar Musulmi, idan mutum ya je Hajji, ya je kuma ziyarar Annabi (S) a Madina, sai kuma ya wuce Masjidul Aqsa a birnin Qudus ya yi ziyara, sannan ya dawo gida. An dade ana yin haka, har izuwa lokacin da suka rufe kofa suka hana, ya zama yanzu mutane basu san ma ana ziyarce-ziyarce zuwa nan ba, in an je Hajji sai dai a je Madina kawai an gama, a da kuwa har da birnin Quds Alhazai sai sun je. Ba lallai duka ba, wanda duk ya samu iko sai ka ga ya je har da birnin Quds, amma yanzu mutanen nan sun hana.

 

ISRA’ILAWA NA TSANANTA HARE-HARE KAN PALASDINAWA

Wannan, inda mutum yana bibiyan abin da ke faruwa, zai ga cewa tun kamawar watan Rajab, ko ma nace tun karshen Jimadas Thaniya, wanda ya yi daidai da farkon shekarar miladiyya din nan, kullu yaumin mutanen nan kisa suke yi, kullu yaumin suna kashe Palasdinawa ne, su je su kai musu hare-hare, sojoji ne dauke da bindigogi da kwalkwali, da rigunan da ke kare kai daga harsashi, da manyan-manyan takalma, da miyagun shiga, idan ka gansu kamar dodonni, su suke shiga su kutsa unguwa-unguwa. Kullu-yaumin wai suna neman wai ‘yan ta’adda.

Duk duk wani saurayi ana iya kama shi, harbi suke yi, kuma harbin nan da suke yi a ka suke yi. Mafi yawan wadanda suka kashe a ka ne, kuma mafi yawansu matasa ne ‘yan shekara goma sha zuwa shekara ashirin da wani abu ko ‘yan shekara talatin da wani abu, mafi yawa ‘yan kasa da goma ne da kuma ‘yan kasa da talatin, mafi yawansu kuma suna harbinsu ne a ka. Kullu-yaumin sai sun kashe mutum, basu ma damu da abin da suke aikatawa ba.

 

KAFAFEN WATSA LABARUN TURAI SUNA RUFE ABIN DA KE FARUWA                                       

Kuma abin mamaki, in dai ba kana bibiyan kafafen watsa labarum Musulmi da na Larabawa bane, ba ma za ka ji wannan yana faruwa ba. Domin su sauran kafafen watsa labaru na Yammacin duniya sun yi shiru ne da maganar tamkar ba wani abin da ke faruwa. Sam basu ce komai dangane da abin da ke faruwa ba. Shiru suka yi.

Tun bayan da wannan gwamnatin da suka kafa wadda suke cewa mai tsattsauran ra’ayi, suka yi hadin guiwa da wadansu mutane wanda ra’ayinsu shine a kashe duk wani Bafalasdine, ba ma a nan Palasdinu kawai ba, a kashe duk wani Balarabe. Kuma an san ra’ayinsu kenan, amma an yi hadakan gwamnati da su.

Duk da mun san akwai Isra’iliyawan da su basu goyi bayan abubuwan da ake ba, har suna ma fitowa suna Muzaharori na rashin goyon bayan wannan gwamnatin, amma dai matsalarsu ta cikin gida ce, suma kansu suna ganin abin da wadannan gwamnatin suke yi ba daidai bane. Amma mu abin da ya fi damunmu ko ma wane ne ma yake gwamnati a cikinsu, bamu tunanin kawai zai mana adalci.

Dubi irin ta’asan da wannan suke yi ya wuce kowanne, ba a taba yin irinsa ba. Kwanaki suka jera, kullum su je unguwanni, akwai lokacin da suka kashe mutum 11 kuma galibansu yara, akwai lokacin da sukan kashe fiye da haka, akwai lokacin da suke kashe kasa da haka nan, kullum.

