Connect with us

Labarai

Harkar Musulunci Ta Gudanar Da Muzaharar Quds 2024 A Nijeriya

Published

on

‘Yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun gudanar da Muzaharar Quds a ranar Juma’a 26 ga Ramadan 1445 (5/4/2024) a manyan garuruwan Nijeriya kimanin 30, ciki har da babban birnin Tarayya, Abuja.

Muzaharorin wadanda aka yi su don bayyana goyon baya ga Al’ummar Falastinawa, da kuma yin Allah wadai da haramtacciyar ƙasar Izra’ila da ke kashe su ba dare ba rana tsawon fiye da shekaru 70, a dukkan garuruwan ya samu halartan dubun dubatan al’umma.

Muzaharar ta kunshi dukkan bangarorin al’ummar Musulmi, Shi’a da Sunnah, a wasu garuruwan kuma, kamar a Katsina, an gudanar da Muzaharar ne tare da wasu daga mabiya addinin Kirista, inda suka bayyana cewa al’amarin Falastinawa ya shafi mutuntaka ne ba addini kawai ba, kuma in ma addini ne, Yahudawan Sahayina suna kashe har da Kiristoci ne a Gazza.

An gudanar da Muzaharar a birane da dama, inda aka yi ta da safe a garuruwan Katsina, Bauchi, Kaduna, Potiskum, Zariya da wasu garuruwan masu yawa, sannan kuma bayan sallar Juma’a, aka gudanar a Abuja, Kano, Jos, da wasu biranen, sannan aka yi kashi na biyu kuma a garin Zaria.

A dukkan garuruwan da aka gudanar da Muzaharorin, an yi an kammala lafiya, in banda a Jihar Kaduna, inda gamayyan jami’an tsaron Nijeriya suka bude wa masu Muzaharar wuta a Kaduna da Zaria, sun jikkata mutane kimanin 30, tare da kashe mutum 4 a Kaduna, 2 a Zariya.

Ga hotunan yadda Muzaharar ta gudana a Abuja:

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Daliban Fudiya Masu Shirin Yin Sauƙar Alƙur’ani

Published

on

Kamar yadda shafin ofishin Jagoran (H) ya fitar da wasu hutuna dake nuna cewa; Ɗalibai daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin hardace Alkur’ani sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a jiya Laraba 15 ga watan May 2024 wanda yayi dai-dai da 7 ga watan Zul-Qada 1445 a gidansa dake Abuja

Ga Hotuna….

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Dawo Gida Nigeria Bayan Halartar Taro A Iraƙi

Published

on

Kamar yadda shafin Jagora (H) ya sanya wasu hotuna da yake ɗauke da saƙon dawowar shehin Malamin gida Nigeria a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu 2024.

Shafin ya wallafa cewa; Jagoran ya dawo gida ne bayan halartar taron ƙasa da ƙasa na nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu, wanda ya gudana a birnin Bagadaza, kasar Iraƙi a ranar Laraba 08 ga watan Mayu 2024.

Continue Reading

Labarai

Sheikh Zakzaky (H) Ya Ziyarci Haramin Imam Ali (As) A Najaf

Published

on

Shafin Ofishin Jagoran Harkar Musulumci Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), sun wallafa wasu hotuna a yau 12 ga watan May 2024 da yake nuna cewa shehin malamin ya ziyarci Haramin Imam Ali (As) da yake birnin Najaf a ƙasar Iraƙi.

Ga Hotuna…

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.