Connect with us

Labarai

Bayanin Shaikh Zakzaky Dangane Da Abin Da Ke Faruwa A Zamfara

Published

on

Sabon Salon Mamayen Kasashen Afrika

Wannnan wani bangare ne daga karshen Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), da ya gabatar ga dandazon dubban ‘yan’uwa da suka halarci taron Yaumush Shuhada a ranar Asabar din 25 ga watan Rajab, 1435 (24/5/2014) a filin Polo dake kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ne ya rubuto muku. A ciki Shehin Malamin ya yi bayani dangane da makircin dake cikin kai hare-hare a kauyukan Zamfara, Birnin Gwari da sauran su. Asha karatu lafiya.

DANGANE DA MASU TSAREWA

To, shikenan, sai kuma dangane da su masu, tunda na ma fara taba su masu tsarewa, da tunanin cewa; su basu da wani aiki illa suyi harbi. Mukam muku nasiha don kuna da hakkin muyi muku. Na ga kun ga ji, gashi rana tana tsaka da… tana ta dukan ku. Zan tashi hakanan ko don dole. Ba don na gama ba, zan tashi haka. Sai don lokaci ya yi nisa. Su mahukunta, kamar yadda su mahukunta da wuri suka yi, ainihin suke ganin da karfin tsiya zasu kawar da bayin Allah. Haka ma na yanzu suke tunani. Kuma tunaninsu iri daya ne. Basu daukan darasi daga abin da yake faruwa daga karshe. Ina mulkin Banu Umayya? Ina na Banul Abbas? To. Kunga yanzu me ya rage? Lokacin da shi wannan Harun din nan zai cika (makashin Imam Kazim), sai gashi da bakinsa yana cewa; “ma’agna anni maliyya, halaka annin suldaniya.” Da wa’innan kalmomin ya cika. Shi da bakinsa ya fada ya yanke ma kansa hukumci. “dukiyata ba ta tsinanamin komai ba, sarautar tawa ta riga takai karshe.” Khalas! Ina sarautar? Shi da kansa, yanzun gashi ya ga zai mutu, ya kanjame, gashi yana jiran mutuwa ne. Mutuwa kawai yake jira. Yanzun ana cewa; ranka ya dade ya kaza? Yana cewa; “kai, yanzu ni ta kaina nake. Yanzu dukiyata ba ta tsinanamin komai ba, kuma gashi mulkin nawa ya kare.” Ina dadin da ya sha? Ina shagulgulan da ya yi? Ina hamshakan fadojin da ya gina? Ina sauransu, ina sauransu? Duk basu tsinana mishi komai ba. Ance wani sarki na Banul Abbas, ya taba mutuwa sai ana ma dansa mubaya’a, ya zama ‘suldani’. Aka ajiye gawar, in an gama mubaya’a za a zo a yi jana’iza. Sai wani, ko Zomo ne wanda ake kiwo ah…. Zomo yana cin nama? Ina jin ko kyanwa ce? Ko wani abu mai kama da hakanan wanda suke kiwo a Daji (a lambun Sarki). Sai yazo ya sami idanun sarkin ya ciccire ya cinye su. Ko da aka zo Sarkin Musulmi ba idanu. Shikenan zancen. Duniyar kenan. An gama. Saboda haka kuma taku haka zata kare. Saboda haka kuna da hakkin muyi muku wa’azi, cewa; ainihin wannan abin da kuke aikatawa bazai tsinana muku komai ba. Mulki ne zai gushe ‘lamuhalatan’. Hatta na magidantanku. Dan abin da kuke samu na dukiya. Wanda suke ganin ana baku dukiya kuyi komai, shima zai kai karshe. Eh, zai kai karshe. Amma Shahidai suko kuna raya su ne. Amma kuma harka din da kuke fata ku ga karshenta, to, kunyi kadan, dashen Allah ba abin da yake iya tunbukeshi. Wannan al’amari insha Allahu, Allah ya riga ya ga daman ya kafu kuma sai ya kafu daram! Saboda haka ku kuyi naku, in da abin in baku shawara ne, sai munce; kuyi abin da ya fi alkhayri ne gareku a lahirarku. Amma in baku ji ba, duk abin da zaku yi, ku yi. Duk kulle-kullen da za kuyi ku kukkulla ka da ma ku saurara mana, kui ta tayi. Insha Allah ba abin da za ku iya tsinanawa sai abin da Allah ya kaddara. Shi ne! Kar wani kuma wanda yake da rai wani abu, wai shahada ta bashi tsoro. Dan Allah an taba maka barazanar za a kaika aljanna? Sai akai ka aljanna ka ji dadi. An taba maka barazana hakanan? In mutum ya ce; sai in kaika aljanna ka sha shagali. Me zaka ce mishi? Kai ni. Eh mana! Har a yi mana barazana da kyakkyawan ‘akiba’ alhali burinmu kenan. Kai da kake ma’aikacin tsaro, wanda suke amfani dakai, inda zamu yi maka addu’a ko da ka zama babba, ko da ko ‘officer’ ne kai. Ka kai ‘General’. Inda zamu ce in kai Dan Sanda ne, ka kai ‘Commisioner’ ko ‘IG’ ma. Mu ce; “Allah ya sa ka mutu kana Dan Sanda.” Zaka ce; wallahi bamu sanka. Inda zamu ce; “Allah yasa ka cika kana Soja.” Zai ce; wallahi baka so na. Fatan shi shi ne; yabar Soja. To, mu kai mana addu’a, ka ce; “Allah ya sa mu cika muna gwagwarmaya.” Za ka ji munce; Masha Allah. Babban burinmu kenan! Allah ya sa mu cika muna gwagwarmaya. Yawwa! Ka gani duk abin da muke so kenan. To, in wani Dan sanda ya isa, ya ce; Allah ya sa ya mutu yana Dan sanda. Inda jami’in tsaro anan, ya ce; Allah ya sa ya mutu yana jami’in tsaro. Ka ga ba ya fatan hakanan. Ko yana burin wannan? To, kai ina kai ina fada da abin da, kai naka zai gushe ka ke fada da wanda yake zai tabbata. Naka kamar yazo ya wuce. Amma dai ya rage muku, shikenan dai. Nasiha ce, kuma kuna da hakkin muyi muku. Kuma mukan muku.