Amma abin mamaki, ni da yake na kan bibiyi kafafen yada labaru na Yammacin duniya, na kan dan dauki lokaci duk da dai ba dadi amma na kan so na ji ra’ayoyinsu, rannan ina budewa sai na ji wani kafan watsa labaru na Turai sun ce kawai yau gashi wani Bapalasdine ya kai hari ya kashe isra’iliyawa guda bakwai. Shine farkon labari. Kai kace wannan shine farkon ma abin da aka fara yi. Kai kace tuntuni ma ba a taba kashe wani Bapalasdine be, ko wannan ba ramuwar gayya bane. Kai kace Palasdinawa ne ma suke kuntatawa isra’iliyawa. Haka suka nuna.

To sannan kuma, bayan nan wani matashi ya buge wasu isra’iliyawa guda biyu da mota. Ba su yi wata-wata ba suka je suka kashe shi, kuma suka je gidansu suka baje gidan, suka kashe mutanen da suka samu a unguwar, wai a kan cewa shi ya kashe isra’iliyawa guda biyu. Ba su bincika ba hatsari ne ko me ya faru? Don mutum yana tuka mota, yana iya zama hadari ne, a kama shi mana a kai shi mahukunta, a kuma ji dalili ko da gangan ya yi, ko kuma mota ta kwace masa ne? Ina!

Alhali kafin wannan, akwai wani dan zaman kaka-gida, Ba’isra’ile, wanda ya bi ta kan wasu mutane biyu da suka dawo daga bikin ‘yar ‘uwarsu, sun tsaya suna kwance taya za su canza tayar motarsu, ya zo ya bi ta kansu. Kusa da su kuma akwai wajen bincike na sojojin haramtacciyar kasar isra’ila suna wajen, suka ganshi. Wadannan sun yi ‘parking’ ne a gefen hanya, amma ya karkata ya bi su ya taka su ya wuce, ya je kuma wannan digon binciken sojojin isra’ila din ya wuce basu ce masa komai ba. Suna kallo. Kuma ya kashe su dai, shikenan, mutum biyu ne, wa da kani. Kuma basu ce komai ba, ba ma labaru bane a wajensu.

Amma wannan da mota kwace masa ta yi, ko da gangan ya yi? Ba su ma bincika ba kawai sun kashe shi, sun kuma je gidansu sun baje gidan. Haka nan abin yake, Yammacin duniya basu cewa komai game da abin da ke faruwa.

 

TA’ADDANCIN BANA YA TSANANTA AKAN NA BARA

To sai wani abin mamakin da ba a taba ganin yana faruwa ba ma, sai ya faru a wannan shekarar. Shine wadda yake tun kamawar Ramadan din nan, an san a ko ina a duniya Ramadan lokaci ne na ibada ga Musulmi, su kan yi azumi da rana, da yamma lokacin bude-bakinsu yakan zama kamar lokacin biki, a wurare da dama a kan je a yi abinci a yi ‘ifdar’, kuma har ma sauran duniyar da ba na Musulmi ba har su kan yi ‘Mujamala’ su gaishe da Musulmi a lokacin Ramadan.

Alal misali ko Obama da Trump, da shugaban Canada, da na ina ne, duk sai da suka yi abin da suke ce ma Ramadan Kareem. Suna taya al’ummar Musulmi murnan wannan wata mai alfarma, watan da mutane su kan sadaukar su nuna damuwarsu da sauran al’ummu da halin da kowa ke ciki, da sauransu. Wannan sanannen abu ne, ko da mutum ba Musulmi bane, ya san Ramadan. Ya san Ramadan kuma lokaci ne da al’ummar Musulmi sukan hadi a wuraren ibada, su yi salloli.

To amma wannan karon, sai ya zama tun farkon fara Ramadan din nan, kullum wadannan la’anannun mutane za su je da sojoji cikin wannan Masallaci (na Aqsa) su tarwatsa masallata. Ana cikin salla sai su tarwatsa mutane. An saba bayan an yi Magriba da Isha a kan yi nafilolin Ramadan, to ana nafilolin nan za su shigo su tarwatsa mutane har da harbi da bindiga, su farfasa gilasoshin masallacin. Za su shiga kuma da takalmansu ne da duk tarkace da kwalkwalinsu, har da ma gilashin da ke rufe fuska. Su kuma wadannan masallata ne, sallah kawai suke yi.

Kuma za ku ga in mutum ya damu da ya duba hoto, zai ga inda za a zo a samu kan sahu a birkita sahun. Kuma banda wannan a rika dukan har da mata, ka ji mata suna ihu ana dukansu, kuma a kakkama mutane a daddaure. Bara sun yi wani abu mai kama da haka nan, amma na bana sai ya fi muni. Sai a kama mutane, akwai rana daya da suka kama mutane sama da 400, duk suka kama su suka kifa cikinsu suka saka igiya ta baya, wai sun kama su. Kuma sallah suka je yi.

Wannan irin al’amarin za ka ga cewa ko da ma mene ne addinin mutum, mu an ce mana mu girmama addinin mutane. Inda yahudu ne yake yin abin da muke yin nan, ko ma mene ne idan yace ibadarsa ne, namu kallo ne, ba yadda za a yi mu ce masa ya daina ibadarsa.

Wadannan mutanen kuma basu kyale wasu masu ibada ba banda su, har ma a ranar Larabar nan sun hana Masihiyawa, wanda suke bin kiristanci, sun je cocinsu sun hana su yin wani biki da suka saba yi.

To wannan irin abin al’ajabi da ban-mamaki. Duniya tana kallo, kuma baka jin komai, sai abin takaici, kafafen yada labarun Yamma wai sai su ce wai na yi hatsaniya, ko abin da suke kiranshi da Ingilishi wai ‘clash’, kamar an yi artabu ne tsakanin gungu biyu; Palasdiniyawa da isra’iliyawa. Kai kace dan rigima ce tsakanin wadansu mutane.

Alhali wadannan hotuna na nunawa a sarari cewa sojoji ne dauke da bindigogi, da kwalkwali, da murfin ido – gilashin da ke rufe fuska, da jigidan harsashi, da kuma kayan da ke kare su daga harsashi, da manyan takalma, suke shiga da bindigoginsu su tarwatsa mutane, su dauki kulake kuma su rika dukan mutane har da mata. Wai amma wai sai a kira shi wai ‘clash’. Wato kamar rigima ake yi tsakanin bangarori biyu. Ya za a yi mutumin da ya tafi sallah ko sanda bai dauka ba, wa zai je masallaci da sanda? Ya je ya yi sallah ne kawai, a je a dirar masa, wai sai a ce ana rigima ne.

Sannan kuma idan su Palasdinawa suka mai da martani ta wata hanya, to sunansu ‘yan ta’adda. Abin da kafafen yada labarun Yamma ke nunawa kenan, sunan Palasdinawa ‘yan ta’adda. Yanzu su idan isra’ila suka yi harbi, su sun yi ramuwar gayya ne a kan ‘yan ta’adda. Idan suka kashe Palasdinawa wai suna kashe ‘yan ta’adda ne. Ko da mene ne ‘yan Palasdinu suka yi, ko da sun fito ne suna nuna basu yard aba, duk sunansu ‘yan ta’adda ne, kuma haka dai wadannan suke nunawa.

 

DUNIYAR TA YI BIRIS DA ZALUNCIN DA AKE MA PALASDINAWA

To wannan kin gaskiya da yawa yake. Yadda za ka ga duniyar nan baro-baro sun yi biris da wannan al’amarin na Palasdinu, suna ji suna gani. Dubi irin hayaniya da kwarmato da suka rika yi a kan al’amarin Ukrain, cewa gashi nan Rasha ta mamaye Ukrain, gashi nan tana kaza, gashi nan tana kaza. Suna ta iface-iface a kan Ukrain.

Bamu ce ana iya yin shiru dangane da Ukrain ko mutanen Ukrain ba, amma me? In dai har ka damu da Ukrainawa, ana zaluntarsu a ganinka, to me zai sa kuma a zalunci wani shi kuma sai ka yi shiru? Idan da gaske ne kai baka son zalunci. Amma biris suke yi da al’amarin Palasdinu.