To, da yake Magana ta yi tsawo. Na so in Magana dangane da abubuwa da daman gaske. Wanda dole zan watsar. Saboda akwai wasu abubuwan da za a yi. Akwai su kyaututtuka. Tunda ba mun tashi ba kenan.

MAMAYAR AFRIKA

Kunga yanzu muna fuskantar wani abu a kasarnan. Dama can nasha wannan maganar cewa; akwai wani abu yananan tafe. A wa’azuzuka daban-daban na ambata wannan. To, Akwai wani abu na tafe, shi ne; mamayar Afrika. Wanda suka ce, sunyi nazari sunga cewa; karnin da za a shiga (tun kafin ma a shiga), tun kafin a shiga karnin nan. 2000 din nan. Tun a 1900 suke fada. Suka ce; karni na gaba, sunansa KARNIN AFRIKA. Domin sunyi nazari sunga cewa, Afrika na da kusan kashi biyu bisa uku na dukkan dukiyan da ake dashi a duniya. Saboda haka za a sake kama Afrika na biyu. Sabon rububi. Abin da aka kira ‘scramble for Africa’. Suka ce za a yi ‘second scramble’. Za a yi sabon rububi. Saboda lokacin rububin Afrika na wancan karon. Tsakanin daulolin Turai da Ingila da Faransa da ‘Germany’ da ‘Italia’ da ‘Portugal’ da ‘Belgium’, duk kowanne, wannan ya kama nan, wannan ya kama nan, wannan ya kama…. Har suka je ‘Berlin, suka yi ‘conference’ aka raba. Kowa ya fadi inda ya kama aka tsaga aka ba, aka ce; kowa ga nasa. To, sunce za a yi wannan karon. To, sai kuma Amerika ta zo ta ambata ta ce; zata yi amfani da ta’addanci wajen sake kama Afrika. To, shiyasa ku ga wannan abin da yake faruwan yanzu. Sunyi a Libya. Bayan lokacin da suka ji dagowar Larabawa din nan, da dagowar Misra, abin ya firgita su, suka ce, to, suma bari suyi na su. Sai suka yi a Libya. Suka je suka rugurguza Libya din, suka kashe Gaddafi. Yanzu bakomai dake gudana a Libya banda kashe-kashe da fada na Kabilanci. Tsakanin Melisha da kabila. Da na warin launi. Su ko suna diban dukiya.