 

AL’AMARIN PALASDINU YA SHAFE MU ‘KUSUSAN’ MUSULMI

To, wannan lokaci mu muna fitowa ne mu nuna cewa al’amarin Palasdinu fa namu ne duka, kususan mu Musulmi, ya shafe mu duk cikarmu. Kuma a bara an nuna fushi a lokacin watan Ramadan a ko ina a duniya, dangane da abin da aka rika ma Palasdinawa a Palasdinu, musamman a Masjidul Aqsa. Bana ma da ake yi shima haka nan, irin yadda aka yi ta nunawa za ka ga a birnin London an yi gagarumin taro dangane da abin da ake yi a watan Ramadana a Masjidul Aqsa, da kuma sassa na duniya daban-daban.

Mu a nan inda muke zaune, inda ake ce ma Nijeriya, an jarabce mu da wadansu masifofi da fitinoni masu ban-al’ajabi. Yanzu duk wannan abin da ke faruwa da ta’asar da ke faruwa din nan, za ka ga mutane ba abin da suke cewa dangane da shi. Maimakon haka nan, sai wani ya kunno da wata mugunyar magana game da ko aqidarsa, ko wani irin tunaninsa, ko ya jefa wani wuta, ko ya kafirta wani, ko ya yi wata baqar magana mummuna game da wani Shaksiyya na addini da ake girmamawa. Sai a yi caaa a kanshi, wannan yace kaza, wancan yace kaza, wannan yace kaza. Idan ya lafa, sai wani ya sake babaro wata maganar. Sai kuma a sake komawa ana raddi. Can sai wani ya sake fito da wani abin.

Don Allah, yanzu Shaidan ya baku aiki irin wannan? Yanzu baku da wani aiki sai kullum kuna cecekuce a tsakaninku, akan wannan yace kaza, sai a ce masa kaza, wannan yace kaza? Yanzu shaidan idan ya gano ku da wannan al’amarin ai shikenan ya samu hanyar da zai kautar da hankalinku daga abin da ya kamata ya dame ku.

Ana kashe ‘yan uwanku a wani waje, masallaci mai tsarki naku gashi ana zuwa a dirarwa masallata, kuna kallo, amma wannan bai dame ku ba? Kuna nan kuna cecekuce game da wadansu ra’ayoyi. Wannan sai ya fito da wannan, wani ma ya riga ya rasu, sai a ce wai wane kafin ya rasu yace kaza. Sai kuma ai ta surutu, wasu suce wane da yace kaza bai kamata ba, wasu suce kaza. Haka nan aikin kenan, kullum kuma sai an kunno mana da wani abu, sai ya zama shine ake ‘trending’ kowa kamar dole sai ya yi magana a kai.

An dauke hankulanku daga abin da ya kamata ya dame ku. Ku tuna fadin Manzon Rahma (S); wanda bai damu da al’amarin Musulmi ba, bashi daga cikinsu. “Man lam yahtamma bi amrul Muslimina falaisa minhum.” Kuma ya misalta al’ummar Musulmi kamar jiki guda, wanda idan wani bangare ya koka duk sauran na amsawa. Ko yatsa ne ya yi ciwo, to duk sauran jiki zai amsa, da zazzabi da rashin bacci. Ba yadda za a yi a taba yatsa, sauran jiki yace ba ruwansa, ko a taba hakori ido yace ba ruwansa, ko a taba ido hannu yace ba ruwansa, duk jiki ne ke amsawa.

To idan ka ga wani bangare na al’umma an taba, ya kamata duk al’ummar ne aka taba. Musamman wannan tabawan da izgili ake yi da Addininmu da Alkur’aninmu, a je ana sallah a masallaci a birkita.

 

AL’AMARIN PALASDINU BA NA MAZHABA BANE BARE YA ZAMA SHI’A

Sannan kuma wani abin mamaki da wadansu wawaye a nan, sai suna jingina abin da wata Mazhaba, wai Shi’a ne. To, in dai kana da hankali, ka duba al’ummar Palasdinu ka gani, dubi yadda suke yin sallah, ka dubi Malamansu da sauransu, ba wani abu mai kama da Shi’a a wajen. Ana maganar al’ummar Musulmi, ku kuna cewa Shi’a?

Wannan abu da ban-al’ajabi. Har ma kamar yadda nake cewa bara, na ji wata kafar yada labaru da suke cewa wai ranar Juma’ar karshen Ramadan wai rana ce da ‘yan Mazhabar Shi’a suke nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasdinu. Wannan abu da ban-takaici. Goyon bayan Palasdinu din al’amari ne na Mazhaba? Al’amari ne na mutuntaka, in kai mutun ne, ya shafi mutum.

 

HATTA WASU YAHUDAWA BA SU GOYON BAYAN MAMAYAR PALASDINU

Na farko dai, ya fi shafan Musulmi, tunda ana izgili da addininsu da wurare masu tsarki. Sannan kuma ya shafi Masihiyawa, wadanda muke ce ma Kirista a nan, tunda suma ana izgili da addininsu da wurarensu masu tsarki. Sannan ma kuma wannan al’amari ya shafi hatta su Yahudawa, tunda ba duka Yahudu ne yake goyon bayan abin da ake yi ba.

Don akwai Yahudawan da suke ganin cewa, su ana amfani da addininsu ne don nuna abin da basu yarda ba. Bara ina ba da wannan bayani, nace akwai wata kungiyar Yahudawa, wadda suke kiranta da yarensu Neturei Karta, wanda yake nufin “Ba da suna na ba.” Wato ma’ana, ni ba da sunana ake wannan ba. To su har ma duk ranar Quds su kan saka irin wannan alamar Palasdinu, ka ga suma suna Muzaharori, har na fadi ‘site’ dinsu, amma na yi kuskuren fada, yadda suke sakawa shine nkusa. org. Idan mutum ya buga zai ga ranar Quds dinsu na shekaru daban-daban.

Zai ga ba ma kawai sunansu Isra’iliyawa bane, har da limamansu, irin wadanda ake ce ma Rabbi din nan, wanda suke su Limamansu ne, wadanda suke ganin a Yahudanci abin da ake ce musu shine idan Mahdi ya bayyana, (ko me ma suke ce masa da harshensu), to zai daukaka wannan al’umma, zai kuma hada kanta, ya dawo da mulki. Haka nan suka ce an rubuta musu. Kuma Mahdin nan bai bayyana ba. Ni na kira shi Mahdi ne, ta yiwu suna kiransa da wani suna daban.

To kuma suka ce, wannan abin da ake yi ba sunansa addinin Yahudu bane, sunansa Sahayonanci, Sahayonanci kuma ‘ideology’ ne na kwacen kasa da mamayar kasa da kashe mutane, ba shi da dangantaka da addinin Yahudu.

 

MUN HADU DA KOWA A FAGEN FADA DA ZALUNCI

Don haka ne ma a wasu wurare za ku ga har mukan yi taro tare da su. Na san akwai wani hotona da aka nuna tare da wasu ba’adinsu. Mu muka saka hoton, ba wai an je an gano ne a wani waje ba. Da ‘camera’ dina aka dauki hoton, ni kuma na kawo aka saka a ‘site’ aka gani, wasu suka fara cewa gashi nan ma tare ma da Yahudawa. Nace na’am, ba ma Yahudawa ne aka gammu tare da su ba, Malaman Yahudu ne, limamansu ne ma, amma su basu yarda da zalunci ne ba, abin da ya hada mu kenan.

Zaluncin da ake ma Palasdinawa, a kan haka nan da Kiristan da bai yarda da zalunci ba, da Bayahuden da bai yarda da zalunci ba, da Musulmin da bai yarda da zalunci ba, da ma wanda yake ko ma wane irin addini ne in bai yarda da zalunci ba, mun hadu a kan rashin yarda da zalunci. Wannan shine ma’ana. Ba wai yana nufin wai addininmu daya bane, kowa da addininsa, amma wani abu ya hana mu a kan cewa mu mutane ne, kuma bamu yarda da zalunci ba. Wannan shine. To kuma wannan mutuntaka ne, amma gaskiyar magana ya fi shafanmu mu Musulmi.