LIBYA DA NIJERIYA SUKE DA MAI ME DADI (SWEET CRUDE)

To, dama da Libya da Nijeriya ance su suke da mai din da ake ce mishi; mai zaki , mai zaki ‘sweet crude’. To, na Libya yanzu dama na su ne. Na Najeriya dama na su ne. Tunda suna samun gaulaye ne su ajiye. Kullum basu da wani aiki, sai dai su samo wani Gaula su ce shi ne shugaban kasa, su samo Dolo su ce shi ne Mataimakinsa, su sami Gabo su ce shi ne Gwamna, su samu Wofi su ce shi ne Minista, su sami, ga sunan. Su yi ta tatsan arziki din.

SALON MAMAYAN KASA

To, yanzu kuma sai suka zo da wani salon to, mamayan kasa. Saboda haka suka shirya suka mamaye Mali. Yanzu ko shekaranjiyan nan a labaru suna cewa; an fafata a Kidal da Gawo da wa’insu ‘yan bindiga. Haka kawai zasu bayyana a unguwa su yi ta zubar da wuta, bakasan wa ake harbi ba. A ce ai wasu ne masu kishin Islama ne suka bayyana ana fafatawa. Alhali Mali, Zinariya suka gano a Mali. Zinariyar da ba a san inda take ba tuntuni. Don dama ana da labarin akwai Zinare a Mali. Mansa Musan nan, wanda ya yi tafiya zuwa Hajji. Wanda ya shiga tarihi. Wanda aka ce, ya tafi da Rakuma dubu dauke da kayan Zinare da Bayi dubu, kowanne yana dauke da Sandan Zinare. Da yaje Misra, Zinaren da yakai Misra sai da ya sauke farashin Zinare da har yanzu bai tashi ba. Da yaje Makkah ya yi gine-ginen da sai kwanannan ne Ali Saud suka rusa wasu. Suka rurrusa suna gine-ginen su a gewayen harami. Amma har ya zuwa dan shekarun baya gine ginen Mansa Musa abin kallo ne. To, Gwal din nan ba a san inda yake ba. Ansan akwai Gwal. A ina ne ma Mansa Musa ya yi fada, ba a sani ba. Ko su ce, NAWA ne, ko su ce Iraira, ko su ce kaza ne, Bil ne, a je Bil a shafa ba a gani ba. A ce wannan garin ne, a je ba za a gani ba. To, yanzu sun gano Gwal din, saboda haka, suka tsara yadda suka mamaye Mali. Suka ce ‘yan kishin Musulunci ne suka fada daga Aljeriya. Ba dan Mali ko daya a cikinsu. Wai sun kama rabin Mali fiye ma da rabi, sun kafa daula wai sunanta ‘Azwat’. Sannan sai Faransa maza wuf ta shiga wai ta fatattake su. Ta riga Amerika shiga. Don Amerika ita ta shirya shiga. Sai suka… wai sun fatattake su. Bayan wannan, sai Faransa, akwai ‘Diamond’ a Central Africa, shi ne; sunje diban ‘Diamond’ ne sai suka hada fada. Wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba. Wai su Saleka, suka shiga cikin Central Africa Republic, suka yi ta kashe Kiristoci suna kona Cocina da sunan wai su Musulmi ne. Sannan su ba ‘yan Central Africa Republic. Suka fita kasar. Bayan sun fita Afrika ta tsakiya, sannan sai suka kawwana Melisha na kirista wai su Anti Balaka. Sai suka bi suna kashe musulmin da suke zaune a kasar. Wai suna ramuwar gayya. To, inma wadancan Saleka sun zo sun kashe ku, ‘yan kasar ku ne? Daga wani wuri fa suka shigo, suka kuma fita. Waima su suka fara. Kamar yadda suka yi juyin mulki a Mali. Suka wani wai shi Sanogo ya zama shugaba. Wai shi ya yi juyin mulkin akan cewa, shi Sulaimanu Traore ya kasa ima ‘yan tawayen Arewa. Sai kuma aka ce, ‘yan tawayen Arewa din ma sun kwace kasar gaba daya ma a karkashin shi Sanogo din. To, nan ma na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, sai aka ce, wai wani musulmi ya yi juyin mulki na soja. Wai sunanshi Michael Odofia. Kun taba jin sunan musulmi Michael? Wai Musulmi ne, amma sunanshi Michael Odofia. Wai Odofia Michael ya kwace mulki. Wai shi musulmi ne. Ya za a yi Musulmi ya zama shugaban kasar a inda mafi Yawa Kirista ne? Ashe haramun ne Kirista ya zama shugaban Kasa a kasan da yake mafi yawan su Musulmi ne, shi ne har aka samu Kiristoci suka zama shuwagabanni a Najeriya? Da wannan suka fake, suka je suka shiga cikin Central Africa suna ta kashe Musulmi musamman Fulani makiyaya wanda ba-su-ji-ba-ba-su-gani ba. Diamond suka je diba. Kudancin Sudan da suka ga bazai yiwu sukai cewa; ‘yan kishin Isalama ba ne, sai suka hada fadan Kabila tsakanin Dinka da Nod. Amma shi ne, hana ma China Mai. Ya zama tunda dama Kudancin Sudan suna dasawa da China, ya zama basu tare da China. Najeriya kuwa, shi ne suka bullo da wani abu wai shi Boko haram. Wanda tuntuni su wasu ba’adin Amurkawa sun riga sun ambata sanannen abu ne cewa, ba wani abu wai shi Boko haram kikkiran Amerika ne.