 

ABIN TAKAICI GA MUSULMIN KASAR NAN DA KUMA MAHUKUNTA

Abin takaici ne ace Musulmin kasar nan, su ba ruwansu da abin da ke faruwa da al’ummar Musulmi a sassan duniya, suna nan an basu rigimar da suke yi a tsakaninsu. Ana ta kawo musu rigingimu, sam baa bin da ya dame su sai rarraba kawukansu, da maganganu da yake daddatsa mutane, da suka gaba tsakanin al’ummar Musulmi, da kuma shuka gaba tsakanin al’ummar Musulmi da wasu al’ummu da ba Musulmi ba, kawai abin da ake ta faman yi kenan.

To kuma mahukuntan kasar nan su kuma amsuwar da suke bayarwa gare mu shine harbi. Ko mene muke yi harbi ne ake yi da bindiga. Kuma yadda Yammacin duniya take yin biris game da abin da ke faruwa idan ana zaluntar Musulmi, haka ma ake mana a nan. Sai ka ga an yi biris da abin, ba ka ji wani yace wani abu ba, sam bai dame su ba.

Duk lokacin da muka yi Quds, Quds ne fa kawai ana nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu, amma sai a zo a bude wuta. Ka yi mamaki, to mene ne na bude wuta? Mun yi taro ne mun ce muna goyon bayan Palasdinu. Mene ne na zuwan jami’an tsaro da bindigogi su harbi mutane? Wani lokaci ma su kan jira sai an gama, wadanda ba su (riga sun) tafi ba su harba. Kuma su harbi yara kanana, kananan yara har wadanda basu kai shekara goma ba sai a harbe su, kuma harbin a ka. Kuma shikenan. Su kuma wasu wayaye suce ai ma addini ne. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Wannan musiba har ina?

 

MUNA KARA FADA CEWA MUNA TARE DA AL’UMMAR PALASDINU DARI BISA DARI

To mun sha fada, muna kara fada, a’ummar Palasdinu muna tare da su 100/100, bamu yarda da zaluncin da ake musu ba, kuma bamu yarda da mamayar da aka musu ba, kuma wannan mamaya da kakaba mana wannan al’umma da suka yi suka ce mata isra’ila, to kamar ta gushe, kuma ana nan rana tana nan zuwa za ta gushen ne.

Kuma fafutukan da al’ummar Palasdinu da sauran al’umma suke yi, na nuna basu yarda da wannan zalunci ba, da dakewar da suke yi daram duk da da tsara, ana shekar da jinanensu, amma basu ja da baya ba, wannan dakewar insha Allahu zai haifar da natija.

Insha Allahul Azeem ba da jimawa ba wannan abin da suka kakaba, ya zama kamar sankara a cikin al’ummar Musulmi, insha Allahu watan-watarana zai gushe.

 

KULE GA MAGOYA BAYAN ISRA’ILA A WANNAN KASAR!

Kuma su wadannan magoya bayan nasu a nan, mun yi musu wani kaka-kara-kaka, muka ce ga wani kule! Idan muka fito muna goyon bayan ‘yan Palasdinu, bamu yarda da zaluncin da ake musu ba, to ba bindiga za ku zo ku yi harbi ba. Abin da ya kamata, tunda kuna goyon bayan isra’iliyawa, sai ku ajiye wata ranar, ba ranar Juma’ar karshen Ramadan ba, sai ku ce wannan kuma ranar Tadamuni ne da al’ummar isra’ila, kun goyi bayan isra’ila da ta’asar da suke yi, ku a wajenku daidai ne.

Duk da su fa basu dauke ku matsayin bil-adama ba. Basu ma dauka ku mutane bane, a luggarsu ku dabbobi ne ma! Amma dai tunda kuna goyon bayansu, shikenan sai ku ajiye wata rana, kuce duk mai goyon bayan isra’ila shima sai ya zo ya yi Muzahara, yace ya goyi bayan isra’ila, idan ya so ma duk abin da ya so ya yi na nuna goyon baya, amma ba zai kai hari a kan wani mutum ba, ba zai zagi kowa ba, yana goyon bayan isra’ila ne, illa iyaka. Kun ga shikenan.

Kuma ba za mu ce musu kar ku yi ba, tunda suna da hakkin su yi. Muma muna da hakkin muce mun goyi bayan Palasdinu. Mu ma muna da wannan hakkin. Saboda haka mene ne na cewa kuma ranar Quds sai a yi harbi?

 

KO KUN YI HARBI KO BAKU YI BA ZA MU YI MUZAHARAR QUDS!

A shekaru tara da suka wuce, bayan ma an kammala Muzahara, sun yi harbi a Zariya, inda suka kashe mutum 34. Kafin nan ma da kamar shekaru 23 da suka wuce, sun yi harbi a Kano, shima bayan an kammala a ‘yan mota, suka yi harbi suka kashe mutum takwas. Haka nan dai suke al’amarin.

To, ko bara, duk ko ina sai da aka ga an yi Quds a ko ina, ba inda aka yi harbi. Hatta a birnin Quds kanta a bara ba a harbi kowa ba ranar Quds, an yi ranar Quds a Juma’ar karshe ne Ramadan bara ba a ji harbi a ko ina ba, amma abin mamaki sai a ka ji harbi a Kaduna da Zariya. A Kaduna rannan aka kashe wani dan uwa mai suna Mustapha Wagini. Kuma a Zariya an ji ma wata ‘yar uwa ciwo, mai suna Fatima Usman, wadda bayan jinyar wajen kwana 52 ita ma ruhinta ya bar gangan jiki ta cika.

To har ma a lokacin mutane suka ce, an shafa duk duniya ba a ji inda aka kashe mutum a ranar Quds ba, sai shi wannan Mustapha Wagini din. Har sun saka hotonsa a wasu wurare da dama (masu daraja), saboda shi kadai aka kashe.

To, abubuwan nasu yana daure mana kai. Kamar shekara tara da suka wuce da suka yi harbi a Zariya din nan, duk duniya ba inda aka yi harbi sai a Zariya din. Wannan abu da daure kai, sai ka ga cewa wai wannan wane irin abu ne haka? Yanzu ku baku san inda duniya ta saka ma gaba bane? Ku baku da wani aiki (sai kisa)?

Alla ayyi halin dai, abin da nake cewa shikenan, idan ma ku kun ce harbin za ku yi, ruwanku! Abin da muke baku tabbaci shine guda daya; ba za mu fasa ranar Quds ba! Ba za mu fasa fitowa mu nuna mun goyi bayan al’ummar Palasdinu ba, har ranar da Allah Ta’ala zai kawo mafita. Har Allah ya kai mu wannan wuri mai tsarki mu yi sallah, ya zama ba wannan barazana daga wata sankara da aka dasa a kan al’ummar Musulmi, an kawar da ita, al’ummar Musulmi da sauran al’ummu sun tsarkaka daga wadannan miyagun ayyuka, har wannan rana.

To kuma duk abin da za ku yi, ko ku yi harbi, ko kar ku yi harbi, duk ranar Quds dai za a yi. Ko ku yi hauka ko kar ku yi, duk ranar Quds dai za a yi.

 

NASIHARMU GA SAURAN AL’UMMAR MUSULMI

Amma abin da za mu ce ma sauran al’ummar Musulmi, ya kamata ku idan kun dauka wasu ne suke nuna Tadamun din nan, da kun damu da ku saurari labarun duniya, za ku ga ranar Quds kowa da kowa yake yi, a ko ina ake yi a duniya. A birane daban-daban, har da birnin London da birnin Newyork da sauran manyan birane duk ana yi, amma abin mamaki mu nan wai wani abu ne daban.