SACE WASU ‘YAN MATA A WATA MAKARANTA: GWAMNATIN JONATHAN CE

To, yanzu gashi wai Boko haram sun sace wasu ‘yan mata a wata Makaranta, amma su ‘yan matan da iyayensu sun san suwa suka sace su. Sun sani sarai, gwamnatin Jonathan ce. Ance ana ta zanga-zanga, na ce; wai ana zanga-zangar me ne? Harda jan kaya. Ina jan kayan ya fito? Wai ku bamu ‘yan matanmu. Wa zai baku? Jonathan ko Shekau? Idan Jonathan ne zai baku ‘yan matan ku, eh, to, ku yi mishi zanga-zanga ya fito da ‘yan matan inda yasan ya ajiye. Don yasan Barikin Sojan da ya ajiye su. Idan ko Shekau ne, kunsan a wacce Sheka yake? Yaushe yake jin ku? Yananan shima suna tsare da shi a wani Barikin Soja. Don kayan su ne duka.

BA WATA TSIYA WAI ITA BOKO HARAM

Ba wata tsiya wai ita Boko Haram, karyar tsiya ce kawai. Wannan iskancin din bamu za a yiwa ba. Idan kuna so ku zo ku diba Mai ku diba zinariya ku diba arziki, ku zo a yi ciniki. Ko da cinikin ‘Mugabala’ ne. Mu baku Kwai ku bamu Kaza. Ko, mu baku Rakumi ku bamu Rago. Mun yadda gwara hakanan. Amma kwazo ku yi mana iskanci da addininmu. Ku ce mana muna fama da musulmi masu kishin addini kunzo ku cece mu. Alhali munsan kunzo ku cuce mu ne.