To shikenan, tunda dai nan mun samu kanmu a cikin wasu al’umma da kullum ake dauke musu hankula da wasu abubuwa, sai mu ce shikenan, watan-watarana kila ku gane, amma abin da ya fi alkairi gare ku shine kuma ku damu da abin da ya kamata ya zama ya dame ku, ba kullum a rika kunno muku abin da zai dauke muku hankula ku rika rigingimu a tsakaninku kuna zage-zagen juna, kuna kafirta juna, kuna jefa wadansu a wuta, da sauran wannan abubuwan da kuke yi kuma kuna ganin kamar abin da kuke yin daidai ne. Ya kamata ya zama abin da ya dame ku ne ya dame ku. To kuma wannan dai nasiha ce, mun yi, ko a dauka ko kar a dauka.

 

ISRA’ILA ZA TA GUSHE BA DA JIMAWA BA INSHA ALLAH

Amma dai muna ba al’umma tabbacin cewa insha Allahul Azeem wannan al’amari mai tabbata ne, kuma zai tabbata din, insha Allahul Azeem isra’ila kamar ta gushe. Dama kafata aka yi, kuma zai zama bata, kuma ma ta kama hanyar kawuwa insha Allahul Azeem.

Fir’auna ya shekara 200 yana kashe jariran Bani Isra’ila maza. Ko da yake ba duka yake kashewa ba, ya kan dauki shekara guda ne ya kashe, shekara guda ya yara, amma daga baya ya zo karshe.

To wannan al’ummar Palasdinu gashi an doshi shekara 100 suna fama da wannan, kuma nasu insha Allahul Azeem ba zai yi tsawo irin haka nan ba, tunda su yanzu abin da su isra’iliyawan suke yi ba irin abin da fir’auna ya ma Banu Isra’ila bane, shi Fir’auna yana kashe ‘ya’ya jaririai ne maza shekara guda, su kuwa yanzu wadannan suna zuwa ne su baje gari da kauye, su kashe kowa da kowa maza da mata da yara, wanda ko Fir’auna bai yi wannan ba. Saboda haka nasu kamar ya zo karshe shima, don zalunci baya dauwama. Wannan alkawari ne na Allah.

Da wannan kuma ina fatan mun amfana, insha Allah.

Wasallallahu Ala Sayyidina Wa Nabiyina Muhammad wa ala alihid Dayyibinad Dahirin.

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.

 

– Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Ranar Quds Ta Duniya

23 ga Ramadan 1444H (14/4/2023)

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

An Yi Taron Bikin Idil Ghadir A Abuja

Published

on

Harkar Musulunci a Nijeriya, ƙarkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da gaggarumin bikin tunawa da ranar da aka naɗa Imam Ali (AS) a matsayin Khalifa kuma Magajin Annabi (S) a bayansa.

Taron wanda ya gudana a garin Abuja, a ranar Talata 18 ga watan Zulhijja 1445, daidai da 25 ga watan June 2024. Sheikh Zakzaky ne ya zama Babban Baƙo mai jawabi a wajen taron.

Ga Hotunan taron:

Continue Reading

Labarai

Jagora Sayyid Zakzaky (H) Ya Yanka Ragonsa Na Layya

Published

on

Kamar yadda Shafin Ofishin Jagoran (H) na kafar sada zumunta, suka wallafa wasu hotuna da suke nuna shehin Malamin zai yanka ragonsa na sallar Babbar Sallah wato Eid Adha na shekarrar 1445/2024 a gidan sa dake Abuja, domin Ibadar tunawa da sadaukarawar Annabi Ibrahim (As)

 

Ga Hotunan..

 

#JibiyarWallafa

#17/06/2024

#10Zulhijja1445

Continue Reading

Labarai

A Yayin Bikin Tunawa Da Auren Imam Ali (As) Da Sayyida Zahra (As), Jagora Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Dandalin Matasan Sharifai

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin dandalin Matasan Sharifai na Harkar Musulunci a yayin bikin tunawa da ranar Auran Imam Ali (S) da Sayyida Zahara (S), a gidansa dake Abuja.

Rahoton ganawar ya bayyana ne a shafin Jagoran, a ranar Asabar 1 Zulhajji 1445, wanda ya yi dai-dai da 8/5/2024.

Ga Hotunan ganawar…

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.