BOKO HARAM SUN SHIGO NA SOSAI

To, ga Boko haram din sun shigo na sosai, su ne; Amerika. Suna shigowa ko, yalai sai kashe-kashe. Sai tashe-tashen bama-bamai. To, kuma wannan irinshi fa suka yi a Afghanistan ko kuma suke yi har yanzu. Kuma irinshi suke yi har yanzu a Irak. A Afghanistan suna da filaye gomomi ne na filayen jirgin sama suna kwasar dukiyoyi. Da sunan suna yaki ne. Asali sun shiga da cewa; suna neman Bin Laden ne. Ba a san inda Bin Laden yake ba. Can kuma suka ce; Bin Laden dinma sun kashe shi a wani wuri ma ba a Afghanistan din ba. To, suna menene a Afghanistan? Har yanzu sunanan. Irak ko suka shiga suka ce akwai WMD. Suka rugurguza Irak. Suna ta cewa; za a ga WMD din. Za a gani. Can sai kuma, har suka kamo Saddam ma, har cocila suka kunna suna kallon bakinsa, imma WMD din yana cikin bakin Saddam ne, Duk sun dudduba. Sai suka juya kuma wai suna kai musu Dimukradiya ne. Yanzu kuma sunce ba WMD amma basu bar Irak ba. Sunanan suna tatsar dukiya. Kullum sai tashe-tashen bama-bamai da kashe-kashe. Kuma su suke yi. To, yanzu tunda suka shigo nan muma abin da suka yi mana shiri kenan. Haka kawai munyi gari abin da muke jin labari a wasu kasashe ya kunno mana bagtatan. Mun tabbatar ba wata kungiya wai ta kishin Islama wai wanda ake ce ma ta wai Boko Haram. Mun tabbatar bata. Ba ta da wujubi sam-sam. A ina? A wani gari? A wani titi? A wacce unguwa? Amma bama-bamai na tashi. Su suke sa bam-baman nan. Ko su haka rami wawukeke su saka su birne ko su matsa ‘remote’ ko su zo da Mota su ajiye su danna. Aikin kenan. Ko wasu su bayyana su bude wuta. Saboda mene? Dukiya suka zo di ba. A tsakanin Zamfara Zinare ke kwance, suna so su share Eriyan da Zinare yake ne, ya zama ba mutum ko kadan, su yi filin jirgin sama, su yi sansanin Soja su rika kwasan Zinariya. Nan tsakanin Zariya da Birnin Gwari, Zinare ne yake kwance da duwatsu masu daraja. So, suke su share mutanen wurin su kafa filin jirgin sama su kwasa. Tsakanin Sakwkwato har zuwa Borno, daga Uranium sai Zinare sai Platinum. Shi suka zo diba. To, ku zo mana ai ciniki. Ko da ma ku bamu Kaza mu baku Rakumi, amma ku barmu da ranmu kuma ku kyale mana addininmu. Amma menene na cewa; zaku shigo ne, da yinma mutane wayayyu babarodo. Ina ku kuke da wayon? Yaushe aka yi Ba amurke? Yaushe aka yi Bature ma tukunna? Wani wayo yake dashi? Eh mana. Dauko tarihin Bature ka karanta mana, badaje, maye, dan bori! Yaushe ya waye harda zai mana wayo? Rashin kunyan banza kawai. Ku zo ai ciniki. Kuna da Bindiga mun sani, kun iya kisan kai, amma a kyale mana addininmu.

To, yanzu abin da ya kawo su kenan kuma yanzun musiban yana rutsawa nan da nan tsakanin ‘yan’uwa. Kunsan a Gwoza. Harma sun rutsa da garin Gwoza, sunce, baza su shiga ba, saboda suna jin tsoron ‘yan shi’a. Don akwai wani dan uwa da suka kama suka cire masa kai, suka fille kansa sosai, amma sai suka ji kalma, kan na Kalmar shahada. Suka duba ga Kai yana ‘la’ilaha illallah Muhammadur Rasulillah’ ga gangan jiki din. To, shi ne suka ce; suna jin tsoron garin saboda ‘yan shi’a. To, wannan abin da muke fuskanta kenan. Kuma nasan sun riga sun ambata tuntuni, abin da suke jin tsoro kawai ita ce; wannan harka din. Don sunsan ita ce kawai zata taka musu burki.

Amma muna ma kira ga su wa’innan mutanen, mun ji an kira ka baka ci zabe ba ance kaine kake da mukami, mun ji baka cancanta ba, mun ji kai Gaula ne, ko Gabo ne ko Sakarai ne ko Shashasha ne, ko Wofi ne, to, mun ji kaine. Yanzu ko a hakanan ka yadda yanzu a baka kudi a kashe mutanenka? Kai baka da tunani? Shikenan an baka mukami an baka kudi shikenan a kashe mutanenka. Shirun ya isa ga al’umma. Kuma ba kyaleka za su yi ba, in sun gama dakai, in ka zama fanko kashe ka zasu yi, haka suke yi. Saddam din nan da suka kashe kayansu ne, Gaddafin da suka kashe kayansu ne, duk su suka yi su. Suka kama suka kawar da su. Kaima in sun gama dakai zasu yanka kane, an gama.

Nasan wannan, ah, munasabar yaumush shuhada muna da Magana da yawan gaske ganin cewa; wannan abin da ya kunno kai a kasarnan lallai fa ya shafe mu. Kuma lallai kam fuskantan wannan da duk iyan abin da muke iyawa, aiki ne ga addinin Musulunci. Kuma wanda duk suka kashe a cikinmu sunansa Shahidi! Bance muku tunda su suna daukan Bindiga ne, muma zamu dauki Bindiga ne, amma muna da makamai irin namu. To, su zamu dauka insha Allahu.

Allah Ta’ala muna rokonka ka nuna mana Yaumush Shuhada na badi cikin koshin lafiya da yalwar arziki. Allah madaukakin Sarki ka karemu da kariyarka, ka taimakemu da taimakonka ka dora mu birbishin makiya.

Wasallahu Ala Muhammadin wa’alihid dayyibinad dahirin. Wassalamu alaikum warahmatullahi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Nasihar Shaikh Zakzaky Kan Raya Daren 27 Ga Ramadan

Published

on

“Yau Talata 26 ga watan Ramadan 1434. Gobe insha Allah zai zama 27 ke nan. Saboda haka abin da ke gabanmu yau daren 27 ne. Dare ne mai muhimmanci, wanda yake ya kamata mutum ya raya shi da ibada. Ya yi kokari kar ya yi barci iyan iyawarsa. Ya raya shi da ibadodi.

“Ko ba komai su Ama sun fi tsammanin wannan daren ne Lailatul Kadri. Saboda haka bai kamata a bar ka a baya ba, ya zama ana ibada kai kana barci. Kana ganin kamar kai ka raya layalil Kadr. To, bai kamata wani ya raya daren 27, ya zama ya fi ka ba. Ya kamata ka fi shi!

“A ruwaya an samo cewa, an ji Imam Zainul Abidin (as) yana addu’a tun farkon daren har zuwa karshen daren. Addu’ar da yake yi ita ce: *Allahummar zuqni tijafiya an daril gurur wal inabata ila daril khulud. Wal isti’idada lil mauti qabla hulil faut.*”

“Wato Allah ka azurta ni nisantan gidan rudu da komawa zuwa gidan dawwama, kuma tanajin mutuwa kafin saukar kubucewar ta (damar).

“Wannan addu’ar duk daren aka ji Imam Zainul Abidin (as) yana karantawa. Daga cikin jimlan abin da za ka yi shi ne ka roki Allah ya kiyaye ka daga karkata zuwa wannan duniyar, ya azurta ka nisantar gidan rudu, da karkata zuwa gidan dawwama da tanajin mutuwa kafin saukar ta. In ta sauka shi ke nan an gama, dama ya kare kuma.”

Ibrahim Musa ya rubuto daga audio na tafsirin Suratul Dalaq, Aya ta 5 zuwa karshe da Cibiyar wallafa ta yada a yau 26 ga Ramadan 1441.

Continue Reading

Labarai

Gargadi Ga Masu Tafsiri – Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Published

on

“Na sha yin wadansu bayanai a shekarun baya, farkon azumi, amma kuma dai na san ba bi za a yi ba, ba kuma ji za a yi ba, amma dai mutane suna da hakkin mu tunatar da su, in ya so kar su ji, kar kuma su yi aiki da shi, amma mun fita hakkinsu.

A nan kasar mun saba idan Ramadan ya kama akan yi ta yin tafsirin Alkur’ani. To, ba mu ce tafsiri ba kyau ba, duk da mun san da yawan mutanen da ke yin tafsirin ba su da ahliyyan su yi, amma dai suna yi. A karanta wa mutane Alkur’ani su ji me Allah ya ce, masha Allah, to amma kuma sai ya zama fage ne a nan na mutane su rika fadar ra’ayinsu. Ra’ayinsu na siyasa, ra’ayinsu na addini, ra’ayinsu na son rai; duk sai su fada da sunan tafsiri. To, wannan bai dace ba.

Ya kamata a girmama Alkur’ani. In kana da ra’ayi, ra’ayinka na siyasa, sai ka ce, “jama’a ina da ra’yin siyasa, zan yi muku bayanin ra’ayina. A zo rana kaza.” Sai ka yi ta jawabi, ka yi ta fadar ra’ayinka. Ka ga ra’ayinka ne; ko mutum ya dauka, ko ya bar maka.

Amma in ka dauko littafin Allah ka ce za ka fassara, to fassara abin da yake muradin Allah din. Kar ka kawo ra’ayinka. Ba muhallin ra’ayinka ba ne. Ko ba komai wannan wulakanta Alkur’ani ne, kana da ra’ayi, sai ya zama lokacin da za ka karanta Alkur’ani ne za ka fadi ra’ayin. Domin Alkur’ani ba yana magana dangane da ra’ayinka ba ne.

Ma’anar tafsiri shi ne yaye muradi, ana kokarin a gano mai magana me ya ce, me yake nufi da maganar tasa? Shi ne ake nufi da tafsiri. Wannan ko da wani ne ya yi magana, kake kokarin ka ce me ya ce, za ka yi masa adalci ne ka fadi abin da yake nufi. Ballantana kuma wannan mai maganar Allah Ta’ala ne. Maganar Allah ce ake kokarin a ce me Allah yake nufi da wannan. Amma kuma sai ka kawo duk abin da ranka ke so. To, ba a tafsirin Alkur’ani da ra’ayi.

Kuma da gargadi kakkarfa daga hadisin Manzon Allah (SAWA), yana cewa: “Wanda ya fassara Alkur’ani da ra’ayinsa, to ya saurari makomarsa a wuta.” “Duk wanda ya fada dangane da Alkur’ani ba tare da ilimi ba, ya saurari makomarsa a wuta.” In ba ka sani ba, ka yi shiru ba ka sani ba.

Tafsirin ga su nan, ka ji ana ta fada a rediyo. “Kun saurari tafsiri daga Ustaz fifa’iya ya zawaidi, yanzu kuma ga Malam Ha mai kusussurin komabaya. Kun saurari Malam Ambaki bude, yanzu ga Shaikh fifa’iya ya zawaidi ko Damulahandu.” Ga su nan Shehunnai dai birjik. “Kun saurari Malam mai gafakan salati, to yanzu kuma ga Malam Mai carbi nan.” An dinga zubawa ke nan. Wannan ya yi nan, wancan ya yi can. Masallatai ko’ina, har da masallacin Gidan mai.

Mu dai ba mu ce tafsiri ba kyau ba, amma don Allah a yi adalci. Ya zama muhalli ne na fadin abin da Allah ya fada, ko kuma mutum ya yi shiru. Akwai wasu da suka zo suna tambaya ta, akwai wani gari, dan’uwan da ke yin tafsiri yanzu ya tafi makaranta, yaya ke nan yanzu a yi ta tafsirin? Sai na ce, ai ba lallai ne a yi tafsirin ba. In ba wanda yake da ahaliyyan ya yi, sai a fasa. Sai a yi wani abin daban. A yi wani babban tafsiri mana, a tara mutane, a ba su abin buda baki. Ya ma fi wannan surutun da ake yi. Wallahi ka ba da shayi ya fi alheri. Ya fi wannan surutai din. Ko a yi wani aikin alheri mana, a je asibiti, a gai da marasa lafiya. A yi wani aikin alheri. Amma tafsiri a bar wa ma’abotansa.

To, wannan kuma gargadi ne, ko ba komai ma fita hakki. Wasallallahu ala Muhammadin wa alihid dahirin.

Allah ka ganar da mu abin da muke karantawa, ka shiryar da mu da shiriyar da ke ciki, ka ba mu ikon aikatawa.”

— Ibrahim Musa ne ya rubuto daga tafsirin Alkur’ani na ranar 2 ga Ramadan, 1434, wanda Cibiyar wallafa ta yada shi.

Continue Reading

Labarai

Shaikh Zakzaky Na Taya Al’ummar Musulmi Barka Da Ranar Mauludin Imam Hasan Almujtaba (AS) 

Published

on

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya taya al’ummar Musulmi murna da zagayowar ranar da aka haifi babban jikan Manzon Allah (S), Imam Hasan Dan Ali Dan Abidalib (AS) wanda ya auku a ranar 15 ga watan Ramadan.

 

A yayin da yake gabatar da jawabi dangane da Imam Hasan (AS) bayan kammala Tafsirin Alkur’ani Mai Girma a ranar 15 ga watan Ramadan, Shaikh Zakzaky ya bayyana muhimmancin raya Mauludin Imam Hasan (AS) ko da ta hanyar shirya walima da raba abinci da tunatar da juna matsayinsa ne a tsakanin masoyansa.

Da yake karanto darajojin Imam Hasan (AS), Shaikh Zakzaky ya ambata cewa ana wa Imam Hasan lakabi da ‘Assibd, As-Sayyid, Al’amin, Alhujja, Attakiy, Azzakiy, Almujtaba, Azzahid, Al-Barr, Annaqi.”

Shaikh Zakzaky yace dangane da fadin Allah (T) a cikin Alkur’ani, ‘Fi ayyi suratun maaSha’a rakkabak.’ Imam Hasan (AS) yace: “Allah (T) ya sauwara Ali a tsatson Abudalib, a surar Manzon Allah (S), sai ya kasance Ali Bin Abidalib (AS) ne ya fi kowa kama da Manzon Allah (S). Husaini Bin Ali kuma ya fi kowa kama da Fatima (SA). Ni kuwa sai na zama na fi kowa kama da Sayyida Khadijatul Kubra (SA).”

Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa:” yayin da aka haifi Imam Hasan, Sayyida Zahra ta zo da shi wajen Babanta (S) nannade a kyallen Haririn da Jibril ya taba kawowa Annabi daga Aljanna. Sai Manzon Allah (S) ya saka masa suna Hasan, ya kuma yanka masa rago.”

Imam Hasan Almujtaba (AS) shine limamin Musulmi na biyu, bayan Amirul Muminin (AS) a cikin jerin Wasiyoyin Manzon Allah (S) kuma Halifofinsa Tsarkaka a bayansa.

Continue Reading

Trending

Copyright © 2019 By Institute for Compilation and Publication of Sheikh Zakzaky's Works.